← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 110

Sashe 38

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Mommy na son ƙarasawa wurin Raihan amma tana shakkun abin da zai je ya zo, a hankali Raihan ta ɗago cikin galabaitarwa ta ce, "Mommy kaina." Hawaye ne ya ciko idon mommy a hankali ta taka gaban Raihan, tana zama Raihan ta faɗa jikinta Mommy idonta na zubda ƙwallah. Jikin Raihan zafi ya ɗauka zau ta janyo hannun mommy ta ɗora a kanta tana faɗin, "Mommy kaina ciwo." A hankali Mommy ta kama Raihan Malama Nafisa ta taimaka mata, mommy ta shiga banɗaki bakinta ɗauke da addu'a ta wankewa Raihan jiki. A kan katifa ta zaunar da ita tana kallon Malama Nafisa da kallon tuhuma, Malam Nafisa na shirin fita Malam Usman da Daddy suka shigo ɗakin, hankali a tashe Raihan da dubi Daddy ta ce, "Daddy me wannan? Wa ye ya ji maka ciwo a jikinka?" Daddy ya yi tsilli-tsilli da ido don bai san amsar da zai bawa Raihan ba. Malam Usman ya ƙarasa gaban gadon ya ce, "Malama Raihan ki kwanta ki huta kafin zuwa an jima." Raihan ƙurawa Malam Usman ido ta yi tana son gano inda ta san kammaninsa amma ta rasa takamaimai wurin da za ta shaida ta san shi, haka kawai ta ji mutumin ya kwanta mata ba za ta iya yi masa musu ba. Ba ta san ya aka yi ba amma kawai sai ta tsinci kanta cikin faɗuwar gaba, Malam Usman na niyyar fita ta ce, "Amma Abba don Allah me ya faru da Daddyna?" Daddy ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce, "Ɗan accident na samu amma babu wani ciwo da na ji." Malama Nafisa ta dubi Mommy ta ce, "Hajiya ki sauya mata kaya ki haɗa kayan buƙatarku sabida tare za mu wuce."

Daddy tare da Malam Usman suka fita harabar gidan, su Inno na jin motsinsu da sauri suka fito, Goggo ta raɓe a bayan Inno kamar mai shirin fita da gudu. Inno ganin Daddy da yanayin da yake ciki ta rafka salati tana faɗin, "Audullai yanzu haka wannan hatsabibin ya yi maka, kai wallahi ba don zai iya ji na ba tuni na faki ido na kwashe masa albarka." Daddy ya fara takowa wurin yana faɗin, "Inno ai komai ya zo da sauki." Goggo ta matsa can gefe tana nuna Daddy da ɗan yatsa tana cewa, "Audullahi ka bar matso mu, don Allah ka tsaya Malam ya wanke aljanun da suka shafe ka. Allah ya sani idan ka ƙara tunkaro mu, taku ɗaya ba zan yi ba sai a Albasu, ina dalili Aljani ya shafi fatarka ka matso wurinmu." Inno ta fututtuke cikin ɓacin rai ta waiga wurin Goggo tana faɗin, "Wallahi a yau ba sai gobe ba Zinaru sai kin tafi Albasu, haka kawai ɗana da gidansa ki riƙa saka masa ido haka kawai gidan wani ko nasa? A gidan nan babu abin da Zainabu ta mallaka idan ba Raihanu ba, yoo kayan ɗakin da kika yo mata naga dududu da Tsahare dillahi ta siya ko dubu hamsin ba su yi ba." Goggo ta gama zuwa wuya sai kawai ta nufi saitin windon Raihan ta fashe da kuka tana ƙwalawa Mommy kira, a hargitse mommy ta fita tana tambayar ba'asi. Goggo ta kalli Daddy ta ce, "Wallahi ka sakar min ƴata a yanzunan don yau duk dare a Albasu za mu kwana." Malam Usman da farko ya ɗauka wasa suke yi wa juna da sauri ya kalli Goggo yana faɗin, "Don Allah Mama ku yi haƙuri wannan ba girmanku ba ne." A zafafe Goggo ta dakatar da Malam Usman tana nuna shi da hannu tana cewa, "Dakata Malam wannan ba abin da ya shafi aljanu ba ne, ka bari idan muka zo fagen sai a neme ka, ka yi ruƙiyya yau zan nunawa wannan matar almatsutsan kaina sun fi nata. Zainabu dai nina haifi abata don haka yau ko a ƙafa sai mun tafi Albasu idan ya so duk abin da zai faru sa dai ya faru."

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 idan
kina buƙata ki min magana 0706 206 2624

20
Chapter 38 · 0% Book details