← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 110

Sashe 55

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Salman cikin yanayin tausayi ya dubi Mommy ya ce, "Dama haka rayuwa take Allah ya gafartawa Salim, na so ace yana raye da na ga wannan mai tsananin kama da ni." Raihan ta goge hawayen idonta har lokacin tana karanta hailala acikin zuciyarta, wata irin nutsuwa ce ta zo mata. Ta dubi Salman tana murmushin ƙarfin hali ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Salman da abin da ya faru, wallahi a duk lokacin da wani abu na Salim ya zo gare ni ina kasa riƙe kaina tabbas mutuwa gaskiya babu wanda zai mutu ya taɓa dawowa." Intisar ta karɓi lambar Raihan tana tambayar mommy address ɗin hotel ɗin da suka sauka. Sunan hotel ɗin mommy ta gaya mata Intisar ta ce su shiga mota su sauke su idan ya so sa je su ga hotel ɗin. Babu musu su Raihan suka shiga motar sai dai wani irin ɗaci Raihan take ji a zuciyarta. A hankali ta lumshe idonta tana jin wani iri a zuciyarta. A daidai bakin hotel ɗin Salman ya sauke su Raihan, mommy ta yi musu godiya sannan suka yi sallama Raihan ta sumbaci yaran Intisar tana jin kamar kar ta rabu da su. Su Intisar sai da suka ga shigewar su Mommy sannan suka ja mota suka yi gaba, Salman ne ya waiga wurin Intisar ya ce: "A cikin hatsabiban aljanu ma ke ta daban ce, a gidan uwar wa muka haɗu a saudiyya?" Intisar ta bushe da dariyar ƙeta sannan ta ce, "A da'irar abar bauta. ke kin ga yadda ta susuce lokaci ɗaya mahaukaciyar banza, ni na ɗauka ciwon haukan nata zai tashi ma." Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar Salim ta ce, "Ai na gaya miki ta warke garau wannan karan dama dole mu sauya salo idan ba haka ba waɗannan ƴan iskan iyayen nata su gama da mu." Intisar ta waiga wurin su Suhaima ta ce, "To garda'u har yanzu kana kan sunanka na Suhaiman ne?" Kusan lokaci ɗaya su Salma suka sake bushewa da dariya suka ce, "Wa ya ga Suhaima." Salma ta rikiɗe zuwa wani mummunan tsuntsu ta ce, "Ni fa ban so ta sauke ni daga jikinta ba don wallahi jikinta wani irin taushi na ji an ya ba zan maye gurbin Huzaifa ba." Mugaza ta saka wata irin dariya mai ɗauke da ma'anar ka kusa kai kanka halaka ta ce, "In dai Huzaifa ne ga fili ga mai doki." Daga haka suka ɓace daga titin Ba su yada zango a ko'ina ba sai a cikin tsibirin ƙungiyarsu. Abar bauta na ganinsu ta bushe da dariya saboda duk abin da yake faruwa tana ganin komai, kallon Intisar ta yi tana yage manyan bakunanta ta ce, "Kin burge ni da wannan shawarar da kika kawo matuƙa, yanzu haka na san tana nan cikin wasu-wasi kuma haka za mu ci gaba da jefa mata wasu-wasi kala-kala har sai mun mayar da ita ruwa mun cimma burinmu a kanta. Wannan karon ba za mu dogara da Huzaifa ba domin shi ma kansa yaje yi wa yaƙi, da mu da shi kowa ya yaƙi abin da yake niyyar cimma buri idan ya so kowa tashi ta fisshe shi." Lokaci ɗaya suka ɗauki soya da wani irin ihu mara daɗin sauraro saboda farincikin samun mafita.

Su Mommy na shiga ɗakin su Inno suka same su duk sun yi jigum-jigum da alamun suna cikin damuwa, mommy ta yi musu barka da hutawa kamar dai ba za ta tanka musu game da yanayinsu ba sai kuma ta ce, "Inno lafiya na ganku duk wani iri?" Inno kamar me jira ta ɗago hijabinta ta ce, "Don Allah me ye wannan Zainabu?" Mommy ta ce, "Hijabi ne Inno." Inno ta ce, "Wallahi yanzu nake shirin fita na bi jikata. Ina dalili ce mana kuka yi kanti za ku je siyayya, ya ilahi kanti da yake cikin unguwa. Tsorona Allah kar yarinyar nan Raihane ta ɓace miki a hanya na shiga uku." Raihan na daga gefe ta ja guntun tsaki ta ce, "Da yake kuma kowa irinku ne ko Inno?" Mommy ta yi mata daƙuwa, Raihan ta turo baki gaba. Goggo da ke gefe ta ce, "Ni abu ɗaya ne ya hana ni fita, ina tsoron kar na shiga cikin larabawa na ɓace don Allah Zainabu ko hasken fitilun ƙasar nan ba su isa kashe min ƙawayar ido ba?" Mommy ta yi murmushi tana cewa, "Ai shi ya sa muka ce ba za ku fita ba sai ranar da za mu tafi saboda kar a wahalar da ku." Inno ta kalli window ta ce, "Zo ki ga Zainabu ni kam waɗannan dogayen gine-ginen an ya ace laburorine suke ginawa? Kai gaskiya akwai ayar tambaya don mutanen nan da alama hatsabibai ne." Goggo ta karɓe zancen da cewar, "Zainabu ba don kar nace idona gizo yake min ba Allah da sai na ce Sha'aban mai aski mijin Safare na hango a wancan wurin a tsaye." Mommy ta riƙe baki ta ce, "Sha'aban Goggo kuma? Me kika ga yana yi?" Goggo ta washe baki ta ce, "A tsaye dai na hango shi." Raihan ta girgiza kai cike da ɗoki ta ce, "Inno yau dai na ga Intisar har da ƴaƴanta sai kuma..." Raihan ta katse maganarta da cewar, "Wallahi baki ga yaran ba gwanin sha'awa. Su Inno suka yamutsa fuska Goggo ta ce, "Wace kuma mai wannan sunan?" Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Ƙawar nan tawa fa." Ganin ba su gane ta ba ya sa Raihan ta tuno musu da Intisar nan take suka gane ta. Nan Raihan ta ci gaba da ba su labarin yadda ta ga Intisar da ƴaƴanta. Sai dai ko kaɗan bata gaya musu ta ga mai kama da Salim ba, don tun a lokacin da ta bawa Kamal haƙuri ta ci burin ba za ta sake yin zancen Salim ba saboda ta lura tana aikata abubuwa da dama cikin rashin nutsuwa. Mommy ta ji daɗi sosai ganin hankalin Raihan bai ta shi ba sai dai yanayinta kaɗai zai nuna maka tana ɗan cikin damuwa. Ko da Mommy ta ƙarasa ɗakin da suke ita da Daddy tas ta bashi labarin abin da ya faru, shi kansa ya yi mamaki matuƙa mommy ta nuna masa ba abin mamaki ba ne a cikin lamarin ubangiji tun da haka na iya kasancewa baka san mutum ba bai sanka ba ka ga yana yi maka kama da wani ko kuma kai kanka. Daga haka suka ci gaba da hirar yadda kasuwanci Raihan zai kasance da irin kayan da zai saya mata, da bayan sun koma Nigeria har zuwa yadda za ta ci gaba da sarrafa dukiyar da kanta. Raihan a ranar kusan kwana ta yi tana tunani daga ƙarshe da ta ga abin ya yi mata yawa sai kawai ta miƙe ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila raka'a biyu ta kai wa Allah kukanta akan ya yaye mata damuwar da take ciki.
Chapter 55 · 0% Book details