← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 110

Sashe 28

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Raihan ce shirye tsaf cikin doguwar riga kayan ba ƙaramin kyau suka yi mata, hannunta ɗauke da jakar makarantarta don tun dawowarsu daga India suka shiga first semester level 300 sai dai ba ta samu ta halarci makarantar ba. Da kanta ta ƙarasa wuri parking space ta ɗauki motarta, sai da ta je bakin gate ta fara zabga Horn. Da sauri Kabiru ya ƙarasa jiki na rawa ya buɗe mata ƙofa, da gudun gaske ta fice daga gidan ta ware sauti na tashi a cikin motar fuskarta ɗauke da ƙaton glass baƙi. A kan titin shigarta gate ɗin makarantarsu bisa tsautsayi motarta suka yi taho mu gama da wani matashin saurayi da ke kan babur ɗin lifan, sai dai Allah ya rufa asiri ba wata buguwa suka yi mai ƙarfi ba. A zafafe Raihan ta fito daga mota cikin masifa tana faɗin, "Kai wanne irin mutum ne da baka lura da gabanka..." Muryarta ce ta maƙale sakamakon tozali da ta yi da kyakkyawar fuskarsa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wacce ta dawo da saurayin daga tunanin da ya faɗa na firgicin abin da ya faru. Bai tanka mata ba ya fara ƙoƙarin saukowa domin ɗauko wayarsa da ta faɗi can gefe, da sauri Raihan ta tsugunna ta ɗauko masa tare da sa gefen mayafinta ta goge masa. Tana shirin miƙa masa ta riski muryarsa yana faɗin, "Na gode." Ya yi maganar yana karɓar wayarsa, har zai tada mashin ɗinsa ta furta, "Ka yi haƙuri." Raihan ta samu kanta da furta waɗannan kalaman, murmushi ya sakar mata sannan ya ce, "Ba damuwa." Raihan ta gyara tsayuwarta tana lumshe ido sakamakon jin yadda muryarsa take rikitata, tun da take bata taɓa tsintar kanta a cikin wannan yanayin ba. Mutane da dama sun nuna suna soyayyarsu a gare ta amma babu wanda ya taɓa yi mata balle ta ji wani abu daga gare shi. Tana tsaka da tunani ta tsinkaye shi ya kunna mashin ya yi gaba abin sa, firgigita ta ɗora idonta a kan katafaren gate ɗin makarantarsu. Tana nan tsaye har ta ga shigewarsa cikin, hannunta ta sa ta dafe gefen ƙirjinta ya yin da ta ji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, tana nan tsaye cikin duniyar tunani ƙarar horn ɗin motar da ke bayanta ta dawo da ita daga duniyar tunani.

ALLAH YA SA HUZAIFA YA BARI SOYAYYAR TA ƊORE😂

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

14

Kamar wacce aka zare wa laka a jiki haka Raihan ta fara takawa a hankali ta buɗe motarta, tana shiga ta bata wuta da ƙarfin gaske. Duk yadda ta so cimma matashin sai dai kamar an yi ruwa an ɗauke haka ta neme shi ta rasa sama da ƙasa, daga gefen hall ɗin da suke da lecture ta yi parking ɗin motarta. A kasalce ta ziro ƙafarta ta fara takawa kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, ɗaga kanta ta yi tana ɗan waige-waige don har lokacin bata cire rai da tsammanin ganinsa ba, a haka har ta ƙarasa bakin hall ɗin tana tafe tana saƙa da warwara. Zuwanta ke da wuya ƴan Department ɗin su suka fara yi mata ta'aziyya sakamakon mafi yawa daga ciki basu halarci gidansu ba, Raihan yaƙe ta riƙa yi musu amma sam hankalinta baya wurinsu. Tana nan tsaye Intisar ta ƙaraso sanye da coffee ɗin hijabi, kalarsa ba ƙaramin karɓarta ya yi ba. Ta baya ta rungumo Raihan tana faɗin, "Oyoyo Besty." Hararar wasa Raihan ta yi mata tana faɗin, "To ƙarasani ki huta kin ji." Hannuwa biyu Intisar ta sa a daidai kunnuwanta tana cewa, "Tuba nake na ƙaryaki ina na kama." Gabaɗaya suka saka dariya tare da rankayawa cikin block ɗin sakamakon zuwan malamin da zai yi musu lectures, Mr Samuel shi ne lectural da yake ɗaukansu Oral Engilsh ɗalibai na ƙaunarsa sosai sakancewar ya iya koyarwa, yana shiga ajin ya yi tsit saboda a dokarsa matuƙar kuna surutu nan take zai yi test a kan topic ɗin zai koyar a ranar, kuma matuƙar ya ɗauka yana amfani da shi. Tun shigowarsa Raihan ta kafe shi da ido lokaci ɗaya ta ji ta kawaɗaita da shi, sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tana son aiwatar da manufarta a kansa runtse idonta ke da wuya fuskar matashin saurayin nan ta faɗo mata a ƙwayar idonta. Ganin halin da take ciki ya sa Intisar murmusawa don ta fahimci abin da Raihan take buƙata game da Mr Samuel, a hankali ta ɗan zungurota tana cewa: "Wai yau lafiya Samuel yana lecture na ganki some how?" Muryar Raihan a raunace ta ce, "Ya tafi da zuciyata." Wata irin faɗuwar gaba Mugaza ta ji sakamakon jin magana Raihan, cikin ƙarfin hali ta wurga mata tambaya. "Wa kenan." Raihan ta manta shaf malami na ajin ta kwantar da kanta a kan desk muryarta na ci gaba da rawa kamar za ta yi kuka ta ce, "Kallo ɗaya ya yi min amma ya tafi da rayuwata, jin sa nake a ƙarƙashin zuciyata ta yadda duk bugun nufashi fuskarsa na walƙiya a fuskata. Sai dai kash..." Da sauri Intisar ta katse ta da faɗin, "Wanene shi? Ɗan gidan uban waye?" Ta yi wannan tambayar don so take ta ji daga bakin Raihan dukda zafin zuciyar da take ji a kanta, alwashi ta ci muddin Raihan ta furta waɗannan kalaman akan babban masoyinta Huzaifa za ta nuna mata iyakarta, don ta gwammaci ta halakata idan ya so ita ma su abar bauta su halakata kowa ya rasa. Raihan ta katsewa Intisar tunani da cewar, "Wani matashin saurayi ne, da alama shi ba kowa ba ne..." Nan take Raihan ta zayyanewa Intisar abin da ya faru tsakaninta wannan saurayin. Yanda Intisar take murna sai ka rantse da Allah ita ce mai saurayin, Raihan na shirin yin magana Dr Samuel ya hango su suna surutu. Da hannu ya nuno su yana kiransu, Raihan ko gezau haka ta miƙe ta nufi wurinsa Intisar ce take tafe jiki a sanyaye kamar mutuniyar kirki. Raihan tun bata ƙarasa wurinsa ba ya ce mata su fita, madadin ta yi takaici sai kawai ta bushe da dariya har sai ta bawa sauran ɗaliban mamaki. Tana fita Intisar ta bi bayanta suka zauna a dandamalin jikin block ɗin, Raihan na zaune ta runtse idonta nan take fuskar saurayin ta ci gaba da dawo mata. A fusace ta furzar da iska mai zafi, lokaci ɗaya faratan hannunta suka fara sauya launi, daga farare zuwa jajawur. Daga cikin lectura hall ɗin Dr Samuel ne ya fara jin wata irin juwa na neman ɗaukansa, cikinsa ya fara murɗa masa haka kawia ya ji kamar ana fusgar hanjin cikinsa. Tun yana iya daurewa har ya zage ya ƙwallah wata irin ƙara cikin fitar hayyaci, Raihan na daga waje ta bushe da wata irin dariya nan take hannuwanta suka fara dawowa daidai. Intisar ta dube ta cikin tsoron ƙarya ta ce, "Me yake faruwa Raihan?" Raihan bata kulata ba ta sauke idonta a kan wani narkeken jangwalagwada kamar tsuntsuwa tana tsaye ta cafe shi a haukace ta kaiwa kansa cizo, a daidai lokacin ɗaliban cikin block ɗin su suka fito da gudu sakamakon aman jinin da Dr Samuel yake yi, maza daga cikin ƴan Department ɗin su suka kama shi wasu suka wuce wurin hukumar makaranta don sanar da abin da yake faruwa. Carko-carko sauran ɗaliban suka yi dukda sun san Raihan na da aljanu amma ba su taɓa tsammanin za su ga tana gididdiba ƙadangare gida biyu ba, Wani irin huci ta fara yi mai ban tsoro haɗe da gurnani, tana yi tana tunkararsu ganin haka ya sa ɗaliban kowa ya fara yin ta kansu masu ciro waya suna yi mata suna yi daga nesa, Intisar ma wurin ɗaliban ta koma tana nuna tsoronta don duk wani abu da za a zarge tana ƙoƙarin kiyaye shi. Kafin wani lokaci tuni Malaman makarantar suka zo da motar makaranta aka ɗauki Dr Samuel sai dai tun kafin su je asibiti rai ya yi halinsa, amma ba su yi ƙasa a gwiwa ba sai da suka kaishi asibiti don tabbatar da haka daga bakin likitoci.

Raihan na tunkararsu ta fara fige ɗankwalin kanta, hannu biyu ta sa ya ɓark doguwar rigar jikinta don ma Allah ya sa akwai T-shirt a jikinta. Kasancewar rigar na da santsi nan take ta zuge ta faɗi ƙasa, Raihan daga ita sai ƙaramar riga da gajeren wando da ko cinyarta bai ƙarasa ba. Wasu daga cikin securities ɗin makarantar ne suka tunkari wurinta da niyyar kamata don su killace ta saboda suna gudun ta yi wa kanta tsirara a cikin jama'a. Ɗaya wanda ya kasance a kan gaba ya fi ɗayan kwari don na bayan yana da ƴan shekaru zai iya haihuwar Raihan, suna gabda ƙarasawa wurinta ta buga tsalle haɗe da wani kukan kura ta cafko kansa ta kafa masa haƙora a kunnesa. Kamar yadda kura take yagar nama haka Raihan ta yake masa kunne guda ɗaya, tana ɗagowa ta wurgar da fatar kunnen a ƙasa ta dubi saitin idonsa tana shirin kai haƙoranta Dattijon security ya kai mata ƙafa a ƙirji cikin shammata, a cen gefe ta faɗi kafin ta miƙe ya sungumi matashin securityn da yake cikin wani yanayi ya zuba da gudu, don tana yage kunnensa nan take ya sume.
Chapter 28 · 0% Book details