← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 110

Sashe 94

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Daga Abar bauta har Hatsabibiya rasa mai bakin magana aka yi, mamaki, tsoro haɗe da tashin hankali ya mamaye zuƙatansu. Huzaifa ya fara takawa a hankali cikin takun isa da ƙasaita har sai da ya zo wurinsu ya fara zagaye su ɗaya bayan ɗaya yana ƙyaƙyata dariya. Sai da ya zagaye su kusan sau uku sannan ya ce, "Waɗanda suka mutu kafin ku ƙaraso ina yi musu murna da farinciki domin duk waɗanda kuka ga irin wulaƙantacciyar mutuwar da suka yi rahama ce akan taku. Ni Huzaifa na tumbatsa ban ga wani Mahaluki da zai ga bayana matuƙar ina numfashi a duniya, ban da toshewar tunani da basira irin taku ta yaya za ku zo neman sa'a a kaina kuma wurin Kakana? Kun san kaf jikokin Jabbul-ƙasi babu wanda ya fi ƙauna sama da ni ta yaya zai taimaka muku ku hallaka ni? Na san kafin ku ƙaraso kun ga mace a ɗaure ban sani ba ko kun gane ta, to idan ma ba ku gane ta ba Mugaza ce. Na gano duk kaidinta da cin amanata da na yi domin dama na jima ina ɗora zargi akanta. Yau kimanin sama da watanni biyar kenan tana ɗaure babu ci babu sha kuma a duk rana ina kawo wasu kifayen aljanu suna tsotsar jininta. Ina raga mata azaba ne saboda ita ɗin uwar ƴaƴana ce ko babu komai mun haɗa zuri'a ɗaya da ita. Amma ba zan yafe irin cutarwar da ta yi matata Raihan ba, ta mayar min da ita matsafiyar ƙarfi da ya ji ta saka ta aikata kisa ba tare da tana cikin hayyacinta ba. Ta saka ta shan jini alhalin ba ɗabi'arta bace ya za a yi na yafe mata waɗannan laifuffukan?" Ilahirin jikin su Hatsabibiya ban da rawa babu abin da yake yi, baki na rawa Abar bauta ta ce, "Wallahi babu laifinmu a ciki ita ta gayyato mana ita cikin mu amma bata gaya mana..." Abar bauta ba ta gama magana ta ji an raɗa mata wani abu a tsakiyar kanta nan take ta faɗi sumammiya. Jabbul-ƙasi na zaune akan kujerar farin dutse ya kalli Huzaifa cikin jin daɗi ya furta, "Dalilai biyu ne suka sa na fi jin ƙaunarka a cikin zuciyata, dalili na farko duk cikin jikoki da ƴaƴana babu wanda ya ɗauko halaye da ɗabi'u irin nawa sai kai. Dalili na biyu ina ƙaunarka saboda taurin zuciya, taurin kai da rashin tsoronka. Tabbas kai namiji ne kuma ka cancanci ka gaji kujerata koda ba na raye, amma ka sani tsugunne bata ƙare maka ba domin zuri'ar gidan Alƙasim Bn Muhammad Mustafa na gabda tunkararka akan jinin ɗan abokinsa da ka ɗauke. A kullin ina yi maka fatan nasara sai dai wanann karon zuciyata rawa take domin Muhammad Mustafa kakan Ibrahim Alƙasim hatsababin Aljani ne fiye da tunanin mai tunani. A shekaru ɗari uku da suka wuce ya taɓa zuwa tsibirin nan har ya ci ni da yaƙi don haka nake jin ɗar a zuciyata domin sun dogara da Alƙur'ani. Na sani kaima ka sani Alƙur'ani zancen gaskiya amma saboda..." A hanzarce Huzaifa ya furta, "Dakata Jabbu. Ba na buƙatar jin yabo da ambaton kowanne addini bayan wanda na buɗi ido nake gani kuma nake wanzarwa." Jabbul-ƙasi bai damu ba don haka ya murza hannun kujerar da yake kai nan take ya koma cikin ƙarƙashin ƙasa. Inkiya Huzaifa ya yi nan take wasu tsuntsayen Aljanu suka ƙaraso suka kwasu su Hatsabibiya kai tsaye aka fara wucewa ɗakin horo da su, ana watsa su ciki kofar wurin ta shafe gabaɗaya.

A fusace Al'amin ya nunawa Raihan ƙofa ya ce, "Fice min daga gida." Idanunta ne suka ciko da ƙwallah tana shirin yin magana ya buga mata tsawa da cewar, "Fice min daga gida na ce." A tsorace Raihan ta juya za ta koma ɗaki ta ji ya fisgota yana faɗin, "Kina hauka ne baki ji me na ce ba?" Jikin Raihan na rawa ta ce, "Kaya zan saka..." Da ƙarfi ya wurga ta jikin ƙofa yana faɗin, "Baƙar munafuka kina kunyar za ki riƙa mu'amala da maza? Ki fice min daga gida na sake ki saki ɗaya, na sake ki saki biyu na sake ki saki uku babu ni babu ke ko a lahira ba na fatan haɗuwa da ke." Wani irin abu Raiha ta ji yaaaam! A tsakar kanta kalaman Al'amin suka fara yi mata amsa-amo adodon kunnenta. Bata ankara ba ta ji ya fisgi hannunta da ƙarfi bai kaita ko'ina ba sai ƙofar gida ya wurgar, da sauri ya dawo kan Sumayya da je kwance cikin jini don tun buguwar da mutumin ɗakin Raihan ya yi mata jini ya fara zuba. Da sauri ya ɗauketa ya saka a cikin mota ya fice daga gidan, Raihan na gefe a zauna ya fito a mota ya saka wa gidan key ya tayar da motar ya bar wurin. Daga ita sai ɗaurin ƙirji haka ta kunce ɗankwalin kanta ta rufe kanta da kafaɗarta ta fara takawa, tafiya take ba tare da tasan inda take jefa ƙafarta ba. Gani take tamkar a mafarki don har a lokacin da take tafiya bata gama gasgata abin da yake faruwa a duniyarta ba. Tana tafe a gefen titi mutane sai kallonta suke, wasu ma kallon mahaukaciya suke mata ya yinda wasu suke yi mata kallon mabaraciya. A bakin titi ta tsaya duk Ɗan sahun da ta tsaida sai dai ya wuce, tana nan tsaye wata mota ruwan toka ta faka a gabanta. Daga mazaunin mai zaman banza aka buɗe tana fitowa ta furta, "Matar Yaya." Kallon wurin Raihan ta yi tana ganin Fatima ta furta, "Na yi rashin masoyi Fatima, na rasa Salim na rasa masoyi na har abada. Na san Salima da yana raye ba zai min haka ba kuma ba za taɓa bari a yi min haka ba." Kallon yanayinta Fatima ta yi ta furta, "Matar yaya daga ina kike haka." Idanun Raihan suka ciko da ƙwalla ta ce, "Daga gidana nake don Allah ki kaini gida." Ba ta musa ba ta buɗe mata baya sannan ta ce, "Tare muke da Abban Salim (Mijinta) bari mu sauke ki." Raihan bata amsa mata ba ta shiga motar sai kawai ta kifa kai a cikin cinyoyi ta ta fashe da matsanancin kuka.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

48
Chapter 94 · 0% Book details