← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 110

Sashe 51

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Mommy suna zaune jigum-jigum Raihan ta buɗe idonta, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta runtse idonta ta sake buɗewa. Da sauri ta zabura za ta tashi zaune Mommy ta riƙe za ta yi magana Raihan ta riƙo hannunta tana hawaye ta ce, "Mommy da gaske Salim ya mutu, Mommy ɗazu fa muka yi waya yace zai gaya min wata magana don Allah ki gaya min gaskiya ko wasa ake yi min?" Mommy ta fakaici idon Raihan ta goge hawayen idonta ta ce, "Raihan!" Raihan ta sake fashewa da kuka ta ci gaba da cewa, "Mommy don Allah kar ki ce min Salim ya mutu!" Mommy ta sauke ajiyar ta ce, "Raihan muna da ikon dakatar da mutuwa ne? Ke fa musulma ce me ya sa ba za ki rungumi ƙaddararki hannu bibbiyu ba? Allah shi ya halicci Salim kuma ya karɓe shi babbar soyayyar da za ki nuna masa ki yi masa addu'a." Raihan ban da hawaye babu abin da yake zarya a fuskarta. Kamar wacce ake yi wa raɗa haka ta ji maganganunsa na dawo mata a lokacin da suke waya, a zabure ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake ta ce, "Ina wayata don Allah ba ni wayata na kira lambarsa na ji." Mommy na ganin haka hawaye ya ci gaba da zubo mata don ta san duk abin da Raihan take yi tana yin sa ne cikin ruɗewa da tashin hankali.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn0706 206 2624

28

Lokacin da Daddu ya ƙarasa ƙofar gidansu Salim cike yake da mutane sun yi jigum-jugum, yana tsaye motar asibiti ta ƙaraso ƙofar gidan tana zabga jiniya. Mahaifin Salim ne ya fito daga motsarsa babu jimawa aka fara kiciniyar fito da gawar Salim daga Amblance, matsawa mutane suka fara yi don a bayar da hanya su shigar da gawar. Lokaci-lokaci Mahaifin Salim yake share ƙwallah da take zuba daga idonsa, ana shiga da gawar Salim Mahaifiyarsa da ƙannensa suka fashe da matsanancin kuka. Mahaifin Salim na ƙofar gida mutane suka fara yi masa gaisuwa, jiki asanyaye Daddy ya ƙarasa wurinsa ya ce, "Alhaji ya muka ji da haƙuri?" Mahaifin Salim ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Alhamdulillah da godiya duk abin da Allah ya yi mai kyau ne." Daddy ya jinjina kai ya ce, "Haka Allah ya jiƙansa halinsa na gari ya bishi." Mahaifin Salim ya ce, "Amin ya rabbi, amma ya ya matarsa ina fatan babu wani abu da yake same ta?" Daddy ya ɗan yi jim sannan ya ce, "Ka san sha'anin ƙuruciya yanzu haka dai tana asibiti ta farfaɗo amma jikinta da sauki." Mahaifin Salim ya furta, "Allah ya bata lafiya." Gabaɗay suka amsa da amin, sun ɗan jima suna tattauna yadda jana'izar Salim za ta kasance sannan suka yi sallam. Jikin Daddy duk ya yi sanyi ko da bai ga gawar Salim ba amma yadda ya ji ana maganar irin ƙonewar da suka yi abin ya ɗaga hankalinsa.

A lokacin da Salim ya gama waya da Raihan kallon Nadabo abokinsa ya yi ya ce, "Mutumin ni fa na yi muku nisa sai kun biyo sawu." Nadabo da yake driving ya yi murmushi ya ce, "Allah na tuba da me kwaɗo ya fi gaya, amma duk cika bakinka ai yanzu dai ɗaya muke da kai tun da yanzu muke kan hanyar zuwa kaika. Ni Allah sa ya sa ma karka ba mu kunya duk kurin nan ka kasa cika aiki." Salim ya saka dariya yana saka wayarsa a aljihu ya ce, "Allah ya kiyaye kai fa shegen kaya ne, an gaya maka abin da zan je yi kenan." Nadabo ya yi masa hararar wasa ya ce, "Ɗan iska irinku ne idan kuka rufe ƙofa tun safe sai bayan isha'i." Lokaci ɗaya suka saka dariya don Salim mutum ne mai shiga rai, mu'amala ta rana ɗaya za ku yi ya shiga ranka. A daidai Zayyan suya spot suka yi parking, Salim da Nado suka fito kowanne sanye da babbar riga. Sauran motocin abokan Salim ne suka yi parking kasancewar suna bayan motar su Salim. Kaji huɗu Nadabo ya sa mai Naman ya saka a leda, mai naman da murmushi ya dubi Nadabo yana murmushi ya ce, "Abokina da alama kai ne angon don na lura ban da ƙyalli babu abin da goshinka yake yi." Nadabo ya sake buɗa babbar riga yana dariya ƙasa-ƙasa ya ce, "Ga angon nan amma yadda kasan ni aka ɗaurawa don ko sheƙin angoncin baya yi." Salim ya yi dariya ya dubi mai nama ya ce, "Wallahi za ka ja na bar maka kazarka don sai mu koma wani wurin haka kawai Allah ya ba ni girma ka sauke min." Mai naman ya yi dariya yana miƙa musu manyan ledoji, Nadabo ya karbi ledar yana taɓe baki ya ce, "To ya na iya dole na biya kuɗin kaza kuma na yi dakonta, idah da rai da lafiya nima baɗi war haka ja rako ni ɗakin matata." Nadabo ya yu maganar yana miƙawa mai nama kuɗinsa. Mota suka buɗe suka shiga juyawar da Nadabo ya yi zai sa ledar kazar a mazaunin baya ya ci karo da wani baƙin kare mai jan ido, ƙirjinsa ne ya buga ya runtse ido ya buɗe amma sai bai ga komai ba. Jiki a sanyaye ya waiga ya ce, "Salim don Allah baka ga komai a bayan motar ba." Salim ya waiga babu komai a wurin ya ce masa, "Kamar ya fa? Ba abin da na gani." Shiru Nadabo ya yi ya kunna motar suka fara tafiya. Ba su yi nisa ba sai jin wani irin haushin kare wanda ya ratsa har tsakiyar kansu, a firgice duk suka juya don ganin abin da yake faruwa. Kafin su kaiga ganin kammanin kare ya yi kukan kura ya faɗa kan Salim tare da kai bakinsa kan daidai maƙogaronsa, Nadabo ba ƙaramin razana ya yi ba nan take motarsu ta fara tangal-tangal akan titi ƙarshe ta faɗa cikin wata babbar kwalbati, motar abokansa da ke biye da su ita ma ta i bayansu sai ta ukun ce Allah ya kare. Nan take wuta ta tashi a wurin mutanen da ke bakin titin suka fara kawo ɗauki ta hanyar zuba ƙasa da ruwan kwata, amma wutar tamkar ƙwara mata fetur suke, sai da ta ci don kanta sannan ta lafa a daidai lokacin ƴan kwana-kwana suka ƙaraso wurin tare da motar asibiti. Sai da suka ƙarasa kashe wutar sannan aka ɗebi gawargwarin su Salim aka wuce asibiti da su.

Kafaɗar Raihan mommy ta dafa ciki dakakkiyar murya ta furta, "Raihan!" Raihan bata amsa ba sai hawaye da yake zarya a fuskarta, ta kafe mommy ta ido amma ilahirin jikinta rawa yake. Zuciyar mommy babu daɗi amma duk da haka ta kauda kanta gefe ta ci gaba da cewa, "Ke muslma ce! Don haka ki rungumi abin da Allah ya jarabce ki da shi. Salim ya mutu kuma lokacinsa ne ya yi idan ke ni ko ke Ubangiji ya so ɗauke wa ye yake da ikon hanawa?" Raihan ta kasa furta komai ban da hawayen da ke zuba a fuskarta. Mama Hafsa ita kanta hawaye take don duk wanda ya ga halin da Raihan take ciki sai ya matuƙar tausaya mata. Mommy ta riƙo hannun Raihan ta ce, "Ta so mu je ki ɗauro alwala ki yi sallah raka'a biyu ki yi wa mijinki Addu'a." Raihan na miƙe wa daga kan gado ta faɗa jikin Mommy ta fashe da matsanancin kuka. Bayanta ta fara bubbugawa sai dai ta kasa bata haƙuri, a hankali ta ɗago Raihan daga jikinta ta raka ta banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah raka'a biyu tana yi tana zubda ƙwallah. Lokacin da Daddy ya ƙarasa asibitin dare ya tsala sosai, don lokacin kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Yan zuwa asibitim ya samu su Mommy a zaune jigun-jigun, Raihan na zaune a kan dadduma ta kifa kanta da cikin ƙafafuwanta. Daddy na zuwa Raihan ta ɗago tana kallonsa sai kawai ta fashe da kuka ta ce, "Daddy kaima ka ji Salim ya mutu? Wallahi ɗazu muka gama waya da shi Daddy don Allah me ya sa..." Daddy ya ƙarasa gaban Raihan ya sa hannunsa ya rufe mata shi yana cewar, "Raihan ba na san ki riƙa surutu haka." Yana daga tsugunne ya kalli mommy ya ce, "Yi wa nurses ɗin nan magana su yi mata allura ko za ta samu relief." Mommy ta jingina kanta da bango ta ce, "Tun ɗazu suka zo wallahi fir taƙi yarda." Daddy ya jima yana yi wa Raihan nasiha ta yi shiru tana sauraronsa tana hawaye. A haka suka ƙarasa ganin daren ba tare da kowa ya iya runtsawa ba.

Mahaifin Salim sai da ya tsawatar wa Mahaifiyar Salim da ƴan uwansa sannan suka yi shiru amma kana kallon Mahaifiyarsa za ka fahimci irin tashin hankalin da take ciki. A daren aka suturta Saim sai dai ko wanka ba a yi masa ba sakamakon mummunar ƙunan da jikinsa ya yi. Su Salim su Biyar ne suka rasu sai dai gabaɗaya a cikinsu da ƙyar mahaifansu suka gane su saboda sun ƙone ƙurmus sun yi baƙiƙƙirin musamman Salim da gawarsa ta fi ta kowa munana saboda irin kisan gillar da mummunan karen nan ya yi masa. Wannan mummunan labarin na rasuwar su Salim lokaci ɗaya ya yaɗa ko'ina musamman da ƴan jarida suka taimaka da masu manyan wayoyi suka riƙa watsa labarin, duk wanda aka cewa Ango ya rasu da abokan a hanyar zuwa raka ango gidansa ba ƙaramin jimantawa suke ba, musamman da hotunan bikin su Raihan ya ratsa kafofin sada zumunta sai kuma katsam aka samu wannan labarin. Mutane waɗanda suka sansu da waɗanda basu san su ba haka suka riƙa ɗora hotunan Salim da Raihan na ranar Dinner da Kamu suka saka alamar kuka tare da yi masa addu'ar Allah ya kyauta makwanci.
Chapter 51 · 0% Book details