← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 110

Sashe 23

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Amma ya kamata ku kwana da sanin Jabbul-ƙasi hatsabibin aljani ne hatta cikin jinsin Aljanu suna matuƙar shakkar shiga gonarsa, ya wuce tunanin mai tunani ya wuce duk inda muke tsammani. Ina tsoron a samu matsala don na tabbata muddin aka samu matsala gabaɗayanmu ba za mu kuɓuta daga hannunsa ba." Hatsabibiya ta yi maganar tana ƙarasowa wurin hannunta sarƙe da na mijinta. Abar bauta ce ta kalleta tana jinjina kai sannan ta ce, "Na san wanene Jibbul-ƙasi don haka ba zan bar wani giɓi da zai sa kwaɓarmu ta yi ruwa ba, amma dole sai mun yi iya bakin ƙoƙarinmu don kar a samu matsala. Mugaza da har lokacin take cikin matsanancin tashin hankali, ta ƙarasa gaban Abar bauta tana cewa: "Abar bauta na shafe sama da shekara ɗari uku a cikin ƙungiyar nan, na yi muku biyayya tun bansan daɗin zaman ƙungiya ba. Ban taɓa bijirewa umarninku domin ku ɗin masu biyan buƙata ne." Abar bauta ta jinjina kai tana murmushin jin daɗi da irin kambabawar da Intisar ta yi mata, Mugaza ta sake marairace murya sannan ta ci gaba da cewa, "Haƙiƙa duk duniya babu wacce na fi tsana sama da Raihan, na kawo ta ƙungiya ne domin a hallakar da ita bisa karan tsaye da ta yi a zuciyar mijina. Amma sai ga shi a lokaci ƙanƙani tana shirin yi min fintinkau cikin ƙungiyar nan, Shin abar bauta kina tunanin idan ta maye gurbin shuɗaɗɗan ruhi alaƙata da ita za ta ci gaba da rufuwa kamar a baya. Karku manta a baya na je mata a zuwan Intisar wato aminiyarta da suke karatu a University ɗaya, babu wanda bai san abotarmu da Raihan ba kuma duk na yi ne don biyan buƙatar kaina. Ina tsoron kar ta samu nasarar maye gurbin shuɗaɗɗan ruhi asirina ya tonu a wurinta domin har abada ba zan yafe mata irin baƙincikin da ta jefa ni a ciki ba koda zan rasa raina. Ta gadar mini da ɓacin ran da har yau na gagar wanke shi, ta farraƙa tsakanina da miji tare da ƴaƴana gabaɗaya. Alƙwari na ɗaukarwa kaina duk daren daɗewa sai na hallakata da kisa mai tsanani ko dan na samu damar fanshe abin da ta yi min. Amma dole zan jinkirta har sai wa'adin zamanta a ɗakin arziƙi ya zo domin zamanta a ƙungiya ni kaina babbar nasara ce." Abar bauta ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai nakasa kunnuwan mai sauraro sakamakon kasancewar duk kawunan da ke jikin abar bauta ne suke ɓaɓɓaka dariya. Abar bauta na yin shiru Gawunge da ke gefe mijin Hatsabibiya ya sa hannuwa biyu ya fisge kansa da ke haɗe da gangar jikinsa sannan ya ƙurawa Intisar idanu lokaci ɗaya ya fashe da kuka mai haɗe da dariya. Sai da ya yi mai isarsa sannan bakinsa ya fara magana da yake jikin dungulmin kan da cewar, "Aikin abar bauta baya ɓaci domin ita shakundum ce, bata aiki kara-zube don komai nata a lissafe yake. Shekarata Ɗari da ashirin ina cikin daskararriyar rayuwa, tun kafin kasancewar haka Abar bauta ta min alƙwarin dawowa cikin rayuwata ta baya, don haka ki daina wasu-wasi akan duk abin da abar bauta za ta faɗa." Mugaza har lokacin fuskarta babu walwala sai dai ta ɗan samu ƙwarin gwiwa, Abar bauta ta fara wani irin zagaye lokaci ɗaya ta yi gammo tamkar wawakekiyar rijiya nan take ƙura ta garwaye wajen, daga cikin ƙurar wani ƙasurgumin maciji ya bayyana. Da ace mutum zai yi tozali da wannan macijin zai yi tsammanin wata shirgegegiyar bishiya ce don jikin macijin tauri gare shi tamkar jikin katuwar bishiyar kuka, tsayin macijin bashi da iyaka illlah ƙaton kanta da yake nannaɗe a tsakiyarta. Da ace Macijin zai kwanta zai iya rufe ƙaton gida da abin da yake cikinsa. Baki macijiyar ta buɗe sai ga amon wuta na fitowa daga ciki, ganin haka ya sa Intisar ta yi sujjada cikin neman afuwa tana faɗin, "Tuba nake abar bauta, a gafarce ni na aikata zunubi amma wannan shi ne na farko na ƙarshe." Wasu ƙananan hallitu masu kama da jaririn jakuna suka ƙaraso wurim Mugaza suna tayata nema mata afuwa. Wani ruwa ne ya fara fita daga bakin macijiyar nan take wutar ta mutu sannan ta fara magana cikin wani irin gurnani mai firgitarwa, tana jima tana gurnanin sannan ta fara magana cikin wani irin yare mai rikitarwa.

🥵 Bari mu ɗana yarensu🥱

( Waskibatin kintasur minbaskila, haisartan kalbiskutu lakastu baksitu warkidasu baigalliasu fatafursu kininar.... Mu bar shi haka😂)

"Mun yi miki rangwame domin aikata zunubi ba aikinki bane, amma ki sani ni abar bauta na gagari kowa a duniya saboda ina iya sarrafa komai yadda nake so. Asirinki ba zai taɓa tomuwa a wurin Raihan ba, za ki ci gaba da yaudararta kuma Huzaifa dole mu katange ki da shi domin ya saka miki ido yana bin diddigin ke wacece, duk da mun sakaya ruhinki a wurinsa. Sanin kanki ne ɗakin arziki kamar gadon mulki ne duk wanda ya hau shi sai ya sauka, za mu ɗora Raihan karaga mulkine don cimma burrin ranmu, da zarar aikinta ya kammala a wurinmu za mu shafe babinta. Amma ki sani ya zama miki wajibi ki kula da kwalbar sihiri domin muddin ta sha iska tamkar ruhin Raihan ne ya ke shaƙar isar ƴanci. Duk wannan abin da take yi tana yin sa ne ba a cikin hayyacinta ba, karku manta mun yi galaba a kanta a ranar da take Chartting a banɗaki lokacin da ta zagaya bayan gida tana tsugunno tana chartting ta nan muka yi amfani da wannan damar don ganin mun gayyaci ruhinta, ba zan ja ki da nisa ba amma zan jaddada miki adana kwalbar sihiri har lokacin da buƙatarmu za ta biya.

A hankali mommy ta fara ja da baya bakinta na ci gaba da furta addu'o'in kariya, sai dai har lokacin a tsorace take. Ido ta sake zurawa Daddy lokaci ɗaya ta daina jin wannan gurnanin da yake yi mai abin tsoro, tana shirin yi masa magana daga can wajen ƙofa ta fara jin wata irin ƙara mai haɗe da kuka, ihun Raihan take ji sosai har da shassheƙa lokaci ɗaya zuciyarta ta sake tsinkewa sai dai wannan karon bata jin za ta iya zuwa, duba da irin firgicin da ta shiga. Daga kan Mudubi ta hango wayarta da sauri ta rarrafa ta janyota, cikin hanzari ta fara lalubar ɓangaren da Audio yake tana shiga ta ci karo da suratul baƙara, hannunta har rawa yake yi ta danna nan take karatun ya karaɗe cikin ɗakin. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka ta ji komai ya ɗauke mata, wata nutsuwa ta sake saukar mata. Ta yunƙura ta ƙyar ta haye gado kusa da Daddy ta kwanta a jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuwa, ta jima a kwance tana saƙa da warwara dangane da abin da ya faru da ita sai daga baya bacci ya yi gaba da ita.

WASHEGARI.
Chapter 23 · 0% Book details