← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 110

Sashe 95

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kukan da Raihan take yi har cikin zuciyar Fatima don haka ita ma ta ji duk babu daɗi ga shi bata son ta tambayeta don ta fahimci tana cikin wani irin yanayi. Nuna wa mijinta hanya ta riƙa yi har ya nufi unguwarsu Raihan, a daidai ƙofar gidansu Raihan ya yi parking ɗin motar jin haka ya tabbatarwa mata da an ƙaraso gidansu. Ɗagowa ta yi fuskarta jawur ta furta, "Na gode Fatima." Daga haka bata sake furta komai ba ta fice daga motar, kai tsaye gate ɗin gidansu ta fara bugawa tana nan tsaye ta ji motar su Fatima ta bar wurin. Daga cikin gidan ta ji ana faɗin, "Waye?" Murya na rawa Raihan ta furta, "Ni ce." Daga cikin gidan ta ji an sake cewa, "Alhaji bai daɗe da shigowa ba, ku yi haƙuri zuwa safiya." A tunaninsa irin matan da suke zuwa maula ne, saboda duhun magriba ya fara yi. Da ƙarfi Raihan ta sake buga ƙofar tana faɗin, "Ni ce Raihan ka buɗe min." Da sauri ya zare sakatar ƙofar ta tura ta shiga ba tare da ta bi ta kansa ba. Da idanu Auwalu ya bita don ba ƙaramin mamakin ganinta ya yi a wannan ɗokacin ba, tafe take ƙafa babu takalmi zani a tsangale babu kykkyawan mayafi a jiki, tana cikin tafiya hango Daddy akan baranda da alamu waya yake don ta riske shi yana faɗin, "To shi ke nan Malam haka za a yi, don lamarin yaron akwai rikitarwa. Zan kira su a waya na sa su kawo shi don a san abin yi..." Maganarsa ce ta maƙale sakamakon hango Raihan na tunkaro shi ƙafa ko takalmi babu. A hanzarce ya furta, "Zan kiraka Malam." Katse wayar ya yi da sauri ya ƙarasa wurin Raihan yana faɗin, "Raihan! Ke ce a daren nan? Daga ina kike?" A madadin ta bashi amsa sai kawai ta faɗa jikinsa ta rushe da matsanancin kuka. Jikin Daddy har rawa yake ya fara hangen bakin gate sai ya ɗago ta yana faɗin, "Wai me ya faru ina Al'amin ɗin?" Cikin matsanancin kuka Raihan ta furta, "Ya sake ni Daddy. Al'amin ya sake ni ban san me na yi masa ba." Sak Daddy ya yi yana jin maganar Raihan na zaga ƙwaƙwalwarsa, rungumota jikinsa ya yi ya ja ta cikin gida. Lokacin da suka shiga Inno da Goggo na falo a zaune suna cin Abinci Inno ta furta, "Saboda Allah me ake da sirika irin Zainabu, yarinyar nan na riƙe ta tsakani da Allah kamar yadda na ɗauki Audullahi amma kulli ta riƙa dafa mana shinkafa kayan basir, yanzu don Allah Zinaru idan ciwon suga ya samu matsuguni a jikinmu wa gari ya waya?" Goggo ta taɓe baki tana tura kwanon gabanta gefe ta ce, "Wallahi ko mutuwa na yi a gidan nan kina da kamasho saboda kullin sai na yi niyyar komawa Albasu ki ba ni haƙuri, ina dalili Audullahi yana da kuɗi daidai misali yau ko gonar masara ba zai iya siya don ya kawo a riƙa dafa mana ba? Ita kuma Abu son namiji ya rufe mata ido sai abin da yake so za ta girki mu ko oho." Inno ta wara hannuwa sannan ta ce, "Bar ta Namiji ƙarin kunama ne balle Audullahi da ya yi rayuwar turawa ina jin tsoron kar wataran ya auro mata Elizabet..." Maganar Inno ce ta maƙale ganin Daddy rungume da Raihan tana kuka, kusan tare suka tashi Goggo na salallami. Inno ta gyara ɗaurin ɗankwalinta tana cewa, "Audullahi wa nake gani da tsohon daren nan?" Zaunar da Raihan ya yi a kujera ya furta, "Raihan ce." A tsorace suka dubi Daddy, Goggo ta dafe ƙirji ta ce, "Raihan kuma a daren nan meye haka na ganta kamar korarriya. Ni wallahi ko a Albasu ban taɓa ganin ziyara irin wannan ba." Mommy ce ta ƙarasa cikin falon hannunta ɗauke da Muhammad ta cewa, "MD wallahi ka fiye rigima ka zauna a wurin su Inno amma fir ka..." Maganarta ce ta maƙake ganin su Inno carko-carko suna tsaye akan Raihan da take sharɓar kuka. Jikinta har rawa yake ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Daddyn Raihan lafiya me yake faruwa?" Daddy ya kalleta fuska babu walwala ya ce, "Je ki da ita cikin ɗaki ki taimaka mata ta yi wanka da saka kaya." Cike da damuwa Mommy ta dubi Raihan tun daga ƙasa har sama ta ce, "A ina ka tsinto ta Daddyn Raihan ko a hanyar Office ɗinka? Ya na ganta kamar ko takalmi babu kamar wata korarriya..." Daddy ya katse ta da cewar, "Ki wuce da ita ciki na ce." Hannun Raihan Mommy ta kamo suka wuce ɗaki suna shiga Mommy ta zaunar da Raihan akan gado tana tattaɓa jikinta ta furta, "Daga ina kike haka Raihan ko kaya babu a jikinki?" Raihan ta kwantar da kanta a jikin mommy tana ƙwalla ta furta, "Mommy ya sake ni." Zaro ido Mommy ta yi tana ja da baya ta furta, "Wa kenan waye ya sake ki me kika yi masa?" Kuka ne ya sake ƙwacewa Raihan ta ce, "Ban sani ba Mommy, ban san me na yi masa ba." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta ce, "Shi kenan shiga ki watsa ruwa ki same ni a falo." A hankali Raihan ta shiga toilet sannan mommy ta dawo falo ta samu su Inno ban da faɗa babu abin da suke yi, Daddy ne ya dubi su Inno ya ce, "Inno ba a yanke hukunci ta bakin mutum ɗaya, ya kamata mu tsaya mu ji ta bakin yaron nan kafin mu yanke masa hukunci ta yiwu akwai abin da ya haɗa su wanda ba mu sani ba." Mommy da ranta ya kai ƙololuwar ɓaci ta karɓe zancen da cewar, "Amma ko me ta yi masa bai kamata ya koro mana yarinya a wannan lokacin ba, ka lura da jikinta ko riga babu daga ita sai ɗaurin ƙirjin wannan wanne irin wulaƙanci ne?" Duk da zuciyar Daddy na raɗaɗi bisa abin da ya faru sai ya danne ɓacin ransa ya furta, "Duk ba wannan za mu duba, kamata ya yi mu duba mu ji ta bakin Raihan idan muka ji ta bakinta sai na nemi Malam na ji abin da yake faruwa, saboda da alama bai san abin da yake faruwa ba tun da muna tsaka da waya da shi ta shigo." Mommy bata tanka ba sai jinjina kai da take yi, su Inno kuwa ba su yi shiru ba ban da ɗebewa Al'amin albarka babu abin da suke yi ba.

Al'amin na zuwa asibiti aka karɓi Sumayya aka shiga bata kukawar da ta dace, ban da zarya babu abin da yake yi lokaci-lokaci yake kaiwa iska naushi. Lambar Mahaifiyar Sumayya ya kira nan take yake sanar musu halin da ake ciki, yana gama waya da ita babu jimawa ya kira lambar Ammi ita ma ya sanar mata. Mahaifinsa ne ya faɗo masa a rai don haka ya ji gabansa ya yi wani mummunar faɗuwa. A ɗarare ya kira Malam tana fara shiga ya ji an ɗauka, sai dai yanayin yadda ya ji muryar mahaifinsa ya tabbatar masa da bai san abin da yake faruwa ba. Har lokacin jikinsa a sanyaye yake ya sanar masa abin da yake faruwa da Sumayya da asibitin da suke, a gaggauce suka yi sallama Malam ya ce zai ƙaraso. Abin duniya goma da ashirin ne ya dagula lissafin Al'amin, wani irin fargaba da tashin hankali ya riski kansa a ciki, amma da ya tuna irin cin kashin da Raihan take yi masa sai ya ji ƙwarin gwiwa ta lulluɓe shi. Ammi ce ta fara shiryawa ta tafi asibitin tana sauka daga Adaidaita sahu mahaifiyar Sumayya da ƙannenta suka ƙaraso, fuskokinsu ɗauke da damuwa suka gaisa haɗe da jajantawa juna abin da ya faru. A harabar asibitin suka samu Al'amin da ke kai-kawo, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Ganin Ammi ya sake tsinka hanjin cikinsa, suna ƙarasowa wurinsa ya tattaro jarumta ya gaishe su. Mahaifiyar Sumayya ta dube shi sheƙeƙe tana faɗin, "Al'amin garin yaya haka ta faru ko wannan karon ma kunamar aka sake turo mata?" Sosa kai Al'amin ya yi ya ce, "Amm dama dai...dama..." Ammi ta yi masa kallon tsaf cikin tausayawa don ba ƙaramar damuwa ta gani kwance a fuskarsa ba. Waigawa ta yi ta ce, "Ina Raihan ne ko bata ƙaraso ba?" Da sauri Al'amin ya furta, "Na'am Raihan...Ehto...Dama..." Wata Nurse ta katse Al'amin da cewar, "Ina mijin Sumayya ko ƴan uwanta suke?" Da sauri Al'amin ya isa gabanta ya ce, "Gani." Juyawa ta yi ta ce, "Dr yana son ganinka yanzu." Tun bata rufe baki ba ya bi bayanta suka ƙarasa Office ɗin Dr Mu'azzam. Su Ammi na tsaye jigum-jigum da ka dubi fuskokinsu za ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa.
Chapter 95 · 0% Book details