← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 107

Sashe 5

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

6
Shiga yai apartment d'in baa Ngari bakinsa d'auke da sallama,babban parlor ne k'ato komi naciki samfarin royal ne harta console dake mak'ale ajikin bango,tatas ko'ina yake kamar b'angaren me lapia,kansa tsaye ya wuce hanyar d'akin yayan nasa dogarai ne gudah uku dasuka sha nad'i da d'inkin babbar riga irin na dogarai kalar masarautar wato kore da ja( green and red),matsawa gefe sukai suka bashi hanya yashiga cikin d'akin bayan sun kwashi gaisuwa.Kwance yahango yayan nasa me kula dashi yana gyara mashi kwanciya da matashin kai(pillow),kamarsu d'aya sak da Hydar,sede shi bekai hydar fad'in jiki ba dayake majinyaci ne, Amma haryaso yad'ara Hydar din a hasken fata da kuma yalwar gashin kai da tsinin hanci... Abinde sede afurta kalmar tubarkAllah...!
Alama Hydar yaiwa me kula da Ngari da hannu,shin yakoma bacci ko kokuwa idanuwansa biyu?!
"Ya farka..." Shine abinda yace da Hydar ahankali sannan ya k'araso yagaisheshi tareda ficewa daga d'akin yajanyo masu k'ofar...
Cikin sauri yareemah Aliyu Hydar yak'arasa gaban Royal bed d'in da yareemah Ngari(usman)Ke kwance,sanye yake cikin k'ananan kaya yan kanti rigar fara me layi layin blue, se blue d'in jeans dake jikinsa,hular kansa tasanyi tad'an zame kad'an yalwataccen gashin kansa yakwanta sidif kamar jariri, kaikace lafiyayyane a yadda yake..da sauri Aliyu Hydar yajanyo hular yagyara masa tareda janyo duvet yak'ara rufe masa jikinsa,duk abinda yake ,d'an uwan nasa sebinsa yake da kallo kaida kagani kasan yayi murna da ganinsa ba kad'an ba..
"Nda dubdo baa Ngari?!ya k'arfin jiki"
Tattausan murmushi yareemah Ngari yaiwa yareemah Hydar,
"Allah yak'ara maka lapia baaa Ngari Allah yakawo k'arshen wannan wahalar,Allah yasa kaffarane"
Murmushi yareemah Ngari yasake yi akaro na biyu had'e da lumshe idanuwansa biyu ahankali sannan yabud'e ,alamar Ameen Nagode..
Hawayene suka soma gangarowa daga idanuwan yareemah Aliyu Hydar da sauri yamaidasu gudun kada d'an uwan nasa yagani, ahankali yasa hannuwansa yana massaging k'afafuwan yareemah Ngari, addua yake ahankali yana tofa masa a ilahirin jikin nasa, tausayin d'an uwan nasa yasake kamashi ganin ga mutum har mutum amma ba bakin magana zeji amma baxe iya mayarwaba, sannan babu dama yamotsa jikinsa kamar me paralysis gaba d'aya jikin nasa ashanye yake, sannan baya iyaci baya sha sede ta drip ake saka masa me protein, wannan wacce irin rayuwace,meyai haka
ake cutardashi?!Sallamar doctor d'in yareemah Ngari ce ta tsaidashi daga dogon tunanin da zancen zucin dayake;
"Wa'alaika Assalamu warahmatulAllahi wabarakatuh...." Yareemah Hydar ya amsa ahankali..
Hannu Doctorn yabashi suka gaysa sannan yawuce wajen yareemah Ngari, gwaje gwajensa yai sannan yaciro drip yasaka mashi had'e da sake gyara mashi kwanciya, ganin bacci yafara d'aukan yareemah Ngari yasa yareemah Hydar fita yana jiran doctor yagama mashi allurar yafito..Doctorn yana fitowa yasake bawa yareemah Aliyu Hydar hannu suka gaysa..
"Yaushe kashigo gari?!" Doctorn yace da yareemah Hydar hka
"Jiya nazo dr mele(idris) ya issue d'in baa Ngari i hope jikin nasa yana sauk'i?!"
Nannauyar ajiyar zuciya dr mele(idris) yasawke,sannan yace.;
"Tohh abinne se a slow yareemah, but trust me Wlhy muna iya bakin k'ok'arinmu Kasan shi irin wannan ciwon bana asibiti bane kad'ai kawaide mu muna k'ok'arine tahanyar gwajin jikinsa da blood,stool nd urine test (jini,kashi da fitsari)sekuma drip da muke saka masa da magunguna damuke diluting dasuke keeping d'inshi healthy and energetic, sekuma d'an abubuwan daba'a rasaba, amma se andage sosai da addua ,akan duniya da dukiya daxa'a tafi abarsu ake neman kashe ran da Allah ya halitta... Kai Allah kashiga tsakanin nagari da mugu Ameen" Dr mele yak'arasa maganar yana jinjina kai
Iska me zafi yareemah Aliyu Hydar ya fusgar daga bakinsa,ya jima yana haka kafin yace;
"Dan Allah dr mele(idris)nasan kuna trying possible best d'inku akan baa Ngari,amma dan Allah asake kula da lapiarsa sosai, idanma yadda ake biyankune yai kad'an nixan ninka maku kud'in nayi alk'awari..."yareemah Hydar yace hakan muryarsa cikeda tausayawa
"Worry not yareemah,nidaku we are family,anxama yan uwa, sanin kankane nine family doctor d'inku for over 30years tunkafin a haifeka kenan,so badan kud'i nake muku aiki ba,nikaina ina fatan samun sauk'in yareemah usman ina Kuma tayashi da addua Allah yatashi kafad'unsa Ameen.Saboda haka kakka damu duk wani k'ok'ari munayinsa,muna kan yinsa,da yardar Allah komi ze dawo normal"
"Allah yasa dr...Allah yasa Ameen"yareemah Aliyu Hydar yace hakan yaname goge zafafan hawayen dake ambaliya a fuskarsa
"To nixan wuce yareemah, anjima kad'an dr fallomi zezo yasaka mai drip d'in dare sekuma sauran meds"
"Okay dr,Allah yasaka da alkhairi"
"Ameen ya rabbi yareemah,"
Sallama dr mele yaiwa yareemah Aliyu Hydar,ahankali yareemah yatura k'ofar d'akin yareemah Ngari hangoshi yai yana baccinsa peacefully se mekula dashi dake gefe a zaune, me kula dashi yana ganin yareemah yai sauri ze fito, ahankali yareemah yamai alamar daya xauna sannan ya kullo masu k'ofar yafito Kai tsaye yai hanyar sashen Amminsu....
Ringing wayarshi tafarayi
'Basma Oxford'sunan dayai appearing kenan a screen d'in wayar tasa,kamar baxe d'auka ba sekuma yad'aga fuskarnan a murtuke ransa inyai dubu a b'ace yake yarinyar tafara takurawa rayuwarsa gashi shikuma bayason a takura masa..
"Boo boo." Basma takirashi da haka,
"Basma..."shine kawai abin da yace
"Baby Bakada lapia ne?!"
"Da akai ya ya kuma??"yace a kafule
"your voice sounds...."bata k'arasaba yai saurin katseta ganinsu Aysa dasuke nuposhi da sauri suna k'walla mashi kira
"I'm kinda busy basma, will holla you idan ina free.."k'it yakatse wayar dede lokacin da auta affy ta mak'alk'aleshi tana tambayarsa;
"Baa Hydar ,dan Allah bani mugaysa"
"Ohh no.."yareemah Aliyu Hydar yafad'a k'asan mak'oshi,
"Abokin nawa zanbaki ku gaysa?!"
Ware ido affy tai tana rufe hancinta alamar kunya..suka hau daria k'asa k'asa itada Aysa seda sukai me isarsu sannan affy tace;
"Kai baa Hydar,ta mace ce fa,we heard her voice tundaga balcony"tace hakan cikin hausarta dabata fita dede..
Da gudu ta antaya tana fad'in;
"Barima nafad'awa Ammi"
"Affy.. Affy .. Ke affy"haka yareemah Hydar yadinga k'wallawa affy kira Amma ina tuni tashige part d'in Ammin nasu,
Bin bayanta sukai shida aysaah amma ina suna shiga affy tana k'arasa gayawa Ammin komi,se haki take tana k'arasa fad'in;
"Se yacewa ta mace cen cikin wayan nasa wai he's kinda busy wai he'll holla her idan yana free"cikeda hausarta dabata fita
Kamar bango yatsage yafad'a haka yareemah Aliyu Hydar yaji,se asannan yatuno handsfree yasaka,cikeda takaici yake jifan autar tasu da harara,tuni ta afko b'aran b'aramar datai bashiri sum sum tamik'e tai d'aki awayonce,itama aysah dake bayan yareemah Aliyu Hydar d'in bin stairs tai tahau ta arce saman,kan lefin yadawo kanta,jiki ba k'wari a kunyace yaxagayo yaxauna a k'asan kujerar da Ammi take yana susar k'eya....!

Nagode sosai ga masoyana wanda suka kirani da wanda sukaimun text message dama wanda basu samu damaba,Allah yabar zumunci naji sauk'i sosai Alhamdulillah...Allah yabarmu tare,#Nagode k'warai,Ina kuma mik'o sak'on gaisuwata ga duk masoyan littafin son rai ko zab'in iyaye
nagaisheku nagaisheku nagaisheku gaisuwa mai k'ima
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;
MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo:
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!
Chapter 5 · 0% Book details