← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 110

Sashe 103

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da safe Mommy ta samu Raihan da maganar Alhaji Shatima, Wani iri Raihan ta ji maganar sai dai a wannan lokacin duniya ta koya mata ladabi ba komai take zafafawa ba, domin ta lura ko ka zafafa matuƙar abun ba mai alkhairi a wurinka ba ne sai dai ya wahalar da kai a banza. Jiki a sanyaye Raihan ta furta, "Mommy tsoron aure nake ji don gani nake kamar ba ni da rabo a ɓangarensa. A yanzu ba ni da zaɓi sai neman zaɓin Ubangiji domin a baya na ɗauka son raina shi ne alheri ashe ba haka ba ne, don haka matuƙar kun amince da ɗabi'unsa na amince zan aure shi." Ba ƙaramin tausayi Raihan ta bawa Mommy ba, ta riƙo hannunta cikin kulawa ta ce, "Allah ya yi miki albarka Raihan, insha Allah zan sanar da Daddynki duk yadda ake ciki za ki ji." Raihan ta sakar wa Mommy murmushi don ta lura mahaifiyarta na cikin damuwa da halin da take tsintar kanta a ciki. Daddy na dawowa Mommy ta sanar masa duk yadda suka yi da Raihan, sai da ya sake tambayar Raihan ya ji daga gare ta sannan ya ce zai sanar da Alhaji Shatima domin ba baƙo ba ne a wurinsa tun da abokin kasuwancinsa ne. Alhaji Shatima na shiga motarsa ya daki sitiyarin motarsa haɗe da sakin wata ƙaramar ƙara a hankali ya furta, "Burina ya kusa cika domin na tabbata matuƙar na auri Raihan sai na san yadda na yi na mallaki Kamfanin maganin sauronsa da ke unguwar Tudun murtala, ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai na mallako har katafaren kamfanin takalmansa na unguwar sharaɗa. Domin babu yadda za a yi na nuna masa yadda ake kamun kifi sannan ya fini iya kamawa. Idan na mallaketa sannu a hankali zan nemi hanyar da zan bi domin na halaka shi, daga nan Raihan za ta samu kaso mafi tsoka don haka idan ta samu kamar na samu ne." Alhaji Shatima ya yi ajiyar zuciya ya ci gaba da cewa, "Ina baƙin cikin na ga na buɗi ido na ga bawan Allahn nan domin arziƙinsa kullin gaba yake baya yin baya. Alhalin wasu shawarwarin dangane da kasuwanci ma ni na ke bashi, amma ni kullin ji-iyau ba na yin gaba." Yana gama surutansa ya figi motarsa da gudu ya fice daga layin. Sati ɗaya da zuwan Alhaji Shatima Daddy ya kira shi tare da sanar masa Raihan ta amince da batun aurensa, murnarsa har sai da ta ƙi rufuwa a gaban Daddy. Shi kuma Daddy a tsamminsa tsananin soyayyar Raihan ce ta saka shi yin haka don haka ya sake jin wata irin ƙaunar Alhaji Shatima a cikin ransa. Nan take ya yi masa kyautar wata gonarsa da ke garin Kura, farinciki ya sake lulluɓe Alhaji Shatima ya riƙa zuba masa godiya da fatan alheri don wannan ne ya tabbatar masa da Raihan ita ce daidai macen da yake so mai ƙashin arziƙi tun da ga ƙofofin arziƙi nan sun fara buɗe masa. A ranar sai da suka gaisa da Raihan yanayinta babu yabo babu fallasa, ya gabatar mata da kansa da adadin yaransa da wasu al'amuransa na yau da kullin. A cikin ƙasa da wata guda Alhaji Shatima suka daidaita da Raihan don har kuɗin gaisuwa ya kawo an tsayar musu da ranar aure wata biyu, su Inno baki har kunne don kusan duk zuwan da Alhaji Shatima zai yi ƙullin ledar su na musamman ne, don wata rana da ya ciko musu ƙatuwar leda da kaza suna ci faɗa ya kacame a tsakaninsu har sun fara lissafin idan Raihan ta haihu su za su je zaman daɓaro. Sai da Mommy ta shiga faɗan ta sasanta su da cewar wuyarta dai a yi auren a samu cikin tana haihuwa duka za su je gidan su zauna har sai ta yi kwana arba'in. Raihan ba wata soyayyarsa take ji a zuciya ba don dai kawai ta faranta ran mahaifanta ne ya sa ta lamunce za ta aure shi, don haka bata wani zafafa ba saboda wannan karonma ta ce babu abin da za ta yi, tun da aure ba na ɗaya ba ba na biyu ba. Hasalima wasu ƴan uwan na nesa ma ba a gaya musu ba don gudun surutu. Ranar ɗaurin auren Raihan da gayya Malam ya kira Al'amin bayan ya gaida shi ya ce, "Al'amin ina son ka zo ka kaini wurin ɗaurin aure don yau da ƙafar hagun nan na tashi tana yi min ciwo." Al'amin ya kalli ƙafar Malam ya ce, "Subhanalla Daddy ka haƙura da zuwa tun da baka jin daɗi." Malam ya jinjina kai sannan ya ce, "Da ace da yuwar haka da na haƙura amma Raihan kamar ƴa take a wurina hasalima Mahaifinta ya mallaka min komai na aurenta." A hargitse Al'amin ya furta, "Aure kuma? Tun yanzu za ta yi aure?" Mamaki da dariya suka kama Malam ya ce, "Me ye naka a ciki? Ga abin da na ce maka ƙafa tana yi min ciwo ka zo ka kaini ɗaurin aure." A fusace Al'amin ya yi gaba Malam ya kalle shi yana ƙunshe dariyarsa don dama da biyu ya yi haka don ya harzuƙa masa zuciya, saboda har lokacin idan Malam ya tuna abin da Al'amin ya yi wa Raihan ransa sai ya ɓaci. Wani irin gudu Al'amin yake yi fuska a murtuke babu walwala don haka Malam ya dube shi ya ce, "Aminu ni ko wani abu yana damunka?" Al'amin ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce, "Lafiya ƙalau Daddy me ka gani?" Malam ya furta, "To ka ja ni a hankali don na ga gudu kake kamar za ka tashi sama, kuma yanayinka duk sai a hankali." Da to kawai Al'amin ya amsa baƙinciki ya mamaye zuciyarsa har suka ƙarasa ƙofar gidansu Raihan da ke cike damƙam da mutane, suna zuwa Malam ya ce masa, "Sauko mu je don babu jimawa kai za ka mayar da ni." Kamar Al'amin zai yi kuka ya ce, "Gaskiya ni ba zan je ba Daddy ba na son hayaniyar mutane." Malam ya yi murmushi sannan ya fice daga motar, Malam na fita Al'amin ya juya akalamar motarsa ya bawa gidansu Raihan baya sai dai jin zuciyarsa yake kamar za ta hudo ƙirjinsa, don da ace Malam ba Mahaifinsa ba ne babu yadda za a yi ya iya jiransa a ɗaurawa Raihan aure yana tsaye a wurin. Yana nan zaune ya ji an ɗaura auren Raihan tare da Alhaji Shatima akan sadaki dubu ɗari, maimatawar da maroƙa suke yi shi ya sake dagula lissafinsa har ya gagara haƙuri ya kira wayar Daddy don ya ce masa ya fito su tafi amma har ta katse ba a ɗauka ba. Malam bai fito ba sai da suka gama gaisawa da mutane sanaan ya yi wa Daddy Allah sanya alheri ya shiga mota, a lokacin Al'amin ya haɗa kai da sitiyarin mota yana jin ɗaci a zuciyarsa. Yana tayar da mota ya hango wani babban mutun da wata dakakkiyyar shadda yana tafe maroƙa na biye da shi da alama shi ne Alhaji Shatima, karaf ya ji Malam ya furta, "Al'amin ka ga Angon Raihan nan idan ma baka son hayaniya nan babu mutane ya kamata ka yi masa Allah sanya alheri tun da ga Mahaifinta can shi ma ka ƙarasa ku gaisa." Al'amin bai gama jin maganar Malam ba ya figi motarsa ya kamar zai bi ta kan Alhaji Shatima.

Daga cikin gida mata ne suke gudanar da yini sai dai babu wasu mutane da yawa, yawancinsu ƴan uwa ne da abokan arzƙi. Raihan ta yi kyau sosai an yi mata ɗinkuna gwanin birgewa sai shiga take tana fita, su Inno suma sun fito shar Daddy ya yi musu ɗinkuna kusan duk iri ɗaya ne. Bayan sallar magriba Daddy da kansa ya ɗauki Raihan ya kaita gidanta da ke unguwar Gaida, yana dire Raihan motocin su Mama Hafsa suka yi parking. Bayan shiga gidan Raihan nasiha suka yi mata sosai kowa maganarsa ɗaya ta riƙe mijinta hannu bibbiyu kamar yadda yake ƙaunarta, ba su ɗauki lokaci ba suka yi mata sallama suka tafi. Fitar su ke da wuya Alhaji Shatima ya shigo tare da abokansa biyu, Raihan tana jin su suna zolayarsa wata maganar idan suka yi har kunya take ji. Su ma ba su daɗe ba Alhaji Shatima ya yi musu rakiya sannan ya dawo wurin Raihan, cike da shauƙin so da ƙauna ya zame mata mayafi yana sakar mata murmushi. Ita ma murmushi ta mayar masa sannan sunne kanta ƙasa, sauka ya yi ya baje musu lodojin da ya shigo da su ya fara ƙoƙarin jan Raihan da hira don ya lura kunyarsa take ji ya ɗora da cewa, "Amarya bakya laifi." Murmushi Raihan ta yi ya ruƙo hannunta suka ba je a ƙasa ya fara bata kayan ciye-ciye a baki tana karɓa a kunyace. Don ba ƙaramin mamaki ta yi ganin yadda Alhaji Shatima ya iya soyayya kamar matashin saurayi ba. Bayan sun ci sun ƙoshi Alhaji ya miƙe don ya ɗauro alwala su gabatar da sallah, wayarsa ta fara ringing yana ɗauka wata baƙuwar lamba ya ga ta shigo kamar kar ya ɗauka sai kuma wata zuciyar ta ce ya ɗauka don ya ji wanda yake kiransa a wannan lokacin da yake shirin amarcewa da amaryarsa. Wayar ya kara a kunne tun bai yi magana ba ya ji an ce, "Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, don haka ka yi hanzarin zuwa gidan gonarka da ke By pass ta yuwu kafin ka je ka sa mu matattun awaki da shanunka idan kuma ka yi jinkira sai dai ka samu tokarsu."

Na ce ba🥵 Auren suger Daddy's fa duniya ne🤭🌚 Na so kammala book ɗin nan a wannan shafin amma sai a na gaba insha Allah, don sai Alhaji Shatima ya hallake mata wancan gayen Huzzy kenan☹️

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

51
Chapter 103 · 0% Book details