Sashe 73
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna wuro na yin sallama da Kabiru ta wuce gida shi kuma Kabiru ya ci gana da kula da Baffajo duk da ciwon nasa sai dai a ce da sauƙin musulunci. Washegarin ranar da Kabiru ya je garin a ranar ne Allah ya yi wa Baffajo rasuwa, mutane da dama sun ji mutuwarsa musamman da jinyar Baffajo ta zama sananniya ce a cikin garinsu Kabiru, kafin wani lokaci tuni aka karaɗe cikin rugar da sanarwar mutuwar tare da cewar za a yi jana'izarsa bayan sallar Azahar. Duk da kasancewar Kabiru namiji ne amma hakan bai hana shi zubar da ƙwallah ba, kafin a yi jana'izar Baffajo ya kira Daddy ya sanar da shi a nan kuma shi ma yake jin daddaɗan labari na dawowar Raihan, Daddy ya ce masa za su shiryo washegari su zo gaisuwa. Farinciki ya yi sosai ya yi wa Allah godiya sannan suka yi sallam, kamar yadda aka shelanta ana idar da sallar Azahar aka yi wa Baffajo sallah sannan aka kai shi gidansa na gaskiya. Da yammacin ranar Kabiru ya shiga cikin gari ya siyo kayan abinci masu yawan gaske, saboda masu zaman makoki, a rumbun hatsi ya ce a riƙa shiga da kayan abincin ana buɗe wa suka ga ya yi tsalle ya fito tsidik sai ga shi a gaban Kabiru. Ras ƙirjin Kabiru ya buga ya kalli hagu da dama yana shirin yin wani yunƙuri ya ji Talatuwa na cewa, "Hai ga mari babban kifi ya fito." Da hannu ya riƙa kai wa yaran duka yama zaro harshe waje. Ganin bai kalli ƙurar Kabiru ba duk da sun haɗa ido ya harzuƙa shi, don gani yake rainin wayon Huzaifa har ya yi yawa. Afusace ya sha gaban Huzaifa ya tattakura ya ɗauke shi da mari, kafin ya an kara Kabiru ya sake ɗauke shi da wani marin jikinsa na rawa ya shaƙi wuyan Huzaifa yana faɗin, "Me ya sa ka wahalar da ƴar mutane bayan ka san ba ƙaunarta kake ba? Ka fito ka gaya mana wanene kai?" Huzaifa ya dafe kunci yana kallon Kabiru a tsorace sai kawai ya fashe da kuka. Da sauri Jume da fasa ihu tana kiran maza su zo su taimaka Kabiru yana dukan ɗan tsintuwa, kafin wani lokaci tuni wurin ya ɗinke da mutane kowa yana bawa idonsa abinci. Da ƙyar su Baffa Giɗaɗo suka kwaci Huzaifa suka rufe Kabiru da faɗa, duk yadda Kabiru ya so fahimtar da su wani abu game da Huzaifa fir suka ƙi sauraronsa. Kaiwa da kawowa ya fara yi a cikin gidan jikinsa na rawa, da sauri ya fice daga gidan ya wuce can bayan gari. Sai da ya yi nesa da jama'a sannan ya kira lambar Daddy ya sanar masa da abin da yake faruwa, wannan labari ba ƙaramin faranta ran su Daddy ya yi ba, nan take ya kira iyayen Huzaifa da jami'an tsaro ya sanar musu da abin da yake faruwa. Tun a ranar Jami'an tsaron da ke kula da shiyyar jahar Kano suka kira wasu daga cikin jami'an tsaron da ke garin Shanono, suka sanar musu duk abin da yake faruwa. Duk wani shirye-shirye game da zuwan su Daddy da iyayen Huzaifa garinsu Kabiri a ranar suka yi shi. Saboda Kabiru ya sanar musu da babu yanda bai yi don su saurare shi amma sun ƙi. A washegarin Ranar Daddy da Mahaifin Huzaifa sai yayansa suka shirya zuwa garinsu Kabiru, da yake Daddy ya san garin ba su sha wahalar kwatance ba. A headquarter hukumar ƴan sanda suka fara sauka kasancewar tare da su za su ƙarasa garin, da yake dama an san da zuwan su Daddy ba su ɓata lokaci ba suka wuce cikin rugarsu Kabiru. Tun da suka shiga yara suke bin su da kallo, tsararu daga cikinsu suna biye a bayan motar suna kurma ihu don abin mamaki da tsoro ne a wurinsu, sakamakon sun jima ba tare da sun ga motar ƴan sanda a cikin rugar ba.
Kabiru na jin dirar motocin ya fito ya yi wa su Daddy barka da zuwa, sai da Daddy ya yi masa gaisu sannan suka ƙarasa ya nemi ƴan uwan Baffajo ya yi musu gaisuwa. Har cikin gida ya shiga ya gaida Inna wuro ita ma ya yi mata gaisuwa sannan ya sa Kabiru ya buɗe booth ɗin mota ya riƙa shiga da kayan abinci. Bayan sun gama gaisuwa Baffa Sama'ila ya dubi Daddy ya ce, "Hai Alhaji da mun san wannan lamarin har da hukuma a ciki da tuni mun sallama wa Kabiru ya kawo maka yaron nan har gida." Daddy ya yi murmushi ganin yadda duk suka firgice lokaci ɗaya, ya juya ya nuna Baba sannan ya ce, "Ga mahaifin yaron nan, kuma Alhaji Sama'ila don hukuma ta shiga cikin maganar ai ba wani abu ba ne." Baffa Sama'ila ya nuna ɗakin da Huzaifa ya ke ciki a ɗaure ya ce, "Kai Kabiru shi ga ka fito da shi, su tafi da shi ko hankalinmu ya kwanta." Da sauri Kabiru ya buɗe ya fito da Huzaifa sai dai wannan lokacin bai da kuzari sai kallon mutane yake a tsorace. Baba na ganin Huzaifa ya rungume shi ya fara kuka shi kuwa ban da yaƙe baki babu abin da yake yi. Cike da mamaki Daddy ya ce, "To wai yaushe Huzaifa ya zo garin nan Kabiru?" Inna wuro na daga gefen dokin ƙofa ta ce:
"Yaron nan Huzaifa yau kusan watansa biyu cir a garin nan yara sun tafi kiwo suka dawo da shi sun tsinto shi a kogi suka ɗoro shi akan jaki ya sha ruwa ya ƙoshi don ma Allah ya sa da kwanansa a gaba, tun da ya farko yake a wannan halin don ga dukkan alamu makarai sun shafa masa kai." Inna Wuro na rufe baki Huzaifa ya zubara ya fusgo wani dokin kara da yake hannun wata yarinya, ya ɗare kai yana faɗin, "Mu je ka kaini gaban Mai shari'a." Da sauri Baba da sauran mutane suka yi kan Huzaifa suka rirriƙe shi. Ganin yananyin Huzaifa ya sa aka ɗaɗɗaure shi sannan suka ci gaba da tattaunawa. Daga ƙarshe aka damƙa Huzaifa a hannu su Daddy suka saka shi a mota, sannan suka yi sallama da su Baffa Sama'ila suka wuce tare da yarjewar jami'an tsaro. Har su Daddy suka tafi Kabiru gani yake kamar Basaja Huzaifa yake yi don shi bai yarda da ciwon haukan da yake yi ba, ya so ace an bar su da shi ya lillisa shi ko ba komai zai yi magana idan ya ji wahala. Sai da su Daddy suka ɗauki hanya sai kuma tsoro ya dira a zuciyar Daddy, zuciya ta raya masa kar suna cikin tafiya suma ya ɓace da su kamar yadda ya faru da Raihan, duk da har lokacin yana wasu-wasi game da lamarin Huzaifa da Huzaifa. Ba shiri ya kunna karatu a cikin motarsa sannan suka ci gaba da tafiya, suna shiga garin Kano kai tsaye Daddy ya bayar da shawara akan su wuce da Huzaifa Waraka Islamic Chemist, idan aka gwada aka ga ba na islamic chemist ba ne sai a yi ci gaba da na asibiti. Malam ya yi murna sosai da bayyanar Huzaifa sai da bai ji daɗin ganin halin da yake ciki ba. Tun daga jin jawabin da suka yi masa ya saki murmushi don ya fahimci wannan Huzaifa shi ne na ainihi wancen nunke su kawai ya yi ya samu ya tafi da Raihan.
Sannu a hankali raunikan da ke jikin Raiha suka riƙa warke wa tana samun sauƙi, kwananta biyu a asibitin aka sallame ta sakamakon ba wasu munanan raunuka ta samu masu yawa ba, lokacin da su Inno suka samu labarin dawowar Raihan, har da kukansu don a ranar sai da Daddy ya kai su asibitin suka ganta sannan hankalinsu ya kwanta. Tun a asibiti Raihan ta riƙa ba su labarin rayuwar da ta yi tare da Huzaifa, har zuwan su Mama Hafsa da Daddy duk sai ta gaya musu, saboda tausayi haka suka riƙa yi mata hawaye daga baya kuma wani abin ya ba su dariya.
Malam Usman dama abin da ya yi tsammani shi ne ya tabbata, lokacin da ya fara yi wa Huzaifa ruƙiyya nan take Huzaifa aljani ya fara magana cikin izza, taƙama da girman kai. "Malam Usman ka na yawon son shiga gonata da yawa, a kodayaushe ina jaddada maka wahainiyarka ta kiyayi ramata. Wai ma me ya sa ka addabi rayuwata? Me na tsare maka da za ka riƙa bibiyar sahuna?" Malam Usman ya bashi amsa, "Abin da ya kai ka jikin bayin Allah shi ne silar dalilin bibiyarka. Idan har ita Raihan birgeka ta yi har ka aure ta shi kuma wannan bawan Allahn me ya yi maka da za ka nemi salwantar da rayuwarsa." Huzaifa ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya ce, "Ba sai an yi wa Huzaifa wani abu ba yake shiga rayuwar bil'adam ba. Hasalima wannan Huzaifan babu abin da ya yi min kwangilar aikinsa kawai aka bawa Kakana Jabbul-ƙasi a yayin da nake durƙushe a wurin neman tawa buƙatar, babban abokinsa kuma amininsa na wurin aikinsu wato Abubakar shi ne ya kai wa Boka Naziru aikinsa, akan yana son a ɓatar da shi ta kowanne hali domin ya jima baya ƙaunar ganinsa a bakin aikinsu, sakamakon yana yawan samun ci gaba tun da ƙwararre kuma gogagge ne abakin aiki.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
40