← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 110

Sashe 89

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tun bayan auren Raihan sai gidan ya yi wa Kabiru wani iri, duk da gabannin bikinta ba wani yawan hira suke ba amma kaɗaicinta bai dame shi kamar bata gidan ba. Ranar da aka kaita gidan mijinta kusan kwana ya yi yana juyi don tuni zuciyarsa ta riƙa yi masa tunane-tunane kala-kala, so da ƙaunar Raihan suka ci gaba da nuƙurƙusarsa a haka har gari ya waye. Haka ya ci gaba da danne soyayyarta kullin sai ya yi addu'ar Allah ya yaye masa sonta don ya gama tabbatar da cewar ya rasa Raihan har abada, tun da ga shi ta shafe wasu kwanaki a gidan mijinta lami lafiya. Lokaci-lokaci tana kiransa su yi waya har ta tambayi jikin Maryama don ta san tana ɗauke da juna biyu, ko a waya idan ta kira shi ta rinƙa yi masa tsiyar tun da ta yi aure bai zo gidanta ba. Kabiru sai dai ya yi murmushi ya ce mata zai zo amma gani yake ba zai taɓa iya zuwa gidanta ba, har ya ganta da wani namijin a matsayin mijinta, saboda shi kaɗai ya san irin kishin Raihan da yake ɗawainiya da shi a birnin zuciyarsa. Watanta biyu da aure wata ranar Asabar su Inno wuro suka kira Kabiru hankali a tashe Maryama na naƙuda amma ta shafe wuni guda idan haihuwa ta zo gadan-gadan sai ta koma, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi ba don haka nan take ya turawa Baffansa kuɗi ya ce su tafi babban asibitin garinsu kafin ya ƙaraso. A lokacin ya kira Daddy ya sanar masa da halin da ake ciki, kasancewar wata ya yi nisa ba a yi albashi ba Daddy ya ɗebi kuɗi masu yawa ya bashi, ya ja kunnensa akan su tabbata sun kai Maryama asibiti. Bayan wasu mintuna Inno wuro ta kira shi take sanar masa sun je asibiti amma an tabbbatar musu da CS za a yi mata saboda ta gama galabaita ba za ta iya yunƙurin haihuwa da kanta ba. Tun Inna wuro bata gama maganar bata Kabiru ya amsa mata, don ya fi son Maryama ta rabu da cikin jikinta lafiya saboda a ƴan kwananin nan kullin sai ya yi mummunan mafarkinta. Lokacin da Kabiri ya isa garin an yi wa Maryama aiki lafiya, Inno wuro ta dubi Kabiru a lokacin likitoco sun tafi da Jaririn Maryama don duba lafiyarsa ta ce, "Kabiri hai sai dai mu yi haƙuri da abin da Allah ya ba mu..." Zaro ido Kabiru ya yi ya ce, "Inno ba dai Jaririn ya mutu ba?" Jiki a sanyaye Inno wuro ta ce, "Yana da Rai sai dai ba daidai yake ba." Kabiru na shirin magana wata Nurse ta shigo da Jaririn naɗe cikin showel, Inno ta miƙa wa sannan ta fice daga ɗakin. Kabiru ne ya miƙa hannu ya karɓi jaririn sai dai nauyisa tamkar ƴaƴa biyu aka haɗa a wuri ɗaya, yana ido biyu da jaririn zumbur! Ya miƙe sakamakon tozali da ya yi da jaririn mai ɗauke da wata irin hallita. Kan jaririn ya kusa na jarirai huɗu ga idanunsa a warƙale, hannuwansa da ƙafafuwansa duk a juye. Jikinsa ne ya fara wata irin karkarwa, kansa ya sara masa wata irin juwa za ta ɗebe shi. Nan take fasalin Kabiru ya sauya muryarsa ta canja daga fasalin harshen fulani zuwa ta tsurar bahaushe. Dangwarar da jaririn ya yi akan gado cikin wata irin murya ya furta, "Tabbas Abokantaka ita ma Ƴan uwantaka ce, wannan ba jaririn Aminina ba ne an taɓa masa shi. Haƙiƙa Jikan Jabbul-ƙasi ka taɓo wa kanka tsuliyar dodo domin a wannan karon na rantse da zatin Ubangiji ba za ka sha daga hannuna ba. A baya ma saboda ba hurumin abokina ka shiga ba da na nuna maka iyakarka, kuma na yi nisan zango sai daga baya na samu labari amma a wannan karon zan nuna maka ina girmama aminantaka." Hankalin Inno Wuro ba ƙaramin tashi ya yi ba muryarta na rawa ta furta, "Ibrahim ka dubi girman Allah ka yi haƙuri wannan Ɗa da kake gani haka Allah yake son ganinsa." Kallon Inno Wuro ya yi sannan ya kai hannu ya cakumi wuyan jaririn ya furta, "Wannan ba jinin Abokina Kabiru ba ne wannan wani bawan Aljanin Jabbul-ƙasi ne kuma a yau ba sai gobe zai tabbatar da ni ba kanwar lasa bane."

Eheeem 🤭 Nace ba. Kun tuna wanda ya taɓa tare Kabiru lokacin da aka tsorata shi zai bar aikin gidansu Raihan, idan baku manta ba a take ya yi masa nasiha kuma ya ɓace.🌚 Wanene Ibrahim ya aka yi Inno wuro ta san da zamansa? Shin ya za ta kaya tsakanin Ibrahim da Huzaifa? Ina labarin gidansu Raihan za ta ƙwato mijinta ko yaya?🫣

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

46
Chapter 89 · 0% Book details