Sashe 58
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Mommy na shiga ɗakin ta same su sun baje kaya ɗaiɗai da yake dama jakunkunansu daban mommy ta yi musu, Mommy na shiga Inno ta ɗago wani leshi da Daddy ya sawa musu ita da Goggo ta ce, "Zinaru wannan leshin a ƙasan akwati zan saka shi, idan Allah ya kaimu Allah ya sauki Zainabu lafiya ranar suna zan rangaɗa kayana." Goggo ta ware wasu kaya kala uku a gefe ta ce, "Ai ba zan ɗinka kala ɗaya ba, saboda ko a Albasu ba na fitar suna da kala ɗaya. Kai amma yarinyar nan ta shammace mu, a lokacin da muke saka rai da ciki babu sai yanzu da Allah ya nufa." Inno ta yi wani murmushin jin daɗi ta ce, "Ni kam na ɗauka Audullahi ya yi bankwana da haihuwa ashe Allah ya ɓoye ajiyarsa mu muke abin mu." Mommy ta ɗan yi gyaran murya haɗe da sallama don ta ji duk hirar da suke yi, gabanta ne ya faɗi take ayyana ashe suma kallon ciki suke yi mata ita take abinta. Su Inno suna ganin Mommy suka washe baki Inno ta ce, "Zainabu an shigo?" Mommy ta zauna a gefen gadon Goggo ta ce, "Inno yanzu tun baku huta ba kun hau kwance kaya, don Allah ku kwanta ku huta man." Goggo ta sake janyo wani ƙunshin kaya da wuƙa a gefe tana kiciniyar yankawa ta ce, "Zainabu kenan a bari ya huce shi yake kawo da rabon wani, kin taɓa ganin na bar kaya sun kwana ko Albasu na je?" Mommy ta girgiza kai haɗe da miƙe wa ta ce, "To bari na baku wuri don na gaji bacci nake ji." Inno ta ce, "Ai dama gara ki huta don gaskiya kina buƙatar hutu." Mommy ta juya ta fita tana daga bakin ƙofa Goggo ta yi ƙasa da murya ta ce, "An ya yarinyar bata ji hirar mu ba?" Inno ta waiga ta kalli ƙofa ta ce, "Da ta ji za ta yi mana magana, idan ta ji ai na ga ta kaina ina uwar miji guda ai sai ta ce na saka mata ido. Don ma Zainabu dai yarinyar kirki ce ni uwa ta ɗauke ni ba sirika ba, amma wallahi matsalata ɗaya da ita da bata son yi mana tuwo saboda Allah ina laifi a ce duk dare mu ci tuwo a gidan nan." Goggo ta wara hannuwa ta ce gane min hanya amma wallahi Audullahi ya fi ta laifi don Allah shi ba zai tsawatar mata akan abin da muke so ba?" Inno ta yi guntun tsaki ta ce, "Bar batun Audullahi baƙin Bayahude ne har gara Zainabu tana yi mana tuwo sau uku a sati amma kin taɓa jin Audullahi ya ce ta yi tuwo?" Goggo ta girgiza kai. Inno ta ci gaba da fito da kaya ta ce, "Ki bar su ƙarƙari idan muka gaji mu kama gabanmu ina dalili gida kullin ka ci shinkafa, ko kunu sai na yi sati biyu ban sha ba." Goggo ta ce, "Ba don ina jiran haihuwar Zainabu ba ai wallahi daga Iyafot (Airport) Albasu zan wuce." Mommy ban da dariya babu abin da take yi don tsofaffin ba ƙaramin dariya suka bata ba. Daga nan kai tsaye ɗakinta ta wuce don ba ƙaramin zafi idonta suke yi mata ba, tana kwanciya babu jima wa bacci ya yi awon gaba da su.
A ranar da Mommy ta sanar da shi mafarkin Raihan a ranar ya je Waraka Islamic chemist, da yake duk yaran Malam Usman sun san Daddy da irin magungunan da ake haɗa wa Raihan ya sa suka haɗa masa magunguna tare da yi masa bayanin yadda za ta yi amfani da su. Kuma tun daga ranar Raihan bata sake irin mafarkin nan ba, su Mommy sun dage sosai wurin nema mata magani kuma babu wani abu da ya sake faruwa da ita. Raihan suna yawan gaisawa da Intisar wani lokacin har video call suke yi, musamman yaran Intisar da Raihan take jin su har cikin ranta. Daddy tsaraba ta musammam ya yi wa Kabiru kasancewar ya shiga ransa sosai saboda Kabiru yana da hankali da nutsuwa. Mommy tun tana ganim kamar duk zancen ne maganar da Daddy ya yi mata na ciki har ta fara zargin kanta sakamakon irin sauye-sauyen da take samu, daga ƙarshe watarana ta shirya ta je asibiti a ranar likita ya tabbatar mata da ciki, sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata. Raihan kasuwancin da take yi ba ƙaramin karɓarta ya yi ba, ganin haka ya sa Daddy ya yi tunanin buɗe mata Boutiqe. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Raihan ba, haka ta ci gaba da rayuwarta haɗe da kasuwancinta gwanin birgewa. Sai dai a fagen samari duk yadda suka kai ga ganin sun saye zuciyar Raihan abin ya ci tura. Tun bata kula su daga ƙarshe ma suka daina zuwa gabaɗaya, da farko abin ko kaɗan bai damu Raihan ba saboda a ganinta ba za ta ƙara samun masoyi kamar Salim ba, shi kuma wanda take bege har tsawon wannan lokacin bata sake cin karo da shi ba. Don haka rashin zuwan samarin da basa yi ya fara damun Raihan har take ganin kamar rashin saurar da ba ta yi musu ne ya sa suka ja da baya. Abin da Raihan bata sani ba tuni wasu daga cikin mutane suka yanka mata ayar tambaya don tuni mutane suka ɗora zargin mutuwar Salim akan rashin lafiyar Raihan ta baya, saboda zancen duniya ko kaɗan baya ɓuya. A haka suka ci gaba da gudanar da rayuwa har cikin Mommy ya kai wata takwasa da sati biyu, a wannan lokacin aka yi wa Mommy Cs don tun a lokacin awon cikinta Likita ya ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda shekarunta sun ɗan ja, idan aka ce a bari ta haihu da kanta za ta sha wahala. An yi aiki lafiya aka ciro mata jaririnta Namiji lafiyayye gwanin birge wa, murna wurin Raihan abin ba a magana. A gaggace take tafiya don ganin ta ƙarasa wurin da ta yi parking ɗin motarta, za ta koma gida don karɓo wa Mommy ruwan shayin da su Inno suka dafa. A jikin motarsa ta same shi a tsaye da waya a hannu yana dannawa, a gaggauce ta buɗe murfin motar ta kalle shi tana faɗin, "Don Allah Malam zan ɗauki mota sauri nake yi." Bai ɗago ya kalle ta ba kuma ko kaɗan bai motsa ba balle ta saka ran zai tanka mata, haushi ne ya fara kama Raihan don a yanayin mutumin da ta gani bai yi kama da wata ɗan ƙabilar ba balle ace baya jin hausa. Haushi ya kama ta a ɗan zafafe ta ce, "Wai Malam baka jin abin da nake faɗa ne?" Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta sai dai bai tanka mata ba ya ci gaba da latsa wayarsa. Ƙugu Raihan ta riƙe ta dawo ta gabansa tana nuna shi da yatsa ta ce, "Malam ba na son wulaƙanci ka matsa min daga jikin mota." Raihan na rufe baki ya ɗago sai da ya kalleta na ƴan daƙiƙu ya ce, "Ki fara koyo sallama kafin ki furta wa ɗan'adam koda kalma ɗaya ce."
Littafin Kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624.
32