Sashe 99
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*79* *S*ai da layla ta d'an huta a asibiti sannan likita ya sallamesu,shehuri aka wuce da ita ana zuwa Modu yasa aka kaiwa maimartaba maimurabus jaririn dan ya ganshi ya kuma saka mai albarka. aton d'aki aka warewa layla ta shiga ta zauna 'yan barka sai zuwa suke Aisha (kiara) kuwa ta kasa ta tsare tana rik'e da jariri da kyar take iya bawa mutane su ganshi dan hatta layla bata bawa shi wani sa'in ma sai Ammi ta lek'o tace abashi nono tukunna akeyin tunanin bashi,duk sun barwa Modu yin komai shine zuwa ya d'akko kayansu daya dawo za'a ce ya manta kaza ya kuma komawa bawan Allah babu gaddama bare girman kai haka zai sake komawa yayi musu abinda suka ce ba tare daya saka wani ko wata ba. Sai dare tukunna Aliyu hydar ya koma apartment d'inshi wanda yake gari guda,a parlour'n shi ya zauna bayan ya gama duk abinda zai yi sannan ya d'auki waya ya kira matan nashi cewar suzo, kowacce ta fara murna an kira ta ba kamar Meenah da take tunanin bazai iya yin wani abun bane yasa ya kirata duk kuwa da cewar yau zai koma wajan Basmah, A k'ofar shiga parlour'n shi duk suka had'u suka tsaya kalon-kalo a tsakaninsu,Basmah ce ta daure tayi mata magana tana kakalo murmushi tace, Ina yin Amina...? Aikuwa Meenah ta yatsina fuska da kyar da kai zuciya nesa tace, "Yini lapia amma kuma kamar dare ne ko?!. Daga haka tayi saurin shigewa ciki tana faman cuno baki yana zaune yana facing kofar ya saci kallonsu sai kuma ya d'auke kai dan karma ya fara kallon wata a cikin su d'aya tace yak'i kallonta dan haka ya maze yana ci gaba da karanta news paper d'inshi,da sauri Meenah ta k'arasa jikinshi ta zauna kan kafarshi tana watsa mai wani sassanyan kallo yayi murmushi kad'an tare da ajiye jaridar yace, Ajlal karki karya ni fa yanzu kinyi nauyi da yawa. Bakinta ta kuma turowa ya kalleshi tamkar ya cijeshi amma ya maze sabida ganin Basmah ya d'an d'auke Meenah daga cinyar shi ya zaunar da ita kusa dashi ta fara zumburar baki shi dai be kulata yayi gyaran murya yana kallonsu yace, Ku shirya muje gurin Ammi layla ta haihu. Meenah ta zaro idanuwa cikin mamaki tare da ce, Nan aka dawoda ita ba gidan su aka kaita ba...?! Toh Ajlal babu kyau ne yin hakan?! Sarki Aliyu hydar ya tambaya yana kallonta cikin mamaki, tab'e baki tayi tana jijjiga kai tace, Mudai a gidan mu duk wadda tayi haihuwan farko gida ake kaita,amma ita a kawo ta nan dan Allah,uhm'um idan nice kuwa bazan yadda ba tabd'i... Dariya yayi sabida ganin har yanzu yarinta na damunta,ita kam Basmah idonta na kan tangamemiyar plasma TV d'in dake kafe a parlour'n tana jinsu amma bazakayi tunanin sauraronsu takeyi ba kasan cewar ta kafa ido tamkar tana son gano wani abun a cikin t.v d'in. Ku tashi ko wacce ta d'akko hijjab dare na sake yi. Mik'ewa Basmah tayi ta fita ita kuma Meenah ta turo baki cikin shagwab'a da tab'ara ta kalleshi, Ni dai gaskiya tsoran fita nakeyi muje ka rakani. Shareta yayi ganin lallai rigima take nema tunda tasan ba gurinta yake ba dan idan ita yayiwa haka akan Basmah ranar da rigima zasu kwana,waya ya janyo ya kira Basmah tana d'agawa yace, Please ki tahowa da Ajlal aron hijjab dan Allah. Toh. Kawai Basmah ta fad'a Meenah kuma ta sake turo baki ita a dole ba haka taso ba,sanye ta dawo cikin nata hijjab d'in hannunta rik'e da wani tazo ta mik'awa Meenah ta k'arb'a tare da cewa, Na gode Daga haka shima ya mik'e suka jera duk sun sashi a tsakiya hirar su sukewa tsakanin Meenah da shi Basmah kam ko kulawa bata yi sabida sam bata san mezata ce ba a hirar har suka k'arasa apartment d'in Ammi. Da gudu Meenah tayi ciki tana neman Ammi har cikin bedroom amma babu kowa Basmah kuwa wucewa tayi inda take jiyo magana shi kuma ya tsaya yaga iya gudun ruwan Meenah,yana nan a tsaye kuwa sai gata ta fito da alama bata ganta ba ya kalleta tare da ware mata hannuwan shi alamar ta taho tayi saurin shigewa ya matsa ta yace, Ammin bata nan ne?! Meenah ta d'aga kai alamar eh yayi murmushi yace, Toh ai kece waike 'yar gida ana zuwa kika yi gaba, ita kuma ta shiga can kuma da alama duk suna ciki tunda gashi bata fito ba ita. Ai ita kai ka gaya mata amma ni sai ka barni na tafi nasha wahala. Kai Ajlal babu ruwana ni babu wadda na nunawa inda zataje, yanzu dai kishiga kije kuga baby boy mu koma. Zare jikinta tayi daga nashi tayi gaba tana cewa, Wai kai duk ka k'agara a wani koma dan zaka je d'akin ta. Shigewa tayi shi kuma ya bita da kallo ya lura yanzu ta fiye neman rigima ta babu dalili, juyawa yayi zai koma parlour ya zauna yajiyo muryar Modu a bayan shi, Saraki sai Allah kainuwa dashen Allah wai bazaka shiga bane?! Aliyu hydar be juyo ba sai da ya k'arasa ya zauna sannan yace, Kai guy wai baka tafi gida ba me ka tsaya yi haka a nan?! K'arasawa shima Modu yayi ya zauna tare da shafa sumar kanshi ya kalli sarki Aliyu hydar yace, Bari kawai guy ina nan sai fama nake da Aisha akan tazo mu tafi amma ta kafe wai anan zata kwana su kuma su yaruwaiya sai zuga ta suke yi so ina cikin damu dan bazan iya kwana ni d'aya a gado ba na saba najini a jikin mace wallahi. Toh sai ka kwana anan kawai cikin su. Kai guy dan bani da kunya...?! Cewar Modu yana zaro ido Aliyu hydar yayi murmushi ganin ashe duk iskancin banza yake yi,tashi Modu yayi yaje ya d'akko d'an ya kawo mai, karb'a yayi yana murmushi yayi mai addu'o'i sannan ya kalli Modu yace, Guy gaskiya kasha aiki wannan yaron sak kai babu abinda ya bari sannu da k'ok'ari guy. Dariya Modu yayi sosai jin irin shak'iyancin da sarki Aliyu hydar keyi mishi, sun jima suna hira kafin Aliyu hydar yace zasu tafi Modu ya shiga yayiwa su Basmah magana suka fito shima ya k'arasa wajan Aisha (kiara) yana lallashi sai da layla tayi magana sannan ta yadda zata bishi zuciyarta cike da kewar boy d'in sannan suka tafi. Basu samu damar ganin Ammi ba kasan cewar tana wajan mijinta haka duk suka tafi da nufin da safe zasu dawo... Ranar suna yaro yaci sunan yareemah yareemah Ngari wato usman xa a dinga kiransa da NAUFAAL kowa yayi mamaki kwarai matuka don ba ai xaton sunan da Modun xe sanyawa yaron ba kenan,sosai akai shagalin taron sunan a babban katafaren dakin taron dake masarautar anci ansha ankuma rarraba savouniers abinde se wanda yagani kawai.. Hakika yareemah Ngari yakashe kudi akan takwaran nasa kayan barka ma akwatuna set biyu na loui vitton ya cika da kayan baby hade da shanu guda goma sha biyu dukde na takwaran nasa duk wata cima da akai a sunan shi yayi ya hana kowa ya bayar,kyautar bata tsaya anan ba seda yasake baiwa takwaran nasa fili a unguwar bulabulin Ngarnam dake jihar bornun.. Duk abinda meenah taci a taron sunan sedata amayar gaggawar kiran sarki Aliyu Hydar tayi awaya asukwane ya garxayo ya sunkuceta se asibitin dake masarautar gwajin farko yanuna positive meenah na d auke da ciki harna tsawon sati goma sha shida wato wata hudu kenan,murna awajen sarki Aliyu Hydar abun harbawa Meenah kunya yai se cuno baki take gaba shikuma ya xauce se sumbatun dadi yake yana sumbatar cikin.. Kiran layikan yan uwa da abokanan arziki ya shiga yi ciki hardasu Ammi ba ko kunya,Meenah ta dallah masa harara tana cuno baki gaba, Wai ya Aliyuu meye haka ne?! Cikin kissing gefen wuyanta yabata amsa yana gyara mata gashin kanta, Da nayi me Ajlaal?! Kobah kai bane kanata kiran mutane kana gaya masu.. Toh Ajlaal lefi ne dannayi?! Aidan asan nid in lafiyayyane ba ai sangartaccen sarki ba Hum uhm cewar Meenah hade da ture masa hannu don sam yanxun batason ya rabeta Bedamuba yasake nanukarta yana sinsinar wuyanta, Wifey ashe shiyasa kike avoiding dina bakyason na kusanceki ashe ashe ajiyata ce a nan yafadi hakan yana nuni da mararta.. Ni kadena tabani pls Dan murmushi Aliyu Hydar yayi wanda har seda kyakkyawar wushiryar sa ta bayyana, Toh Ajlaal xan k arta amma kinsan de baxan dena ba sede na rage ko?! Duka takai masa aciki tana dariya sun dan jima aasibitin ana gaya masu yadda xata kula da cikin ta raineshi har izuwa ranar da Allah xe sauketa lapia,daga nan sashen Ammi suka nupa duk yan gidan suna nan aka shiga masu congratulations da gudu Affy ta sakko daga stairs tana tsalle xata rungume Meenah Idanuwan Aliyu sun rufe da sauri ya dakatar da ita yana galla mata harara, Ke ke ke..Dakata hakanan se wani gudu kike Kina tsalle idan kika bigemun ita fa tunda yanxun kinsan ba ita kadai bace Allahu Akbar sannu babaa atoh Sannu baba andeji kunya wallahi agaban Ammi kake fadar haka Lalle Aliyu cewar Aunty yaruwaiya Se asannan Aliyu ya lura dab aran batamar dayai sumsum ya fice yana susar keya sukuma yan parlorn suka hau daria,yana fita ya kira Affy awaya seda ta kusa tsinkewa sannan ta dauka, Auta zo nan waje ina jiran ki Kamar baxata amsa ba sekuma tace Toh,fita wajen tai wajensa yana xaune yana danna waya tadan tsaya nesa dashi tana turo baki agaba, Zo nan lil sis kakki fushi da baa Hydar dinki mana kinji autanmu Dan murmushi Affy tai sannan takarasa wajensa taxauna akusa dashi, Me kikeso nasiya maki yanxu uhm?! Sabon apple laptop Dame kuma?! Se..uhm wannan inaso naje naga Disney castle a Florida Your wish is granted lil sis kita addua Insha Allah xankaiki Florida kije kiga Disney castle.. Rungumeshi tai tana murna,sannan yamata transfer kudi a account dinta dukdan kartai fushi saboda yasan idan tai fushi to fa kamar da Ammi yake fushin,saboda ko kad an Ammi batason fushin autar tata!!! *2 MONTH LATER* (BAYAN WATA BIYU) Abinci ne a gabanta sai dai sam ta kasa ci saboda yadda taji