← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 110

Sashe 10

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, "A'uzubillahi minasshaɗanirrajim. Ba zan ga shaiɗan da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haɗa ni da Shaiɗan la'anannan Allah?" Larai rasa hanyar da za ta ɓullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaɗaya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, "Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riƙa yi mini a tsakar ɗaki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama."

Ganin wannan lamarin yana ƙoƙarin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har ɗakin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karɓa tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya ɗauke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faɗa da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haƙura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, "Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa ɗazu ƙarya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na ƙi jini irin raini."

Inna Furai ta miƙawa Lantan hannu ta ce, "Lantan taɓa ni na ji." Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, "Billahilazi idan har wannan taɓawar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri." Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faɗa don hantar cikinta ta fara kaɗawa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa.

Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce,

"Yahanasu lafiya kuwa?" Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, "Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni." Cikinsa ne ya bada wani sautin ƙulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji ya ce, "Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?" Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, "Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buɗe idona." Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruɗu-ruɗu a jikinta. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen ƙafar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faɗa gado jikinsa na rawa ya ce, "Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a ƙasa." Yahansu na jin haka ta ƙara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su ƙare. Auwalu ne ya yi ta maza ta miƙe cikin sanɗa ya banko musu ƙofa da ƙarfi ya sa sakata.

Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana.

Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita.

Washegari.

Jama'ar gidan gabaɗaya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaɗaya labari ya watsu a ko'ina Inna Furai ta yi ido huɗu da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riƙa ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin ɗakin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu.

Ɗakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miƙe saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga ɗakin to ba za ta ƙara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miƙewa caraf Baba Sule ya damƙi hanunta yana cewa, "Ina za ki tafi ki bar ni?" Sahura ta ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce, "Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman ɗaki ba zai kai mu ba." Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, "Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba." Bugun ƙofar ne ya tsananta don haka suka taso riƙe da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buɗe ƙofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faɗo. Daga waɗanda suke tsaye a ƙofar ɗakin har su na cikin ɗakin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen ɗakin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riƙe da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, "Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?" (Uwani ƙanwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaɗaya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa ta zo ƙarshe.

Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba ƙaramin ɓata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, "Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga ɗaki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka." Baba Sule ya sake matsar ƙwalla ya ce, "Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa ƴan sama jannati ne za su tafi da ni." Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi Ɗan cikinta ma ya sanar da ita.

Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi.

Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita.

Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaÉ—aya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa'azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana.

Inna Fuarai ta karkace ta ce, "Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi." Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faɗi abin da ta sani, Yahanasu da ta buɗe ido da kyar tana sunne kai ƙasa don duk yanda hankalinta ya ɗan kwanta har Yaya Idi ya sa ta buɗe ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta ɗora da cewa, "Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a ɗakinsa to gaba shi za su ɗauka. Shi ya sa na ce tawa ta ƙare." Auwalu ya rumgumota yana cewa, "Ba za ki mutu ba Yahanasuna" Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, "Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan ɓullowa lamarin.
Chapter 10 · 0% Book details