Sashe 47
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Akwana a tashi babu wuya a wurin Allah haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa, wata rana Raihan ta fita shopping ɗin kayan shafe-shafenta da turarruka a WAHIDAH SHOPPING COMPLEX. Kayan shafa ta siyo har ta kusa zuwa wurin Accountant don ta biya kuɗi ta manta ba ta ɗebo da turarruka ba, da sauri ta juya don ta lura yamma ta ƙarato sosai ga shi Mommy ta ce karta sake ta kai magriba a waje, juyawar da za ta ci suka yi gware nan take kayan da ke hannuwanta suka tarwatse a wurin, wayarta ta faɗi daidai ƙafarsa. Kusan tare suka miƙa hannu don ɗaukar wayar da sauri ta ɗago tana kallonsa, karaf suka haɗa ido da shi. Wani shu'umtaccen ƙamshi ne ya doki hannunsa ga wani irin kwarjini da ya yi mata. A hankali ta janye idonta sakamakon kasa jure kallon da yake yi mata, cikin inda-inda ta furta. "Am...Kawo...Bari na kwashe." Ta ƙarasa maganar tana miƙa hannunta za ta ƙarɓi wayar, janye hannunsa ya yi yana ci gaba da kallonta cikin wata sasaanyar murya ya furta, "Ni ne mai laifi don haka a bar ni na goge laifina." Ajiyar zuciya ta sauke don muryarsa ba ƙaramin kuwwa ta yi mata a dodon kunnen ba, a hankali ta ja gefe ya tsugunna ya fara tattare kayan sannan ya ce, "Kin gama ne?" Girgiza masa kai ta yi cikin kasalalliyar murya ta ce, "Zan je wurin turare." Gaba ya yi yana riƙe da kayan ta ƙarasa ta fara ɗaukan irin waɗanda take amfani da su, sai da ta gama ta miƙa hannu za ta karɓa tana faɗin, "Na gama bari na wuce gida." Hannu ya sa ya sake ɗebo mata waɗanda ya fa ta ɗiba da farko, Raihan ta fara bin sa da ido kamar za ta yi masa magana sai kuma ta ja bakinta ta rufe don ta ga iya gudun ruwansa. Yana gama ɗiba ya wuce wurin biyan kuɗi kafin Raihan ta zo har ya ciro ATM ɗin sa ya bayar. A hankali Raihan ta kalle shi ta ce, "Ka bari da kuɗi a wurina." Yamutsa fuska ya yi yana girgiza kai ya ce, "Gaskiya na wurinki sun yi kaɗan, na san ko 50k ba su kai ba." Waro ido Raihan ta yi da mamaki ta ce, "Kai ta ya ka sani." Dariya ce ta suɓuce masa ganin lokaci ɗaya ya yi mata dabara. Raihan na ganin haka ta gane wautar da yi lokaci ɗaya ta tura baki gaba ta ce, "Ai ATM ɗin biyu na taho da su idan wannan bai kai ba sai na ciro ɗayan." Murmushi ya yi mata ya miƙa hannu ya karɓi reciept sannan suka fito ya raka har wurin mota, hannu ta miƙa masa za ta karɓi kayan ya girgiza mata kai yana cewa, "Ba zan baki ba sai kin biya tukwici." Cikin rashin fahimta Raihan ta ce, "Tukwici kuma? Dama ai ba ni nace ka biya ba, ba na ce zan biya ba ka ce za ka biya?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya buɗe murfin motarta saka kayan a ciki ya ce, "Eh! Lambarki za ki bani." Kunyace ta kama Raihan don ita bata taɓa kawo abin da zai karɓa ba kenan."
Tana cikin tunani ya miƙa mata waya a hankali Raihan ta karɓa ta saka masa lambarta, nan take ya yi kira lambarta. Daga nan suka yi sallama sannan Raihan ta shiga mota ta tafi, sai da ya ga tafiyarta sannan shi ma ya koma cikin Store ɗin don ya manta da tashi siyayyar. Raihan na zuwa gida ta zube a falo nan ta hau bawa Mommy labarin abin da ya faru tsakaninta da matashin saurayin, su Inno ban da murmushin farinciki babu abin da suke yi. Duk da bata ce musu saurayinta ba ne amma kana ganin yanayin yadfa Raihan take hirarsa za ka fahimci ya kwanta mata. Tana tsaka da basu labari sai ji ta yi wayarta ta yi ƙara, kallon Mommy ta yi ta ce, "Mommy wallahi shi ne ya kira." Ta ƙarasa maganar ta miƙewa za ta nufi ɗakinta, Mommy ta yi dariya tana cewa:
"Don Allah Raihan ki san yadda za a ki yi masa magana kar ki je ki yi ta sakarci a waya." Kafin Raihan ta yi magana Inno ta ce, "Ummhumm yoo ban da abin Raihanu bata fara ba ni wayar, shi saurayin nata ya gaishe ni. Ni fa na haifi ubanta Zainabu ko bata gaya masa tana da kakanni ba?" Mommy ta gimtse dariya da ke cinta ta ce, "Inno ina zan sani yanzu fa ta gama ba mu labari a gabanku." Goggo ta taɓe baki tana faɗin, "Mutum dai ya gama zagaye-zagayensa mu muka haifi uwa da ubansa idan muka gama mu ce saurayin bai yi mana ba dole a fasa auren." Inno ta yi karaf ta karɓe zancen da cewar, "Wallahi faɗi da ƙarfi Zinaru, wai yarinyar nan rana ɗaya za ta watsa mana katsa a ido. Saboda Allah idan bata ba mu ya bai gaida mu ba ta ya zai ga darajarta ya san ƴar babban gida?" Goggo ta taɓe baki ta ce, "Ga ne min hanya dai."
Raiha na jin su ta shige ɗaki sai da ta zauna ta ɗauka da sallam, amsa mata ya yi sannan ya ce: "Rowa kika yi min ni kuma na gagara haƙura." Kamar tana gabansa ta zaro ido ta ce, "Ni kuma?" Ya bata amsa da, "Eh baki gaya min sunanki ba." Raihan ta yi masa murmushi sannan ta gaya masa sunanta, ta riski muryarsa na cewa: "Sunana Salim Muktar." Bata san lokaci da ta furta, "Wow Nice name." Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ya kai sunan saurayinki?" Raihan kanta tsaye ta ce, "Ni fa ba ni da saurayi." Daɗi ne ya ratsa zuciyar Salim don yadda yake ji akanta idan aka ce tana da saurayi bai san ya zai yi ba. Saboda lokaci ɗaya ya ji ta kwanta masa a rai, bai ɓata lokaci ba wurin zayyana wa Raihan abin da yake cikin ransa, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba sai dai lokaci ɗaya ta ji wata irin matsananciyar kunyarsa ta kama ta, bata iya bashi amsa ba sai katse wayar da ta yi. Duk kiran da Salim ya yi mata bata ɗauka ba sai text message da ta tura masa na amincewart, bakin Raihan ya ƙi rufuwa saboda farinciki. Haka kawai ta riski kanta cikin nishaɗi a ranar Daddy na dawowa sai da ta bashi labarin abin da ya faru, shi kansa ya ji daɗi sosai musamman da ya ga Raihan ta aminta da Salim.
Kafin wani lokaci tuni shaƙuwa da soyayya ta shiga tsakanin Raihan da Salim, Ranar da ya ce zai zo hira farinciki fal zuciyar Raihan. Kabiru na zaune ya ga shiru Raihan bata fito karatu ba har ya gama biya wa su Inno karatu suka koma, sai da Raihan ta fito Kabiru ya ce, "Fillo yau ba ɗaukan darasi." Da yake shi ma Kabiru Fillo yake kiran Raihan kamar yadda take gaya masa. Takawa ta yi har gabansa tana murmushi sannan ta ce, "Fillo yau a haƙura da karatun nan amma don Allah kar ka gaya wa Daddy." Hararar wasa Kabiru ya ce, "Hai kin san ba a aikin banza yanzu, ki ba ni cin hanci sai na yi shiru amma idan ba haka ba Daddy na zuwa an yi an gama." Da sauri Rainan ya buɗe baki tana ɗan ɓata fuska ta ce, "Wallahi Fillo ka lalace da son kuɗi, yanzu dai nawa zan baka?" Kabiru ya yi jim sannan ya ce, "Sai kin faɗi uzurinki don kowanne uzuri da yawan kuɗinsa." Raihan ta riƙe ƙugu tana yi masa fari da ido ta ce, "Saurayina ne zai zo kuma yanzu haka girki nake yi, don Allah ka rufa min asiri Fillo mu kashe mu binne." Kabiru ya sa dariya don ya gano lagonta ya ɗauke kai gefw ya ce, "A yanzu ma va zan karɓi kuɗinki ba sai Saurayin ya zo na ga kamun ludayinsa idan bai min ba, sai na zuga Daddy son raina." Raihan ta watsa masa harara tana juyawa cikin gida ta ce, "Kanka ake ji wallahi Saurayina ya fi nesa ba kusa ba." Tana gama maganar ta shige cikin gida.
Bayan sallar magriba Raihan ta gama shiryawa tsaf cikin doguwar rigar jar atamfa da mayafinta ja, ba ƙaramin kyau ta yi ba dukda ba wata kwallita ta yi ba. A ƙaramin falon su ta sauke shi sannan ta shiga kawo masa kayan ciye-ciye da shaye-shaye, Tun bai sha komai ba ya ce zai fara zuwa ya gaida su Mommy. A babban falo ya samu Mommy bayan ya same ta sun gaisa shi da Raihan suka koma ainihin falon da ta sauke shi, zuciyar Raihan fes da bata ci karo da su Inno ba don ta san da ta haɗu da su sai sun tsinkata a gaban Salima. Tana tsaka da tunani ta riski muryar Inno da Goggo sun tunkaro falon Inno ce a kan gaba tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru ai kya bari na fara shiga tun da yarinyar nan dai ni ce na haifi Ubanta, duk yanda aka yi Raihan bata gaya wa yaron nan tana da kakanni ba da bai shigo ya ƙi zuwa gaida mu ba."
A YI HKR DA ERRORS BAN YI EDITING BA.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn
26