Sashe 57
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kwance take daga ita sai ƴar ƙaramar riga iya cikinta, ɗan gajeren wandonta ko gwiwa bai ƙarasa ba. Mama Uwani ce ta shigo ɗakin ta zauna a gefenta haɗe ta tallafo ta jikinta tana shafata ta ce, "Uwar ɗakina hutawa kike yi." Raihan ta ɗago ta ce, "Huta wa nake Mama Uwani ya aiki?" Mama Uwani ta kai hannu ta ci gaba shafa saman cinyoyin Raihan haɗe da bayanta ta ce, "Uwar ɗakina kin guje ni yanzu ke bakya kewata?" Raihan ta janye jikinta haɗe da tashi zaune ta ce, "Mama Uwani na gaya miki ba na buƙatar ki riƙa taɓa min jiki." Mama Uwani ta miƙe a fusace ta ce, "Ai dama na daɗe da sanin an yi mana farraƙu a tsakani kuma da ni kike zancen." A fusace Raihan ta miƙe ta ce, "Mama Uwani ni kike gaya wa haka? Tsaki Mama Uwani ta yi ta fice daga ɗakin, da sauri Raihan ta bita amma ga mamakinta sai ta ganta a wani ƙaton fili. Waige-waige ta fara yi don kanta ba ƙaramin juyewa ya yi ba, ganin bata da mafita ya sa ta fara tafiya har ta isa bakin wani ƙaton kogi. Wani ƙaton baƙin sa ta hango yana tunkarota yana tafe yana jijjiga kansa, ganin girma da munin san ba ƙaramin razana Raihan ya yi ba. Hankali tashe ta fara gudu don ta lura kanta yake san ya yi gadan-gadan, tana tafe yana biye da ita har ta yi masa nisa sai dai tana shan wata kwana ta ci karo da shi. Da sauri ta ja da baya ƙirjinta yana bugawa da ƙarfin gaske bata yi aune ba ta ji ya fisgi hannunta ya yi gaba da ita, cikin matsanancin tashin hankali ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara haɗe ta zabura wanda ya farkar da ita daga nannauyan baccin da ya yi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ta riƙa sauke wa jikinta na rawa a daidai lokacin Mommy ta turo ƙofar ɗakin tana faɗin, "Raihan lafiyarki kuwa kike yi mana ihu a gida?" Ganin yanayin da Raihan take ciki ya sa Mommy ƙarasawa bakin gadon ta ce, "Raihan! Me yake damunki?" Raihan ta ruƙo hannun Mommy har lokacin jikinta na rawa ta ce, "Wallahi wani mafarki na yi mommy daga kwanciya bacci." Mommy ta kalle ta sosai ta sake maimaitawa, "Mafarki? Mafarki wane iri?" Nan take Raihan ta zayyane wa Mommy duk abin da yake faruwa sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi na yi kewar Mama Uwani ko tana wace duniyar yanzu oho?" Hankalin Mommy ba ƙaramin tashi ya yi ba, da sauri ta riƙo hamnunta ya ce, "Mu je ɗakina ki huta a can." Ba musu Raihan ta bi bayan Mommy suna zuwa Mommy ta kunna karatun Alƙur'ani, Raihan ta kwanta akan gadon Mommy ita kuma ta zauna a gefenta tana shafa kanta. Tunani kala-kala ne ya riƙa zarya a birnin zuciyarta tana Allah-Allah Daddy ya dawo don ta sanar masa abin da yake faruwa, don ko da wasa ba ta fatan Raihan ta riƙa ire-iren mafarkin nan saboda ba alheri ba ne. Baccin da Raihan bata koma ba kenan, ita kanta ta jima tana maimaita yanayin mafarkin da ta yi a zuciyarta, amma tunaninta ɗaya Mama Uwani ko tana wace duniyar don ba ƙaramin sabo suka yi da ita ba, dukda ta ji Mommy ta ce wani dalili ya dakatar da ita da yi musu aiki gabaɗaya. Mommy na jin shigowar Daddy ta miƙe ta fice daga ɗakin, a falo ta same shi ya kunna television yana kallon labarai. Murmushi ya yi mata yana miƙa mata hannu, martanin murmushi ta sakar masa cikin yaƙe ta zauna a gefensa ya tallafota da hannu ya ce, "Ni kam matar nan ban gane wa yanayinki ba. Tun a Dubai nake zarginki don wallahi duk kin sauya kamar ba ke ba." Kallonsa ta yi don bata fahimci in da maganar Daddy ta dosa ba ta ce, "Daddyn Raihan ni fa ban gane zagaye-zagayen nan naka ba, me kake nufi kana nufin ƙasar wasu tafi karɓa ta kenan?" Daddy ya yi dariya sannan ya ce, "Zainab ga ki dai shekarun sun fara yawa amma wani abin idan kika faɗa kamar Raihan." Hannunsa ya kai kan cikinta ya ce, "Jikina yana ba ni akwai ajiyata a nan." Mommy zaro ido waje ta yi ta kalli Daddy ta ce, "Don Allah ka daina faɗin wannan maganar Daddyn Raihan, tsofai-tsofai da ni wace irin haihuwa kuma? Yanzu da Raihan na tare da Salim ɗan/'yarta da sun doshi shekara har da wani abu." Daddy ya jinjina kai ya ce, "Nawa kike Zainab kawai don Raihan ta yi tsawon ƙafa ni kin rufa talatin kuwa?" Hararar wasa Mommy ta yi masa ta ce, "A'a ka manta ashirin zan yi." Ta sauya murya cikin shagwaɓa ta ce, "Wai don Allah Daddyn Raihan me ka mayar da ni?" Daddy ya yi dariya ya ce, "Yarinya mana." Mommy ta jingina da kujera ta ce, "To ka sauke don wallahi ni ma girma ya zo." Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Serious Habibty ina zargin ciki gare ki don tun kafin mu tafi Dubai na fara zargin haka." Mommy ta yi sak jiki a sanyaye ta ce, "Ni wallahi ba ciku gare ni ba, don Allah yanzu na samu ciki na cewa mutane me? Kawai sai Raihan da su Inno su wayi gari ina tura ciki gaba?" Daddy ya yi dariya har da riƙe ciki ya ce, "Su Inno da Raihan ba sun san kina da mijina, yanzu dai yaushe rabonki da baƙon wata?" Mommy shiru ta yi ta faɗa duniyar tunani nan take gabanta ya yanke ya faɗi.
Tunawa ta yi sam bai zo mata ba saboda tun kafin tafiyarsu Dubai take sa ran ganinsa amma har suka tafi bai zo ba, zuwan su Dubai sai ta manta da komai sai yanzu da Daddy ya tuna mata. Idonta ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "Wallahi tun kafin mu tafi Dubai nake sa ran ganinsa bai zo ba." Daddy ya wara hanninsa haɗe da cewa, "Shi kenan kin ga na ci gari." Mommy ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba amma don kar ga nuna wa Daddy ya sa ta kawar da zancen da cewar, "Daddyn Raihan da matsala fa." Ya kalleta cikin nutsuwa ya ce, "Matsala kuma? Wacce iri?" Nan take mommy ta zayyane masa irin mafarkin da Raihan ta yi, kai kawo Daddy ya fara yi cikin damuwa ya furta, "Huzaifa-Huzaifa. Huzaifa ba zai bar min yarinya ta sarara ba ne wannan waccen irin rayuwa ce. Ni ina zargin ba shi ya cire wa yarinyar nam son kula samari ba kuwa? Kina ga kowa ya nuna yana son Raihan za ta fara maganar tsohon mijinta, yanzu haka rayuwar yarinyar nan za ta ƙare?" Mommya ta ƙarasa wurim Daddy ta riƙo hannunsa sai da suka zauna ta ɗauki sauran ruwan da ya sha ta miƙa masa, ajiyar zuciya ya yi sannan ya karɓa sha. Mommy ta dube shi cikin ƙarfafa gwiwa ta ce, "Idan aka san ciwon abin da yake damun mutum kamar an ci rabin magani ne, sannin Raihan na tare da wannan shaiɗanin ba ƙaramar rahama ba ne a wurinmu. Mafita kawai mu ci gaba da yi mata addu'a muna nema mata magani dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma wannan abin yana daga cikin shafin ƙaddararta. Fatanmu akanta Allah ya bata lafiya ya tsare dukkan musulmi bakiɗaya." Daddy ya amsa da amin sannan ya fara tunanin zuwa don karɓo wa Raihan magani. Sun jima suna tattauna wa akan matsalolin da suke damun Raihan sannan mommy ta ƙarasa ɗakin su Inno don tun dawowarsu da suka shige ɗaki bata ƙara jin motsinsu ba.