← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 110

Sashe 62

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A cikin ƙasa da sati guda Daddy ya sa aka binciko masa wanene Barista Huzaifa asalinsa, sana'arsa, mu'amalarsa da waɗanda yake hulɗa da su. Huzaifa ɗan asalin unguwar Kurawa ne wata unguwa da ke cikin garin Kano, su biyar ne a wurin iyayensa yana da yaya Ibrahim shi ne na biyu sai ƙannensa mata guda uku biyu suna ɗakin aure ɗaya budurwa ce tana karatu a FCE Kano. Tare suka taso da Dr Hussain gidajen iyayensu na maƙotaka da juna, daga baya sai iyayen Barista suka tashi daga unguwar kurawa zuwa Fagge, sakamakon gina musu gida da yayan Mustafa ya yi. Barista Huzaifa yana da ilimin addini da na zamani daidai gwargwado, ya karanci ɓangaren shari'a a jami'ar Bayero. Ya samu aiki bai fi da shekara guda ba Mahaifiyar Dr Hussain Allah ya yi mata rasuwa. Fara aikinsa da shekara biyar ya samu canjin aiki zuwa garin Kaduna. Barista Huzaifa yana da kyawawan halaye sai dai abu ɗaya gare shi mummuna wato bin mata, wannan ya samo asali ne tun lokacin da ya fara soyayya da wata yarinaya Sakina, ya so sakina matuƙa daga ƙarshen iyayenta suka ce wani ɗan uwanta za su aura mata. A wannan lokacin ya shiga matsanciyar damuwa, ganin halin da yake ciki ya sa wani abokinsa yi masa tayin fara zuwa Club. Duk da bai taɓa zuwa ba amma ko kaɗan bai musa wa abokinsa Abubakar ba, saboda a lokacin neman duk wani abu da zai ɗebe masa kewa yake yi. Tun a ranar farko ya haɗu da Sima wata riƙaƙƙiyar karuwa, kuma dama tun da ta lura da Barista Huzaifa yawunta ya tsinke a kansa. Babban farincikinta da Abubakar ya sanar da ita sabon yankan rake ne bai saba harkar ba, haka suka jone da Sima suka ci gaba da rayuwa kamar mata da miji. Sannu a hankali Abubakar ya nuna masa ai zama wuri ɗaya tsautsayi ne don haka ya riƙa yi yana cancanza mazauni, wato ya riƙa neman mata kala-kala sun fi ɗebe kewa. A da Barista Huzaifa ya ɗauka ba zai taɓa jin daɗin mace bayan Sima ba, sai da ya tsunduma a harkar sannan ya ji ashe ita ma shafar mai ce. A haka ya ci gaba da rayuwa lokaci-lokaci yana kawo wa iyayensa ziyara, sai dai kullin cikin yi masa faɗan ya fito da mata suke yi, sai dai ya ce musu aure lokaci ne idan lokacin ya zo zai yi. Daga ƙarshe ma sai ya ke ce musu akwai yarinyar da suka daidaita karatu take yi sai ta gama za a yi maganar aure.

Bayan Daddy ya gama bincike da kansa ya samu Raihan da maganar Barista Huzaifa, bata da zaɓi don ita kanta tana sha'awar ace yau ita ce ta yi aure take zaune a gidan mijinta. Musamman da take ganin mafi yawan ƙawayensu duk sun yi aure, don haka ta dubi Daddy ta ce, "Daddy na amince Allah ya tabbatar mana da alheri." Daddy ya yi murmushi ya amsa da Amin. A ranar Daddy ya kira Dr Hussain ya ce masa ya amince ita ma daga ɓangaren Raihan ta amince, Dr Hussain godiya ya yi sannan ya ce zai sanar da Barista Huzaifa duk abin da yake faruwa da yake tuni ya koma wurin aiki. Lambar Raihan Dr Hussain ya roƙa a wurin Daddy a cewarsa zai tura wa Barista kafin ya zo, idan ya so sai su fara gaisawa. Daddy bai musa ba ya turawa Dr Hussain number Raihan, shi ma Daddy na tura masa bayan ya kira Barista ya gama sanar da shi yadda suka yi da Daddy sannan ya tura masa lambar Raihan.

Da daddare bayan sallar Isha'i Raihan na zaune da Laptop a gabanta tana binciko wasu kaya da take son yin order su, wayarta ta fara ringing. Ganin baƙuwar lamba ya sa bata ɗauka ba har sai da aka kira sau biyu. A gajarce ta ɗauki wayar ta furta, "Assalamu alaikum." Sai da ya amsa mata sannan ya ce, "Ashe dai ƴanmatan ta ɗauki nasiha ta, ta koyo sallama." Guntun tsaki Raihan ta yi don a yanayin maganar sa ta fahimci wanene shi. Bata tanka masa ba ta riski muryarsa yana cewa, "Barkanki da dare ina fatan ban takura miki ba." Raihan ta furta, "Kusan haka ne." Siririyar dariya ya yi wacce ya saba saye zuciyar ƴanmata da ita sannan ya fara yi wa Raihan bayanin abin da yake tafe da shi, amsa ta riƙa bashi daki-daki daga ƙarshe ta shaida masa ta taɓa aure da yadda yanayin auren nata ya kasance. Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama. Sannu a hankali soyayya ta fara ƙulluwa tsakanin Raihan da Barista Huzaifa, tun Raihan bata sakin jiki da shi har ta fara saki. Sai dai abin da ta lura da shi Barista Huzaifa yana da matuƙar son zolaya, gashi da barkwanci don idan suna hira yana dariya kamar ba shi ba. A haka har manya suka shiga maganar aka tsayar da ranar aure wata biyar, a lokacin kuwa saura wata biyu auren Kabiru da ƴar yayan Mahaifinsa wacce aka yi alƙawarin aurensu tun suna ƙanana. Kasancewar Barista Huzaifa a nesa yake ya sa bai cika zuwa akai-akai ba, don zuwansa biyu aka tsayar musu da ranar aure sai dai waya da chart da suke yawan yi. Su mommy ba ƙaramin farinciki suka yi ba, haka daga ɓangaren ƴan uwan Salim da suka samu labari har gida Farida ta zo ta yi wa Raihan murna. A ranar ne kuma Raihan take gaya mata maganar auren Kabiru, don a lokacin auren Kabiru saura bai fi sati biyu ba. Wannan maganar ba ƙaramin muni ta yi wa Farida ba, don haka ta wuce gida zuciyarta babu daɗi. Lokacin da za ta tafi Raihan ta haɗa mata sha tara ta azziki, har atamfa ta ɗauka daga cikin atamfofin da ta sayawa Kabiru sabida so take ta yi masa bazata ko akwati biyu ta haɗa masa, duk da ta lura ko kaɗan auren baya gabansa. Ita kanta tana damuwa da rashin walwalar Kabiru saboda a baya mutum ne mai matuƙara barkwanci, da son hira.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

34

Raihan ba ƙaramin kaya ta haɗa wa Kabiru ba kusan akwati uku don akwati biyu ta cika taf, wasu kayan masu yawa suka ragu don haka ta ɗora masa da kit. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba duk da ko kaɗan baya maraba da auren, daga ɓangaren Daddy kuɗi ya ba wa Kabiru masu tsoka a cewarsa ya sayi duk abin da yake da buƙata wajen hidimar biki. Mommy kayan abinci ta saya masu ɗan dama a lokacin da Kabiru zai tafi ta bashi don a yi hidimar biki kafin su je. Kabiru ba ƙaramin daɗi ya ji ba don dama ya san za su yi masa saboda mutane ne masu karamci da kyauta, ko kaɗan abin hannunsu bai rufe musu ido ba. Saura sati guda biki Kabiru ya tafi garinsu don Mahaifiyarsa kusan kullin sai ta kira shi a waya game da aure.
Chapter 62 · 0% Book details