Sashe 48
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Goggo ta karɓe zancen da cewar, "Ni dai sai na ga kamun ludayin yaron nan tukunna, saboda Allah ya sani ba zan bari Raihanu ta auro ɗan da bai fito daga gidan tarbiyya ba." Inno na bankaɗa labule ta rafka sallama har tsakiyar kan Salim, Raihan na ganin haka ta ɓata rai don ta san abin da zai hana su Inno su tsinkata a gaban Salim sai Allah. Inno na haɗa ido da Salim ta washe baki tana faɗin, "Wannan ne saurayin namu ashe?" Salim na ganin su Inno ya sauko ƙasa cikin girmamawa ya ce, "Baba Ina wuni?" Goggo da Inno suka amsa cikin haɗin baki, "Lafiya ƙalau samari ya tsofaffin?" A kunyace Salim ya amsa, "Duk suna lafiya suna agaishe ku." Inno na jin haka ta sake washe baki haɗe da zama akan kujera ta ce, "Allah sarki ashe har sun san da zamanmu? Kai wannan abu ya yi daɗi to ni dai da ka ganni ni ce na haifi Uban Raihanu, wannan kuma ita ce ta haifi uwarta Zainabu. Ka gansa nan Audullahi shi kaɗai ya rage min kamar tsoka ɗaya a miya, ita kuwa Zinaru tana da wata ƴar bayan Zainabu." Inno ta yi maganar tana nuna Goggo da tun shigowarta take ta sakin murmushi, Salim shi ma murmushi ya yi. Goggo ta kalli Salim ta ce, "Ashe shi ya sa Raihanu ta kasa tsaya wa a biya mata ayar Allah tana ta zumuɗin ganinka." Kunyar duniya ta kama Raihan da ido take yi wa su Inno sigina amma ko kallon wurin da take basu yi ba, Salim daɗi ya kama shi ya riski Inno tana faɗin: "Salmanu kake da suna ko Ɗan nan?" Raihan ta tura baki gaba kamar za ta yi kuka ta ce, "Inno sunansa Salim fa." Inno ta dubi Salim har tana leƙa fuskarsa ta ce, "Salim tashi ka hau kujera nan fa gidanku ne, ai na ɗauka Salmanu sunanka in ce sunan wani ɓarawon kaji kenan a Madaka." A kunyace Salim ya tashi ya hau kujera Goggo ta miƙe tsaye ta ce, "Yaro bari mu wuce don yanzu sai mu yi laifi a wurin Raihanu bayan tafiyarka ta zo ta riƙa yi mana faɗa ta ce mun tsinkata a gabanka." Inno ma ta miƙe tsaye suka yi wa Salim sallama har sun je bakin ƙofa Goggo ta ciro ledar goronta ta juya wurin Salim ta ce, "Yaro na ce tsofaffin suna cin goro ne? Ungo ka tafi musu da shi." Salim ya yi dariya don tsofaffin ba ƙaramin birge shi suka yi ba, lokaci ɗaya suka tuno masa da tsohuwar kakarsa da ta rasu ba da jimawa ba, fara'a ɗauke a fuskarsa ya ce. "Wallahi ba sa ci amma ni ina ci Goggo." Goggo daɗi ya kamata ta miƙa masa ta ce, "Allah ya yi maka albarka, ai kuwa duk ranar da na je albasu sai na taho maka da shi." Raihan ta yi zuru tana kallon su Goggo don tun da take da su ba su taɓa yi mata abin da ya ƙona mata rai ba irin na wannan ranar. Suna fita Salim ya kalleta da murmushi ya ce, "Baby zama da tsofaffi da daɗi amma sai ka yi haƙuri." Raihan ta ɗauke kai gefe ta ce, "To amma kawai kana zuwa sai su shigo ai sa bari ka ɗan zo da yawa." Salima ya yi dariya yana gutsurar goro ya ce, "Yanzu kenan kunya kika ji." Raihan ta ɗan zaro ido ganin ya zage yana cin goro ta ce, "Wai da gaske kana ci dama?" Kafaɗa ya ɗaga mata ya ce, "Wallahi a gurin Jadda na koya kin san ni fa goyon kaka ne." Dariya Raihan ta yi ta ce, "Ashe kaima da wuri za ka tsufa." Salim ya kwaikwayi muryarta yana faɗin, "Daɗin abin ma tare za mu tsufa kin ga tsoho mijin tsohuwa kenan." Raihan ta yi dariya don barkwancin Salim ba ƙaramim birgeta yake ba, kayan snack ɗin gabansa ya ɗauka ya fara ci haɗe da lumshe ido ya ce, "Haka kika iya girki Dear?" Kunya ta kama Raihan ta rufe ido tana dariya. Salim ya kalle ta ya sake cewa, "Wai da gaske yau saboda ni kika ƙi zuwa Islamiyya." Raihan ta rufe ido ta yi murmushi tana faɗin, "Ba fa islamiyya ba ce, Fillo ne yake koyawa min karatu a gida ni kuma yau ina aiki na ce ya bari sai gobe." Salim ya yi murmushi sannan ya ce, "To ashe ni ma za ki fara yi min ƙari kenan." Raihan ta saka dariya.
Sun jima suna hira sosai sannan Salim ya tashi ya yi wa Raihan sallama, sai da suka je harabar gidan ta gabatar masa da Kabiru har sai da suka gaisa. Salim na murmushi ya miƙa wa Kabiru hannu ya ce, "Malaminmu ina wuni?" Kabiru ya yi dariya ya ce, "Hai Samrayin Ɗaliba har ka fito." Kabiru ba karamin dariya ya basu ba, yana yi wa Kabiru sallama ta raka shi ƙofar gida a lokacin ya buɗe motarsa leda ce guda cike da alawoyi da chocolate ya miƙa mata. Da farko ƙin karɓa ta yi sai ta ga ya ɓata rai sannan ta karɓa ta yi masa godiya, tana shigowa ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Kabiru yana fito wa ta ɗaga ledar hannunta ta ce, "Ka ga irin abin kirkin da ake yi wa budurwa, ka koya don wataran idan za ka fara neman aure, na san ku fulani akwai maƙon tsiya." Kabiru ya girgiza kai ya ce, "Aradun Allah ina iya gaya wa Alhaji baki zauna karatu yau ba." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Oho dai ko ka faɗa ai yanzo ya tafi." Ta ƙarasa maganar tana wuce wa cikin gida. Raihan na shiga sashensu su Inno suka fara washe baki, Raihan tana shirin yin magana Goggo ta ce: "Zainabu yaron nan na yaba da hankalinsa, ni sai yake min kama da wani yaro a albasu." Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Mommy wai yau kin ga irin abin da Tsofaffin nan suka min? Allah saura kaɗan na sa kuka saboda takaici." Mommy ta yi dariya saboda dama ta san za a rina tun lokacin da ta ji muryar su Inno a falon da ta kai Salim, cikin yanayin zolaya ta ce: "To meye don kakanni sun gaisa da saurayin jikarsu?" Raihan ta kwanta akan cinyar mommy tana faɗin, "Wallahi ni dai daga yau kar su ƙara zuwa idan ya dawo." Raihan na rufe baki Inno ta ɗago ledar ta ce, "Wallahi da ganin yaron nan zai iya riƙe gida, dubi ku ga abin kirkin da kawo mata." Nan su Inno suka fito da alawoyi suna dubawa. Zumbur Raihan ta miƙe ta kwashi wasu daga cikin alawar ta kaiwa Kabiru sannan ta dawo cikin gida.
Soyayya sosai suke yi tsakanin Raihan da Salim babban abin da yake ƙara birgeta da Salim riƙo da addininsa don duk bayan sallar isha'i zai kirata a waya su yi bitar karatu. Kuma duk karatun da Kabiru ya biya mata sai ta sake biya wa Salim, wannan dalilin ya sa suka samu kyakkyawar fahimta a tsakaninsu. Hatta su Mommy sun yaba hankali da sanin yakamatan Salim saboda nutsuwarsa da girmama na gaba.
Salim asalinsa ɗan garin Kano ne Mahaifinsa Alhaji Muniru babban likita ne a asibitin Malam Aminu kano. Mahaifiyarsa asalinta ƴar unguwar Gwale ce, suna zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi. Salim shi ne babba a gidansu sai ƙannensa biyu duka mata Farida da Fatima, dukansu ƴan mata ne suna karatunsu a jami'ar Maitama Sule. Salim Yana da ilimin addini sosai da na boko, ya fi sha'awar kasuwanci don haka bayan ya gama karatu Mahaifinsa ya buɗe masa manyan shaguna a kasuwar kwari, shi yake safarar kaya daga ƙasashen waje yana kawowa cikin gida Nigeria. Yana da nutsuwa da tarbiyya sakamakon mahaifin bai da wasa a fannin addini, Salim ya taɓa budurwa ƴar aminiyar mahaifiyarsu, amma da ya fahimci ba me kamun kai ba ce tuni suka yi hannun riga.
Magana Raihan da Salim ta yi ƙarfi har manya sun shiga tsakani, bayan dogon bincike da Daddy ya yi akan Salim da Iyayensa Mahaifan Salim suka kawo kuɗin na gani ina so. Aka tsayar da ranar aure shekara ɗaya bayan Raihan ta kamallah karatunta, farinciki ba ƙaramin kama su Daddy ya yi ba haka suka shiga shirye-shiryen bikin Raihan. Raihan ta mayar da hankalinta sosai wurin karatu da ginin tubalin soyayyarta. Mahaifiyar Salim da ƙannensa ba ƙaramin ƙaunarta suke yi ba, takanas Salim ya ɗebo ƙannensa watarana suka kawo wa Raihan ziyara. Lokacin da za su tafi haka Raihan ta haɗa masu sha tara ta arziƙi ta basu suka tafi, sun ji daɗin ganin yadda Raihan ta karɓe su hannu bibbiyu. Lokacin da za su tafi Fatima ta dubi Raihan ta ce, "Matar Yaya don Allah zan dawo a koyana min Meatpie ɗin nan." Raihan za ta yi magana Salim ya karɓe zancen da cewar, "Princess ɗina ba kukunku ba ce, idan snacks za ku koya ku je Catering school." Fatima ta ɓata fuska tana kallon Raihan ta ce, "Kin ji fa matar Yaya." Raihan ta yi murmushi sanna ta yi wa Fatima raɗa a kunne, lokaci ɗaya Fatima ta ƙwalla ƙara ta buga tsalle ta maƙale Raihan tana cewa, "Allah ya kaimu asha biki yasin gidanku zan dawo." Raihan ta yi dariya tana kallon Salima, Salim ya naɗe hannuwa a ƙirji ya ce, "Wato wariyar launin fata za a nuna min?" Yanda ya yi magana ba ƙaramin dariya ya basu ba, lokaci ɗaya suka saka dariya. Suna zuwa harabar gidan Kabiru ya fito ya ce, "Samrayin ɗaliba har ka hito?" Salim ya miƙa masa hannu suka gaisa ya ce, "Fillo mun fito za mu wuce sai jango." Farida ta zuba wa Kabiru ido lokaci ɗaya ta ji ya matuƙar birgeta, Kabiru na shiga ɗaki da sauri Farida ta matsa kusa da Raihan cikin raɗa ta ce, "Matar Yaya don Allah wannan waye? Ma sha Allah he looks so..." Raihan ta zaro ido waje ta ce, "So..." Fatima ta katse Raihan da cewar, "Bar ƴar rainin sence Farida fa bata da saiti." Dariya suka yi Raihan ta yi musu sallama amma har suka je gida Farida na tunanin Kabiru don ba ƙaramin burgeta ya yi ba.
BAYAN WANI LOKACI.