Sashe 33
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mommy ta ƙarasa yi wa Daddy tambaya tana tsare shi da ido babu alamar tsoro a tattare da ita. Shiru ya yi yana nazarin maganganunta, Mommy bata damu da haka ba ta ci gaba da cewa, "Duk wannan gatan da kake nuna mata sam ba soyayya ba ce, kuma ba zan taɓa alaƙanta Raihan da ciwon jinnu ba kawai don son raina ba. Uwani da muka shafe tsawon shekaru da ita ba mutum ba ce ƙaton aljani ne da ya shiga jikin Ƴarka Raihan, ɗazun nan muka fahimci haka ni da Inno idan kuma kana musu wataƙila idan ta gaya maka za ka ɗauki abin da muhimmanci, idan kana tantama ka duba cikin gidan nan kaf idan za ka sake ganinta." A wannan karon hankalin Daddy ya fi na koyaushe tashi, jikinsa har rawa yake ya dubi Inno da hargagin Mommy ya dawo da ita cikin nutsuwarta yana shirin yin magana Inno ta ce, "Audullahi!" Daddy ya amsa mata murya a sanyaye Inno ta ci gaba da cewa, "Idan baka haɗa ni da Zinaru ta kaini albasu ba Alhaji Babba ya dawo duniya. Ganin idona na ga Uwani da Kofato har tana gaya mana ita ba mutum ba ce yau mai hanani tafiya Albasu sai Allah." Goggo na maƙale a bayan Daddy ba tare da ta fahimci a wurin wa take ba, tana miƙa hannu ta shafo gemun Daddy a zabure ta leƙa fuskarsa tana faɗin, "Yau na shiga aljanna na kasa fitowa yau ni ce maƙale a bayan Audullahi, astagafirullah Allah ka yafe min me ya kaini bayan siriki ana zaune ƙalau?" Goggo ta ƙarasa maganar tana zazzage ɗankwali sai da ta ɗaura shi akanta ta ce, "Me zan zauna na ci gaba da yi a gidan nan ban da abin kunya, wannan Idan ƴan Albasu suka ji kashina ya bushe gara na tafi sawuna a likafa tun Audullahi bai yanke hukunci ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyi ya ce, "Zainabu meye mafita?" Mommy kamar dama jira take ta ce, "Mafita dole ka nemo malaman Islamic chemist ɗin da baka son a kira su zo su yi mata ruƙiyya." Inno ta hangame baki tana tafa hannuwa ta ce, "Kai ni dai wallahi Ƙasimu ya nakasa min rayuwa da ya ɗoraka a turbar rayuwar masu jajayen kunne. Kai dai Audullahi da kasan taimakon da malamai suka yi maka kana ƙarami da baka guje su ba, wallahi ko labarin ƙarzuwarka na baka ya isheka ishara, a bar batun fitsarin kwance da sannu Allah sannu Ma'aiki da yaya muka samu ka daina, ka san irin tashin hankalin da na shiga lokacin da na ji za ka yi aure, na ce na ga ta kaina yaro ya zo yana fitsarin kwance mace ta raina shi. A'a wannan lamarin ba na aikin likitoci ba ne, ko rashin haihuwar matarka Allah ya sani ina zargin sheɗanu sun murƙushe maka ƙwayoyin hallita, don kar na yi shisshigi shi ya sa na saka muku ido amma da tuni na kira Ɗan wanzam har gidan nan zai zo shi da Kawunsa Malam mai farin allo sun baku magani." Daddy tuni ya gama ƙosawa da maganar Inno, tun bai ƙarasa jin abin da take faɗa ba ya miƙe yana faɗin, "Yanzu bari na kira Alhaji Munniru na ji a ina zan samu wurin da za a karɓo mata magani..."
"Ba sai ka kira kowa ba, ga mu ga Waraka Islamic chemist a titin sharaɗa, kai tsaye ɗaukan yarinyar nan za mu yi mu wuce da ita, da zafi-zafi kan daki ƙarfe." Mommy ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Inno ta yi fiƙi-fiƙi da ido cike da firgice ta ce, "Billahillazi idan kun ga ba mu biku wurin nan ba Allah ya watsa mana albarka, haka kawai ku fice ku bar mu aljanu su dawo su casa hatsi a kanmu?" Mommy da yake neman mafita take bata jira cewarsu ba ta ce, "Shi kenan duk yadda kuka ce haka za a yi." Daddy da kansa ya tunkari ƙofar ɗakin Raihan sai dai lokaci ɗaya ya ji wani irin tsoro ya ɗarsu a zuciyarsa, yana daga tsaye ya fara jin wani irin gurnani kamar gurnanin zaki. Da sauri ya yi baya yana kallonsu Mommy a tsorace, Mommy na shirin yin magana ya ce, "Wallahi ji nake kamar ciwonta ya tashi gurnanin wani abin nake ji." Inno tuni cikinta ya kaɗa, ta maƙale a bayan Goggo tana leƙe. Mommy ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hankali ta yi ta maza bakinta ɗauke da addu'a ta kalli Daddy ta ce, "Babu abin da ya gagari ubangiji, mu yi addua mu shiga ɗakin." Da sauri Daddy ya fara motsa baki yana biya ayatulkursiyyu yana tura ƙofar Raihan ta yi kuka kura ta faɗo kansu cikin wani irin gurnani mai tafe haushi kamar haushin kare. Idanunta a kakkafe suke kanta ya hargitse ga faratanta tuni suka fara sauya launi. Kafin su farga tuni ta fisgi hannun Daddy ta shige da shi ɗaki, ganin haka ya sa Daddy razana ya manta da addu'ar da yake yi ya fara ihu yana neman taimako. Yagarsa ta fara yi ta ko'ina da faratanta tana ƙoƙarin kai bakinta jikinsa Allah ya bashi sa'a ya hamɓareta ya doka ƙofar banɗaki ya shige ciki yana sauke ajiyar zuciya. Sai dai gabaɗaya ya gama tsinkewa lamarin don yadda ya ji tana bugun ƙofar tamkar za ta ɓalleta, a haukace ta juyo wurin ƙofa don mommy na wurin tana ihun kiran Daddy tana ganin Raihan ta yo kanta da gudu ta yi gaba cikin tashin hankali, Su Inno da goggo da rarrafe suka fice daga falon ban da ɗankwalaye da zannuwansu babu abin da suka bari a wuri. Da ƙyar Mommy ta samu ta fice daga falon tana fita harabar gidan ta ja ƙofar ta rufe da ƙarfi amma dukda haka sai da Raihan ta yage bayan Mommy da faratanta.
Kabiru na kwance a ɗakinsa ya ji shigowarsu Inno ganin yanayin da suke ciki ya sa ya duburburci yana faɗin, "Hai Inno lafiya kuwa?" Goggo ta yi karaf ta ce, "Kai Kabiru buɗe mana ƙofa maza Albasu za ni." Kabiru ya dubi su Inno daga su sai ɗan fatarinsun zai yi magana ya ji ihun Mommy da sauri ya fito yana tambayarta, hankali a tashe mommy ta shiga nuna masa gidan tana faɗin, "Wallahi ciwon Raihan ne ya tashi Daddy na ciki ina tsoron kar ta yi masa illah." Cikin Kabiru ne ya kaɗa a tsorace ya ce, "Hajiya ya za mu yi ga Goggo ta ce Albasu za ta tafi." Mommy da hawaye ya gama jiƙe mata fuska ta ce, "Don Allah bar batun Albasun nan, wuce ka je Waraka a nan titin sharaɗa islamic chemist ɗin yake don Allah ka kira mana malamin." Kabiru ya yi jim ganin kamar ba gane abin da yake nufi ba, Mommy na hango hijabinta a kan igiya da aka yi wanki ta fisgo shi da sauri ta saka tana faɗin, "Kabiru ka kula da su Inno karka bari su fita." Tana gama maganar ta fice da gudu, Inno na shirin bin ta Kabiru ya sha gabanta ya datse ƙofar da ɗan mukulli ya cire ya koma ɗaki.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
17
Inno sai da ta kalli hagu da dama ta ga babu kowa a harabar gidan daga ita sai Goggo sai kawai ta faɗa ɗakin Kabiru tana faɗin, "Kai yaro idan kana neman albarka ka buɗe mana gida mu fice." Kabiru ya kauda kansa gefe ya ce, "Inno ko ba a ce karna barku ku fita ba ai bana barku ku fita a haka ba, ku dubi kayan jikinku fa. Gaskiya bari na miƙo muku zannuwan Hajiya ku ɗaura, don zamanku haka bai kamata ba." Goggo ta ja dogon tsaki ta ce, "Kai muna maganar zuwa Albasu kai kana cewa a ba mu zani, shi aljani ina ruwansa da ɗaura zani." Inno da ta gama zuwa wuya ta ce, "Kai Kabiru kake ko wa? Yau da idanunan nawa na ga aljana ko tsirara ka gammu ba za ka yi mamaki ba." Da sauri Kabiru ya ƙunshe baki yana faɗin, "A'uzubillahi gara dai da kuke cikin sitira." Yana gama maganar ya miƙe ya fice ya ɗaukowa su Inno zannuwa suka ɗaura, suka yi jugun-jugun sai dai kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin tashin hankali.