← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 107

Sashe 91

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*75* *N*ayi dana sanin kasancewata daga cikin tsatson ki Mami domin ked in abar kyama ce cewar Yareemah Babagana dake matsar hawaye Yana magana ne yana karasawa cikin parlorn ya yinda su sarki Aliyu Hydar ke biye dashi a baya gimbiya Meenah kuwa faman mutsitstsikar idanuwa ta shiga yi don tabbatar da mafarki take... Jikin hajja Gajiram in banda rawa ba abinda yake, Tur da samun u... be k arasaba mai martaba mai murabus yai saurin dakatar dashi,, Ya isa Babagana ya isa...Mahaifiyar kace be dace ace kana gaya mata irin wa innan maganganun ba..Kayi hak uri kaji?!shi Allah... Kukan Falmata ne ya tsaidashi daga maganar da ya kewa Babagana cikin kuka face face ta k araso parlorn ta xube agaban shehu Bulama hawaye d aya na bin d aya tashiga zayyane abinda yakawota, Baba kayi mun rai,ka jik aina Baba Dubanta Shehu Bulama yai cikin taushasshiyar muryarsa irin ta iyaye nagari yace da ita, Allah shine ma mallakin rayuka Falmata,domin shid in mabuwayine gagara misali.. a kai Falmata tashiga yi.. Baba na aikata babban lefi wanda bansan da wane idanuwan xan dubi Allah ba ranar gobe kiyama Kayya Falmata kisani ce fa Allah gafururrahim ne majik an bayin sa ne a kowane yanayi.. Shiru tai na yan wasu dak ai kafin ta ce, Baba...Baba...Duk tarbiyar da ka ginata akaina na rushe ta ta hanyar.. Shiru tai tasanadiyar kukan data k ara rushe wa da shi.. Meenah da ke gefan Aliyu se duban yan parlorn take da kallo tasake shigewa jikin Aliyun hannunta cikin nasa kamar wanda xa wace shi dariya ma taso tabashi ya dake kawai cikin zuciyarsa kuwa inbanda takaici ba abinda ya lullubeshi duba da irin ha in da Gajiram da yanta suke neman sanyasu aciki.. To muna sauraron ki..Kilan ma duk cikin set up din Mami ne.. cewar Babagana daya fad i hakan cikeda takaici hade da sakin wani bahagon tsaki ji yake kamar ya shakosu itada Mamin ya rufe su da duka koya samu sassaucin abinda yakeji a zuciyarsa game da su.. Hannu Shehu Bulama ya d aga masa sannan ya juya ga Falmata da tai wuri wuri da ita, To ina sauraron ki Falmata.. Baba..Hakik a na aikata mummunan lefi wanda da farko banyi niyyar sanar da kaiba dubada irin tarbiyyar da ka d orani akanta amma nasa k afa nai fatali da hakan, Wanda ba kowa ne ya ja mun ba face Mami..Nayi nayi ta kyaleni nai aure tun shekarun baya tak i ni kuma baba na matsu matsuwar data kaini ga halaka..Baba kayi hak uri ta sanadiyar hakan harta kaini ga.. Rabuwa da mutunci na na rabu da martaba ta baba ciki harda samun ci... Cikin shege ko Falmata?! cewar Babagana hade da rafka mata uwar harara Tashi yai yana huci xe bigeta sarki Aliyu yai saurin dakatar dashi ta hanyar rik e hannunsa yana girgiza masa Kai, Kayi hak uri baa babs kaga ba ishasshiyar lapia ce da ita ba.. Bakin magana Shehu Bulama ya rasa se binsu kawai yake da kallo yarasa ta cewa gabaki d aya jikinsa ya yi masa sanyi hannunsa yasa agefan zuciyarsa ya dafe wajen saboda baraxanar fad uwa da wurin yake masa,Hajja Gajiram dake gefe a tsakure se wuri wuri take da idanuwa kamar na mujiya Meenah kuwa binsu kawai take da kallo mamaki karara kwance a akan fuskarta.. Ahankali cikin k asa da murya hannunsa dafe akan kirjinsa shehu Bulama yace, Abar wannan muhawara zuwa da safe dubada yanxun dare ne..Dare mahutar bawa yanzu ba lokacin mu bane karmu shiga hurumin ababen da mu d in ba ma gani.. a kai Babagana yai yana huci,sarki Aliyu kuwa karasawa yai kusa da shehu bulama ya temaka masa yakaishi d akinsa Falmata kuwa inbanda hawaye ba abinda take, Komawa apartment d'insu sarki Aliyu hydar yayi jikinshi duk yayi sanyi Meenah na mak'ale dashi ganin ya bi dasu ta guri mai duhu,suna shiga parlor'n Meenah ta fara zame jikinta daga nashi yayi saurin kankame ta jikinshi yana faman rintsa ido. Bedroom d'in shi yajata suka tafi suna shiga ya kulle ta hanyar sanya security ba tare da ya bari ta fahimci hakan ba ya jata zuwa bed d'in shi ya kwantar da ita tare da kwanciya a kusa da ita Meenah dake cikin blanket sai faman rarraba idanuwa take jira kawai take taji ta inda zai fara, bata gama tunani ba taji hannunshi cikin k'irjinta yana rage zafi,ita kuwa jikinta ne ya hau rawa ga uban d'in bin tambayoyin da take son yi mai na game da zuwan su apartment d'in babah da abinda taji suna ta magana amma sam ya kanainaye ta hanata tabuka komai. Meenah bata sake ko motsi ba taji yana sauke wani uban numfashi kafin ya matseta a jikinshi tamkar zai maida ita cikin shi. Murya k'asa-k'asa ya manna tattausan lips d'inshi cikin kunnanta yace, Kinyi bacci ne?! Meenah ta zaro ido tamkar yana ganinta tayi kamar bata ji ba,sake tambayar ta yayi ta kuma kudundinewa tana rintsa ido yace. Au baza ki gaya min ba toh ina jin haushi na kikeji dan banje gaba d'aya bako?! Girgiza mai kai tayi alamar a'a yayi murmushi ya sake shafarta yana kokarin juyo da ita,gani yayi idanunta gam yayi murmushi tare da zura bakin shi cikin nata yana tsotsa a hankali,ya dad'e har sai da yaja ra'ayinta itama ta fara taya shi ba tare da tasani ba har sai da ya tabbatar da itama taje limit d'in da yaje sannan ya rabu da ita ya sake cewa. Muje muyi wanka nasan kema yanzu dole kina bukatar yinshi. Da kyar ta samu damar yin magana tana rufe ido tace. Zanyi amma ni dai ba tare zamu yi. Why..!? Ya tambaya yana sake makalota zuwa jikin shi,tayi shiru dan bata san abinda zata ce mai ba kawai dai tasan baza ta iya yin wanka tare da shi ba salon iskanci kawai. Tashi yayi a hankali ta saci kallonshi har ya shiga bathroom, ya d'an jima a ciki sannan ya fito duk a tunaninta wankan yayi tayi saurin rintsa ido tamkar me bacci,ba zato bare tsammani kawai taji ya zare blanket d'in ya sureta suka nufi bathroom d'in tun tana zallewa har ta hakura sai da suka gama sannan suka fito sai turo mai baki take yi, kofa ta nufa da niyar fita tajita lock tayi saurin juyowa sai taga sam ba ita yake kallo ba har ya gama shiryawa sannan ne ya kalli inda take tare da sakar mata murmushi yana kashe mata ido d'aya. Dan Allah ka bud'e min kaya zan d'akko. K'arasawa yayi inda take jikinta d'aure da towel ya finciko shi gaba d'aya sai gashi a hannunshi ya bita da kallo, ai kuwa tayi saurin yin k'asa yayi dariya ya k'arasa tare da d'aukarta ya kaita kan bed,blanket ya janyo ya lullub'a mata sannan yakai bakin shi kan goshinta sannan yace a hankali. Sleep Meenah please. Juyawa yayi ya koma bathroom dan d'auro alwala yayin da ya bar Meenah kwance cikin d'in bin mamaki da al'ajabi ganin shifa ba damuwa zai yi ba tunda bashine zai kwanta a haka ba, da sauri ta sakko ta bud'e gurin kayanshi tana hango underwears d'in shi ta d'auki sabuwar vest fara kal ta bud'e ta sanya sannan ta hango trunk tayi saurin d'auka ta sanya sim-sim ta koma ta kwanta,tana jin shi ya fito ya tada tun tana ganinshi har bacci yayi gaba da ita hankalinta kwance. Ab'angaran su Hajja Gajiram kuwa lokacin da su Aliyu hydar suka wuce basu kulasu ba ya sanya Falmata sakin wani kukan, rarrafawa tayi kusa da yareemah babagana tana kuka harda majina ta fara k'ok'arin riko mishi kafa yayi saurin matsawa tare da zabga mata wata uwar harara murya a dashi yace mata yana nunata da yatsa. Karki sake ki tab'ani domin ba wai wani abu kikai na daban ba, nima d'in da kike gani na bawai tsira nayi daga tarkon da kika fad'a ba. Falmata kinsan 'yan mata nawa na b'ata?duk da cewar cikin su duk da yardar su ba zan iya k'irgasu ba,mutum d'aya ce a duniyar nan nayi raping d'inta kuma itace wadda sanadin hakan yasa nayi kuka da hawaye na na fad'a tarkon wutar azababbiyar kaunarta yanzu haka ta guje ni zuciyata zafi takeyi saboda rashin sanyata a idanuna da banyi ba, wallahi nayi nadamar abubuwan dana aikata a baya,tunani na ne yake gaya min cewar kud'i suna maganin komai sai gashi na kasa siyan soyayyar bilkisu dasu,ina sonta sannan nasan idan bata dawo gareni ba kaunarta itace silar barina duniya, Kakaf cikin 'ya'yanki mami babu wanda bashi da tabo,babu wanda be kona zuciyar mahaifinmu ba amma Ammi fa?duk irin abubuwan da kuke kulla mata da yake zuciyarta a tsarkake take gashi nan kullum ita da 'ya'yanta sai bunk'asa suke mu kuma daga wannan bala'in sai wancan yau ina cikin bakin cikin rayuwa Mami idanuwana sun..." Ya kasa k'arasawa saboda sark'ewa da maganar tayi yayi saurin juyawa yabar musu gurin hawaye na bin kuncin shi zuciyar shi na zafi tamkar zata tarwatse. Hajja gajiram ta fashe da kuka yayin da Falmata nta bita da kallo tana dafe da ciki wanda take jin tamkar ta luma mai wuka ko abinda ke ciki zai mutu dan bata fatan fitowar shi duniya, basu tashi daga gurin ba nan suka ci gaba da zama Hajja gajiram najin tamkar idan ta fita kowa zai san halin da aka ganta a ciki. *DAMBOA ROAD* Se juyi yareemah Ngari yake a kan gadon baccinsa idanuwansa arufe yaketa furta kalmar, Innalillahi wa inna ilahirr raji un..Ammi su Mami xasu kashe ni Ammi da wuk a xasu yanka ni.. Firgigit yatashi yana maimaita salati yayinda k ararrawar dake dauke adakin Ammi tashiga kara hakan yana nuni da something s wrong a sashen Ngari da sauri Ammi dake sallar nafila akan sallaya ta sallame dama ta idar da axama ta mike tai hanyar sashen Ngarin yaruwaiya na biye da ita abaya ko dankwali babu akanta kowannensu fuskarsa d auke da damuwa gani suke wani abun ne yasake faruwa dashi dubada irin alkaba in d aya faru daxun.. Shigar su dakin Ngarin yayi dede da mikewar Ngari daga kan gadon yana ganin Ammin ya mike ya nufe ta fuskarsa duk ruwan hawaye ne da sauri ya rungumeta tsam
Chapter 91 · 0% Book details