← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 110

Sashe 52

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani irin baƙin hayaƙi ne yake fitowa daga ko'ina na sassa jikinta, ya yin da bakinta yake fitar da harshen wuta ƙasanta na fesar da wani irin tafasasshen ruwan mai yauƙi. Ɗaukan bil'adam ta riƙa yi ɗaya bayan ɗaya tana wurgawa cikin bakinta dukda kasancewarsu halattatun ƴan ƙungiya, ganin haka ya sa suka fara nema ceton ransu suna tserewa da ƙafafuwansu. Ƙanananun aljanun da suke wurin a tunaninsu sun tsira sai dai ba su yi aune ba suka riski Abar bauta ta faɗa ɗaukan wasu daga cikinsu tana haɗiyewa. Lokaci ɗaya wurin ya kacame da iface-iface da kururuwa don abin da ba su taɓa gani ba ne, Hatsabibiya gefe ta zauna ta zurawa Abar bauta ido sai da ta gama duk abin da take yi sannan ta furta, "Ko ba komai kin rage mana ƴan ƙungiya sai dai hakan ba yana nuna ƙungiyarmu ta ci baya ba, amma kina ganin wannan ɓacin ran naki zai kai mu ga cin abin da muke buƙata? Aikin gama ya gama tun da Huzaifa ya riga da gama ɓata mana shiri tun da ya kashe mata miji, na ci burin ɗora duk wani shirinmu akan ta bayan aurenta domin shi zai kaimu ga cimma burinmu." Wani irin huci Abar bauta ta yi sannan ta ce, "Laifin Mugaza ne kuma dole za mu ɗauki mummunan mataki a kanta. Ita idanunmu ce kuma kunnuwanmu ce mun sakakankance akan za ta ba mu jawabin halin da ake ciki amma wannan karon tana neman ba mu kunya, na fara zargin tana sane da komai akan a duk hukuncin da Huzaifa ya ɗauka." Hatsabibiya na shirin yin magana suka ji an furta, "Babu sa hannu ko kaɗan akan abin da Huzaifa ya aikata hakazalika ni kaina yaudarata ya yi domin bai taɓa nuna min ya samu lafiya ba. Kullin cikin kwanciya yake amma jiya kawai na neme shi na rasa, ina ganin Huzaifa buɗe mana hanya ya yi don mu ƙara miƙe wa tsaye don mu san ta yadda za mu shawo kan matsalar. Huzaifa ya fargar da mu baccin da muka fara domin na lura da sabon shiri ya dawo na tabbata ko ni ce na kawo masa wargi akan Raihan zai iya kawar da ni." Mugaza ta yi dogon sharhin tana ƙarasawa cikin tsibirin.

Asubar fari bayan sun idar da sallah Daddy yake sanarwa da Mommy cewar ƙarfi takwas na safe za a yi jana'izar Salim a ƙofar gidansu, hakan ne ya sa suka nemi sallama a lokacin don tun farkowar Raihan taƙi yarda su yi mata wata allurar baccin. Kai tsaye daga asibitin gida suka wuce suka kintsa sannan suka yi mota uku suka wuce gidansu Salim, tun da aka doshi hanyar gaban Raihah yake tsananta faɗuwa nan take jikinta ya fara karkarwa. Suna zuwa mommy ta riƙe hannunta suka shiga cikin gidan, su Farida na hango Raihan suka tafi da sauri suka rungume ta suna kuka. Da ido mutane suka riƙa bin su da kallo gwanin ban tausayi, sainda Mahaifiyar Salim ta ƙarasa ta riƙota tare da mommu suka wuce ɗakinta. Mahaifiyar Raihan sosai ta yi wa Rainan nasiha sannan ta ja zuwa ɗakin da aka shirya gawar Salim don ta yi masa addu'a kafin a tafi da shi. Tana tafe gabanta na faɗuwa haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin, tana shiga ya same shi a kwance an gama haɗa shi. Jikin Raihan nan take ya fara karkarwa a hankali ta zube a wurin tana fara yi wa Salim addu'a, lokaci ɗaya kuka ya kwace mata ta jingina kanta a jikin Kan Salim ta ci gaba da rera kuka mai tsuma zuciya. A hankali Mommy ta riƙo hannunta tana shirin fito da ita sai gani ta yi numfashinta yana sama, kafin Mommy ta yi wani yunƙuri Raihan ta faɗi a wurin.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana 0706 206 2624

29

Hankali a tashe Mommy ta yi kanta da sauri Mahaifiyar Salim ta ɗauko ruwa aka fara yayyafa wa Raihan, a hankali take sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idanunta tana kallon su Mommy. A daidai lokaci Mahaifinsu Salim da sauran ƴan uwansa suka shigo ɗakin suna faɗin, "Za mu ɗauke shi mu yi masa sallah mutane sun gama taruwa." Hawaye ne ya ciko idon Mahaifiyar Salim, Raihan na jin haka ta fara bin su da kallo a zuciyarta take ayyana shi kenan ita da Salim sun yi bankwana. Tana raɓe a gefe suka ɗauke shi suka fice da shi lokacin ƙafafuwanta suka fara karkarwa. Tsugunnawa ta yi a wurin don yadda take ji ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukanta ba. Zoben hannunta ta zurawa ido tana tuna ranar Dinner su da Salim ya saka mata shi a hannu, murza ɗan yatsanta ta fara yi a hankali kamar almara sai jin irin muryar Salim ta yi an ce, "Ki ba ni zobena na tafi da shi." Zaburar da ta yi ne ya fargar da Mommy da sauri ta riƙe ta tana faɗin, "Ke Raihan ina za ki?" Raihan ta nuna bakin ƙofar fita ta ce, "Wallahi Salim magana yake min, don Allah ku duba bai mutu ba." Ganin yadda Raihan ta firgice musu lokaci ɗaya ya sa Mahaifiyar Salim ta dubi Mommy ta ce, "Hajiya mai zai hana ku wuce da Raihan gida ina ganin kamar zai fi." Mommy ta yi jim sannan ta ce, "Shi kenan Hajiya Allah ya gafarta masa, za mu wuce insha Allah zuwa anjima zan dawo." Maman Salim ta yi murmushin ƙarfin hali ta furta, "Karki damu Hajiya ki kula da ita don tana cikin wani irin hali ko baki dawo ba anjima babu komai, Salim addu'a kawai yake buƙata amma yana da kyau ita ma a ji da ita." Daga haka Mommy ta riƙe hannun Raihan gam suka fito duk in da suka gifta mutane kallonsu ake yi. Lokacin da su Mommy suka fito a lokacin aka gama sallarta Salim har an saka gawarsa a mota za a wuce da shi, wasu daga cikin masu rakiyarsa na cikin mota wasu na kan mashina wasu ma da ƙafa suke takawa. Ganin haka ya sa Mommy ta ja hannun Raihan suka koma da baya, sai da suka jima a tsaye mommy ta fahimci masu rakiyar gawar sun yi nisa sannan suka fito suka shiga mota suka wuce gida. Suna zuwa gida Raihan ta wuce ɗakinta ta turo ƙofa, kan gado ta faɗa lokaci ɗaya ta saki wani irin marayan kuka. Sai da ta yi mai isarta ta tashi zaune ta takure wuri ta fara ayyana irin rayuwar da suka yi da Salim, ta jima ita kaɗai a zaune gabaɗaya rayuwarta ta yi mata zafi. Lokaci-lokaci take share hawayenta tana yi wa Salim addu'a. Tana nan zaune ƴan jarida suka yi wa gidan Iyayenta ƙawanya, duk yadda mommy ta so hana su naɗar rahoton Raihan abin ya ci tura sai da suka yi mata hikima har ta amince musu. A falo Raihan ta same su a zaune suna ganinta kowanne ya fara gyara abin naɗe sautinsa tare da faɗin, "Sannu Hajiya ya ƙarin haƙuri." Da ido Raihan ta bisu hawaye na zuba, nan take suka fara jero mata tambayoyin abin da yake tafe da su. Sai da ta share hawayen idonta sannan ta ce, "Tabbas na yi babban rashi saboda Salim yana ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da shi ba, na yi rashin masoyi na rasa Salim a lokacin da nake tsananin ƙaunarsa. Ni na san irin abin da nake ji a zuciya har yanzu gani nake kamar tatsuniya ake gaya min akan mutuwar Salim, kunnuwa na jiyo min sautinsa amma mutane gaya min suke Salim ya mutu, gabaɗaya na rasa wanda zai ce min Salim yana raye ko na ji daɗi har kuma kuna ganin Salim ya rasu ko..." Raihan bata ƙarasa magana ba kuka ya ci ƙarfinta da sauri ta faɗa ɗakinta. Kalaman Raihan ba ƙaramin sanyaya musu jiki ya yi ba, daga haka suka yi wa su Mommy gaisuwa sannan suka kama gabansu. Haka taron gidajen bikin ya koma gidajan zaman makoki. Kullin sai Mommy da ƴan uwanta sun je gidan su Salim dukda bata jimawa saboda ba ta son barin Raihan ita kaɗai a gida.
Chapter 52 · 0% Book details