Sashe 20
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_*A STUNNING LOVE STORY_* _*NA_* NANA HAFSAT (_*MISS XOXO_*) HASKE WRITERS ASSOCIATION (_*Home of experts and perfects writers_*) _* Devoted to_* : cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*) _*Tukwicine agareku_* : _*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*) _*particular thanks goes to my two adorable daughters_* : _*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*... _30/31_ Wannan shafin nakine _*ASY KHALEEL_* marubuciyar _*MATAR FAYROOZA_* Allah ya k'ara basira k'anwata nanahafsat.wordpress.com ____________ Da sassafe yareemah Aliyu Hydar yatashi daga bacci se faman xagaye d'akin yake jikinsa sanye da bathrobe haka Modu indimi yatashi daga bacci yasa meshi kotakansa bebiba ya mik'e yashiga bathroom abinsa wanka yayo shima yai brush had'e da d'auro alwala mansa yashafa had'e da goga turarukansa sannan yaxura farar shaddarsa wadda tasha bak'in aiki ya murxa hularsa kotakan yareemah Aliyu Hydar dake sakin tsaki lokaci zuwa lokaci bebiba,ya ciro safarsa bak'a yana shirin sakawa yareemah Aliyu hydar yasake jan wani dogon tsakin akaro na ba adadi, takaicin ya ishi Modu murya a cunkushe yace; "Ha'a haba mana sekace tsaka tundaxu kake tsaki pls kabar kunnuwana su huta dan Allah..." Kamar jira Aliyu hydar yake Modu yai magana yadawo kusa dashi yana binsa da kallo daka kalleshi kasan yana cikin k'ololuwa a damuwa a sanyaye ya furta; "Guy... Ina cikin matsala fa,dan Allah meye solution?!" "Solution d'inme kuwa?! Solution ya wuce wanda zamu tarar a wajen baba yau idan mun koma" "Guy inaga zan samu Baffa kawai nace mishi najanye maganata" Murmushi Modu yai ahankali yace; "It's too late to cry when the head is cut,kai yanzu da wanne idon zaka kalli Baffa dahar kakeda bakin furta wata kalmar?! Plss don't even think bout it" "To... To ko kai zaka gaya mai p..."be k'arasaba Modu ya katseshi yana zare idanuwa "Ka rufamin asiri pls,yanxu ma naji da abinda kasani aciki mana" "To yaxanyi guy?I made a huge mistake" "Kawai kaide kaita addua Allah yakawo komi da sauk'i,amma Ina tsoron fushin baba,Allah de yakiyaye kawai Ameen..." "Ameen"yareemah yace a sanyaye had'e da mik'ewa yad'akko kayan daxe saka Da sauri suka gama shirinsu suka tafi sashen Aunty maijiddah suka gaisheta had'e da yimata sallama sosai tayi masu alkairi ciki harda turaruka masu dad'in k'amshi,godia sukai mata suka nupi sashen Aunty yafendo gaisheta sukai itama sukai mata sallama sosai itama tayi masu nata irin alkairin... Gurin mai martaba suka nupa acan sukaci abinci wanda kusan dukkansu su biyun cakuna suke cike da fargabar yadda xata kaya awajen baba suke,suna kammalawa Mai Alooma Ghaji ya kintsa bayan yace masu tare xasu tafi wajen Mai martaban,gallons na kindirmo da fura a fanteka fal aka bawa su Modun ga kaji da xabi kowanne da nasa d'aurin da kuma na iyayensu,manshanu ma fal aka basu ga bushasshen kifi shima an tanadeshi fal a kwalaye banda sauran kayayyakin da baxasu rubutu ba... Har parking space bataliyar yaran gidan suka rako su Mai Alooma Ghaji dasu yareemah Aliyu Hydar ciki harda meenah dake faman gatsile gatsile suna had'a ido da Aliyu Hydar ta rafka masa harara ta cikin mudubin mota tana pouting k'aramin red lips d'inta girgixa kai yareemah Aliyu Hydar yayi axuciyarsa kuwa maganarta yake yarinya sekace aljana,100k yaxaro yamik'o hannu tacikin window daniyar rabawa yaran caraf meenah ta wafce ta arce da gudu bataliyar yaran suka bita masu kuka nayi masu mita nayi dede lokacin motarsu tafuta daga gidan Aliyu Hydar ya girgiza kai ahankali yafurta; "Trouble maker......" Tafiya suke ahankli har airport bawanda kewa wani magana har suka shiga cikin jirgi suka d'aga yerwa fato motoci a tawaga sukazo d'aukarsu har shehurin.... _*MAIDUGURI_* (_*SHEHURI_*) Suna shiga cikin masarautar k'irjin yareemah Aliyu hydar ya fara bugawa fatan shi d'aya Allah yasa mai-martaba yace bazai saurare su yanzu ba sai gobe domin yanzu idan yayi mai batun zai iya shiga wani yanayin. Farin cikin Mai-martaba ya gaza b'oyuwa ganin d'an uwanshi a kusa dashi kowa ya ganshi yasan lallai yana cikin nishad'i dajin dad'i. Tun sanda suka shigo jakadiya ta zari k'afa tayi sashan hajia yakolo, tana shiga sai da gaban hajia yakolo ya d'an buga saboda tabbas tasan ganin jakadiya ba alkairi bane dan bata tab'a zuwa musu da alkhairi amma tunda su sun kasa tsaida zuciyar su guri guda dole suso jin gulmarma hakan yasa basa k'in zuwanta tunda ta gurinta suke samun duk wani makirci da suke k'ullawa. Gurfana tayi gaban hajja yakolo tana mik'a gaisuwar ban girma tare da yi mata k'irari kamar yadda akasan anayiwa duk wani jinin sarauta Saida jakadiya ta gama fadancinta sannan hajja yakolo ta kalleta tana daga kishingid'e taci kwalliya kai da ka ganta kasan Matar sarki ce, tamkar bazata yi mata magana ba sai kuma ta motsa baki da k'yar cikin isa da k'asaita tace. "Jakadiya lafiya, meke tafe dake yanzu haka?" Hajja yakolo ta fad'a tana yatsina fuska tamkar tana kallon abin k'yank'yami a jikin jakadiya, "Allah ya temakeki ki dad'e ki k'arko, dama yanzu ne naga bak'in motoci toh sai na tsaya naga ko suwaye ashe su yareemah Aliyu hydar ne da Modu indimi da kuma Mai Alooma Gaji shine nace ko dama kunsan da zuwan nasu, yanzu haka dai naga sun nufi fada baki d'ayan su." Jakadiya ta fad'a tana k'ara sunkuyar da kai tamkar zata yi mata sujjada, cikin tashin hankali hajja yakolo ta mike tsaye tana kallon jakadiya cikin tsananin rud'ani tace; "Shin kin sanarwa da hajja gajiram?"Hajja yakolo ta tambaya tana kallon jakadiya wadda kanta ke k'asa, cikin tsananin ladabi jakadiya take magana; "A'a rankishi dad'e ai yanzu suka shigo nan gurinki na fara zuwa." Jakadiya ta fad'a cikin k'ask'antar da kai a gurin hajja yakolo. "Kije kice mata ganinan zuwa." Da sauri jakadiya ta mik'e tana kuma kai gaisuwa, bata dad'e da fita ba itama hajja yakolo ta mik'e tayi side d'in hajja gajiram bayinta na biye da ita a baya har cikin katafaran parlorn da hajja gajiram ke zaune a hakimce tamkar itace sarkin. Zama tayi a kusa da ita bayan hajja gajiram ta sallami bayin dake kusa da ita suna matsa mata k'afa, suna fita hajja yakolo ta kalleta cikin yanayi na damuwa. "Yayya kinji labarin zuwan Mai Alooma Gaji?" A razane tana daga hakimce sai gata a tsaye tana kallon kishiyar ta kuma aminiyarta cikin tashin hankali tace; "Mai Alooma fa naji kina ambata to me yazo yi kuma?" "Wannan shine abun tambayar,kuma gashi duk bamu sani ba amma tunda gidan yazo dole zamu ji yanzu ina jakadiya ita ce zata yi mana wannan aikin?!"Fad'in hajja gajiram da har gumi ya fara karyo mata tamkar babu na'urar sanyaya d'aki,gajikin ta dake ta faman rawa dan tsananin fargaba tana tunanin ko zancen sarauta zasu yi ita dake burin ace yau babagana ne da sarautar. _________ *T*sananin murnar da Mai-martaba ke ciki ne yasa ya manta da komai sai ta d'an uwanshi, suna shiga fada Mai-martaba ya mike tare da kamo hannun Mai Alooma Ghaji suka fito. K'aton apartment d'insa suka nufa har sai da suka kusa shiga Mai-martaba ya juya yana kallon mutanen dake binshi a baya yayi musu umarnin da su dakata daga nan,ya kuma kallon su yareemah Aliyu hydar da Modu dake faman yin k'asa da idanuwa yace; "Modu ya kamata kuje ku huta tukunna,gobe idan Allah ya nuna mana sai muyi magana." Da sauri yareemah Aliyu hydar ya riga Modu amsawa "Toh baba mungode Allah ya nuna mana." Nan suka juya Mai Alooma yayi dariya saboda yana da saurin fahimtar yanayin da mutum yake ciki musamman idan ya zauna dashi. Apartment d'in yareemah Aliyu hydar suka wuce direct ya wuce kan soofa ya fad'a yana mai rintsa idanu kanshi na wani irin juya mai,yayin da k'irjin shi ke tsananin bugawa yana tsoran gamuwar su da Mai-martaba, gashi indai Ammin shi taji sai tafi kowa shiga b'acin rai dan haka yanzu yayi saurin mik'ewa zaune yana kallon Modu indimi dake kokarin cire socks hydar yace; "Inajin kunyar lokacin da baba zai kira mu,bari naje na cewa Baffa na hak'ura zan auri wannan yarinyar kawai, Modu idan Ammi taji cewar na watsawa baba k'asa lallai ina cikin hatsari dan denama kulani zata yi,tana son mu kyautatawa Mai-martaba domin duk cikin mu 'ya'yansa bama yi mai adalci barinje kawai" Yareemah Aliyu hydar ya fad'a duk jikin shi yayi sanyi, banza dashi Modu yayi ba tare da yayi mai magana ba sai ma k'ok'arin shiga bedroom yake mamaki ya kuma dulmiyar da yareemah Aliyu hydar. Tashi yayi yabi shi a baya cikin jin haushin yadda yayi mai banza. "Kanaji ina maka magana sai share ni kake yi?!" Kallon yareemah Aliyu hydar Modu yayi tare da yatsina fuska yana cewa; "Ohh sorry guy ashe magana kake?!" This time around kai ne ka wakilceni a surutu ka zama parrot magana ta babu gaira ba dalili kake yi,and kaje na barka kaje kace ka hak'ura da rik'eka nayi?! You're free to go yareemah ni yanzu babu inda zani tunda Mai-martaba yace mu bari sai gobe..." Kwanciya yareemah Aliyu hydar yayi a kan makeken Italian bed d'inshi tare da cusa yatsun hannunshi cikin sumar kanshi,tunani ya shiga yi dan a zahiri baya son wata Meenah shi kanshi be ga abin soba ajikin yarinyar duk da cewar tana da kyau amma bata da k'irar mata k'irjinta ma yanzu suke fitowa kosu Affy da Aysa sun fita girman na shanu, bata da shape ga tsawo kamar bulala "ohh my God!" Ya furta a fili yana furzar da iskar bakin shi....., ____________ Mai Alooma Ghaji ne zaune kan kujerun da aka kewaye gurin dasu fuskarshi cike da nishad'i ya kalli Mai-martaba; "Ina son sanin wacece yarinyar da yareemah Aliyu hydar keson ya aura?!" Yanayin Mai-martaba ne ya canza daga murmushi zuwa b'acin rai,kollon shi Mai Alooma Ghaji yayi yana nazarin shi cikin damuwa da b'acin rai Mai-martaba yake magana; "A can gurin karatun shi suka had'u yarinyar sam batada tarbiya dan har night club take zuwa da marasa kunyar yara,nasa an bincika min ita hakan yasa nace tunda beson ya kamata ba gara na bashi wacce nasan halinta nasan usulinta, naso idan ya kawo min yarinyar arziki mai cikakiyar tarbiya sai na had'a ita Aminan da yareemah babagana,toh shima sai yaje ya kwaso min kwashi kwarab dole na muka zab'a mishi mafita dani da mahaifiyar shi." Kuma gyara zama Mai Alooma Ghaji yayi yana faman girgiza kai alamar hukuncin