Sashe 83
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Raihan na zaune shiru akan gado a hankali ta zame mayafin kanta tana ƙare wa ɗakin kallo, lokaci ɗaya gidan Huzaifa ya faɗo mata da lokacin da take zaune ya dawo wurinta. Gabanta ne ya faɗi a hankali ta matsa ta jingina da fuskar gado, wayarta ta zaro ta kunna karatun Alƙur'ani kamar yadda Malam ya gaya mata, lumshe ido ta yi tana jin wata nutsuwa na shigarta. Hannuwa biyu ta haɗa ta yi tagumi tana tunanin sabuwar rayuwar da za ta fara, a hankali ta ji an turo ƙofa ƙamshin turarensa ya dokin hancinta. Numfashinta ne ya kusa ɗaukewa gabanta na ci gaba da faɗuwa, ɗago kanta ta yi karaf suka haɗa ido. Ɗauke kanta ta yi ta sunkuyar da kai gefe tare da amsa masa sallamar da ya yi, a gefen gadonta ya ajiye ledojin hannunta sannan ya harɗe hannuwansa a ƙirji ya ce, "Ki fito Falo ina jiranki." Jiki a sanyaye ta amsa masa daga haka ya fice daga ɗakin, yana fita ta miƙe ta gyara tsayuwar mayafinta sannan ta bi bayansa. A falo ta same shi zaune shi da Sumayya akan kujera, kujerar da take kallon tasu ta zaune kanta a ƙasa. Tun da ta shigo Sumayya take bin ta da harara, ganin ta zauna ya sa Sumayya ta sake kwantar da kanta a jikin Al'amin, ta gefen ido take kallon duk abin da yake faruwa don haka ta ji wani abu ya caki gefen zuciyarta. Cikin zuciyarta ta fara ambatar sunan Allah don jin sanyi a zuciyarta, tana cikin wannan yanayin ta riski muryarsa yana faɗin, "Dukkan godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, Alhamdullah muna sake nuna godiyar mu da Allah ya nuna mana wannan rana mai albarka. Dalilin da ya sa na tara ku a nan domin na sanar da ku dukkanku matana ne, babu wacce take zaman wata duk zamana kuke yi, kuma kowacce ɓarinta daban don haka bana buƙatar tashin hankali ko rashin girmama juna, ku haɗa kanku ku zauna lafiya saboda Allah ne ya haɗa mu don haka sai mu haɗu mu gina rayuwarmu bisa tubar addinin musulunci." Yana gama maganar Sumayya ta ɗago ta dubi Raihan sannan ta ja dogon tsaki ta ce, "Ya kamata ka ce dukkanmu matanka ne amma kowacce da matsayinta a zuciyarka, don ka sakan akwai bambamci mai tazara tsakakin matar na gani ina so da matar shige, tun da ko hausawa sun ce matar shige bata dara..." Kallon da Al'amin ya wurga wa Sumayya ne ya katse ragowar maganar bakinta, ganin haka ya sake ƙona mata rai ƙwalla ta ciko idonta cikin kuka ta ce, "Wallahi dama na san kana sonta kawai ka yi haka ne don ka tarwatsa farincikina, tun da haka ne ka je gata nan na bar mata kai." Tana gama maganar ta miƙe cikin kuka ta wuce ɗakinta. Dafe kai Al'amin ya yi rai a ɓace don ko kaɗan ba haka ya so daren amarcinsa da Sumayya ya kasance ba, ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Raihan cikin jin haushi ya furta, "Shi kenan hankalinki ya kwanta!" Ɗago wa Raihan ta yi ta kalle shi nan take idonta ya ciko da ƙwalla, Al'amin ya ƙarasa gaban Raihan da ƙarfi ya fisgi hannunta ya wuce ɗakinta yana shiga ya zaunar da ita akan gado fuska a haɗe ya furta, "Ba dai ni kike so ba? To ga ni." Hawayen da Raihan take dannewa ne ya suɓuce mata, ta fara ƙwalla haɗe da shassheƙar kuka. Kaiwa da kawo wa ya fara yi cikin takaici ya kalleta sannan ya ce, "Me kike buƙata yanzu." Shiru Raihan ta yi ba tare da ta furta komai ba sai kuka da take rairawa gwanin ban tausayi, a ɗan tsawace ya furta: "Ba magana nake yi miki ba?" A zabure Raihan ta ce, "Ba na buƙatar komai." Da sauri Al'amin ya nufi ƙofa yana faɗin, "Ban da shiga haƙƙi haka kawai a haɗa ni da mata biyu ina ji ina gani ƙanƙanin yaro da ni." Waɗannan kalamai ba ƙaramin taɓa zuciyar Raihan suka yi ba, wani irin ɗaci ta ji a zuciyarta musamman da ta tuna wurin wata zai tafi, kifa kanta ta yi akan gado ta ci gaba da raira kuka mai ban tausayi.
Al'amin na shiga ɗakin Sumayya ya same ta kwance akan fado tana gursheƙen kuka, ta baya ya ɗagota ya zauna akan gadon yana jinginata da jikinsa. Ajiyar zuciya take sauke wa sai kuma ta fara mutsu-mutsu tana son ƙwace jikinta, riƙe ta ya yi gam a jikinsa ya kwantar da kansa jikin wuyanta yana cewa, "Kina son Allah ya ƙona ni ne Sumayya?" Shiru ta yi bata tanka masa ba ya ci gaba da cewa, "Ke da ita duka matana ne don haka babu wacce zan fifita saboda sai Allah ya hukunta ni da yin haka..." Wani abu ne ya soke ta a zuciya ya fisge hannunta ta furta, "Dama na jima zuciyata na gaya min kana ƙaunar yarinyar nan idan ba haka ba babu yadda za a yi ka fara wulaƙanta ni a gabanta." Janyota jikinsa ya sake yi yana murmushi don ya fahimci zallar kishi ne ya lulluɓe idon Sumayya, wannan karon bata yi yunƙurin ƙwace wa ba. A daidai kunnenta ya fara lallashinta da cewar, "My Summee kin san dai ina ƙaunarki don Allah kar kishi ya hana ki yi min adalci, na gaya miki ke kaɗai ce a birnin zuciyata ta yaya wata za ta zo ta samu gurbi a wurinki? Ko kina shakku akan soyayyar da nake yi miki?Yarinyar nan na gaya miki Daddy ne ya tilasta ni aurenta amma babu ko ɗishin ƙaunarta a zuciyata." Al'amin ya jima yana lallashin Sumayya sai da ƙyar ta sauko sannan suka gabatar da sallar nafila, da kansa ya riƙa ciyar da Sumayya sai da suka ci suka ƙat sannan ya riƙe hannunta suka fita ya riƙa nuna mata sauran ɗakunan, tsarin gidan ba ƙaramin birgeta ya yi ba takaicinta ɗaya da ta tuna ba ita kaɗai ba ce a wurin Al'amin. Amma da ta tuna irin kalaman da yake yi mata sai ta ji komai ya ɓace daga ranta, ta ci alwashin sai Raihan ta bar gidan da ƙafarta don ko da wuta take yawo sai ta bar mata Al'amin ɗin ta. Raihan na ɗaki sai da ta ci kukanta ta godewa Allah sannan ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallah tana kai wa Allah kukanta, ta jima akan dadduma don har sai da bacci ya fara awon gaba da ita sannan ta miƙe ta sauya kayan bacci ta hau kan gado. Sai dai a madadin baccin ya ɗauke ta sai tunani ya hana ta, babban abin da ya tsaya mata a rai da take ayyana irin soyayyar da Al'amin yake yi wa Sumayya, bata yi aune ba sai ji ta yi hawaye na zuba. Gefen hannunta ta sa ta goge ta janyo blanket ta rufa sakamakon zazzaɓin da ta fara ji a jikinta, ledar da Al'amin ya ajiye mata ta ƙurawa ido tana ayyana wai yau daren amarcinta ne amma take kwance haka miji yana wurin wata. Mutuwar Salim ce ta dawo mata sabuwa take tuna irin kulawar da yake bata da alƙawarurrukan da ya yi mata har zuwa ranar Dinner su, da irin abubuwan da ya shiga tsakaninta da shi a ranar. Kuka take sosai kamar ranta zai fita, sai da dare ya tsala sannan bacci ya yi awon gaba da ita.
Washegari