Sashe 24
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hutawa y ar hutu ce,doguwace sosai a iya shekarunta hancinta becika sirantaka ba bakuma xaka sanyata a layin marassa hanci ba tanada b ular hanci a dama kamar irinnasu Affy, dayake kaman gado kowacce mace a familyn tana dashi tanada manyan idanuwa tubarkAllah kamar zasu fad o don girmansu bak aramin k arawa fuskarta kyau sukaiba,bakinta d an mitsitsine me d auke da jajayen labb a (red lips) batada k iba ko kad an kamar za a busheta ta fad i haka take,daka ganta kasan tanada k arancin shekaru sosai alamun yarinta yabayyana atattare da ita......., Mai Alooma Ghaji yana fitowa daga mota,meenah ta tatafi da gudu ta rungumeshi hartana take yatsun k afar Modu da takalminta ta mak ale baffan tana murna cikeda farin cikin ganinsa tace; ama Jab ama Baffa WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: 19/12/2017, 8:31:20 PM: MISS XOXO: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_* _*A STUNNING LOVE STORY_* _*NA_* NANA HAFSAT (_*MISS XOXO_*) HASKE WRITERS ASSOCIATION (_*Home of experts and perfects writers_*) _* Devoted to_* : cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*) _*Tukwicine agareku_* : _*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*) _*particular thanks goes to my two adorable daughters_* : _*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*... _*36/37_* nanahafsat.wordpress.com _______ G*abaki d'aya ta rasa mafita,ta rasa ta ina zata kamo bakin zaran,ta k'arasa saitin da jakadiya ke zaune tayi tamkar zatayi tamole da ita zuciyarta na tafasa yatsina fuska tayi tare da cewa; Jakadiya ina son ganin hakan bata kasance ba,sanin kanki ne mun dad'e muna k arin ganin yadda za'ayi babagana ya d'are karagar mulki,amma yanzu lokaci guda ace komai ya rushe? Inason in k'ara tabbatar da wannan zancen naki,idan har da gaske ne toh dole ne shima yareemah Aliyu hydar yabi sahun d'an uwanshi Ngari, i need a prove jakadiya cinkin yan kwanakin nan dan inason samawa yareemah babagana farin ciki kije ki sake tabbatar min da mafarkinki,dan wannan zancen naki mafarki ne. Hajja gajiram ta fad'a tana wuwwulk ita idanuwa a cikin d'akin,cikin tsananin kad'uwa da shiga tashin hankali jakadiya mangu tayi k'asa da kai tare da mik'a gaisuwa da jinjina gurin hajja gajiram sannan ta mik'e tabar d'akin cike da fargabar taya zata tabbatar musu da cewar da gaske takeyi yareemah Aliyu hydar shine magajin sarki.ganin babu mafita yasa ta cigaba da bincike ta yadda zata je musu da k waran dalilin da zai sa su yadda da ita... _*YOLA(JIMETA)_* Mai Alooma Ghaji ne kwance akan 3sitter ya d'aura k afafuwan shi akan cinyar aunty Maijidda tana matsamai su a hankali yayin da aunty Yafendo ke zaune a k'asan carpet d'in dake malale a parlorn tana yanka musu fruit suna hira cikin kwanciyar hankali mata ne da suka fuskanci juna hakan yasa basu da matsala a zaman takewar su hankalin mijin su kwance dan bashi da fargaba ko wacce yana sonta babu wadda yake banbantawa hakan yasa bazaka gane wacce yafi so ba. A hankali ya bud'e idanunshi wad'anda suke a lumshe saboda yadda yakejin dad'in matsar da ake mishi.Kallon aunty Yafendo yayi tare da sakin k ayataccen murmushi yace; Albishirinki..?! Tayi dariya bayan ta d'ago sun had'a ido tana yanka tuffa tace; Goro fari kalk Mai Alooma ya gyara kwanciya bayan ya k'ara turawa aunty Maijidda k afafuwanshi shi,ya kuma gyara muryar shi cikin nishad'i yace; arki tayi kasuwa,aure za'a yi mata hope zaki bamu had'in kai sannan zaki tayamu campaign? Mai Alooma ya fad'a tare da juyawa ya kalli aunty Maijidda wadda take murmushi k asa k asa amma batayi magana ba. tab'a baki aunty yafendo tayi tana k arin d'aukar b'arin tuffa guda d'aya takai cikin bakin Mai Alooma ya d'an gutsira sannan ta zauna tana cewa; Me zai hana indai anzo an nemi soyayyar mu?,ina ganin wannan ba matsala bace adai nemi amin cewar mu. Dariya aunty Maijidda da Mai Alooma suka yi suna kallon aunty yafendo da tayi kicin-kicin ita a dole anzo neman auran 'yarta.Tashi yayi zaune yana dariya sosai dan indai yana tare dasu wani nishad'i yake ji,cikin jin dad'i yace; Toh shikenan amma fa ba ita kad'ai zai aura ba su biyu ne at once. Yayi maganar cikin tabbatarwa. Ba aunty yafendo ba hatta aunty Maijidda sai da zuciyarta ta harba dan tsananin kad'uwa dajin maganar,sai dai ita aunty Maijiddah tayi kawaicin yin shiru tunda d iyar tace batare da tayi magana ba sai aunty yafendo ce tayi ta hanyar cewa; "Ah haba dai! Wannan zancen kawai tatsuniyace amma ya za'a ce abawa mutum ya auri mata biyu tashin farko ba tare da anyi mai d'aya anga yadda zaman zai kasan ce ba,gaskiya bazai yuwuba sai dai ya hak ura da Meenah dan ita bazata iya zama da kishiya ba tashin farko. Aunty yafendo tayi maganar cikin had'e rai fuskarta ta canja daga farin ciki zuwa damuwa kallon shi ya maida kan aunty Maijidda ya gani ko zata ce wani abun sai yaga kamar ma batajin abinda suke cewa hakan yasa shi sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya kalli aunty yafendo yana cewa; Mai martaba shine yake son had'a jinina da nashi su kara had'uwa ta hanyar bawa yareemah Aliyu hydar Meenah,idan baku sani ba ya kamata yanzu kuji sannan ku sani yareemah Aliyu hydar yana da *SON RAN* shi ni kuma bazan bari a zalince shiba hakan yasa nace to sai dai a had'a mai biyu saboda Meenah *ZAB'IN IYAYE* ce kunga anan babu wanda zai ce anyi mishi ba dai-dai ba.ya Kama ta ku k'ara k arfafa min gwiwa wajan ganin mun k'ara k ulla kanmu nida d'an uwana,kamar yadda Ameenatu take 'yata shima Aliyu hydar d'anane kuma duk ina son su ina alfahari dasu, ku bani goyan baya sannan itama Meenah anjima zan sanar mata ina fatan zaku taya su da addu'a?! Ya fad'a yana kallon su da k yar aunty Maijidda ta tsaida zuciyar ta guri d'aya sannan tace; Insha Allahu Allah yasa hakan ya zamar musu mafi alkairi a rayuwa. "Amin..!" Mai Alooma ya fad'a sannan ya maida kai wajan aunty yafendo gani yayi tayi shiru alamar bata da niyar yin magana,ya kalli gefen shi tare da bubbuga kusa dashi yace mata; Kema dawo nan,ki gaya min abinda kike tsoro har yasa kika k'i bamu goyan baya taho ki zauna. Da k yar aunty yafendo ta mik'e ta koma inda yake nuna mata,sai da ta zauna sannan yayi murmushi har hak oran sa suka bayyana yana kallonta yake cewa; Yafendo amarya,yafendo tawa ta kaina,amarya bakya laifi koda kin kashe Meenah. Da sauri ta kalleshi tana zaro idanuwa yayin da aunty Maijidda ta tuntsire da dariya tamkar ba itace ke cikin damuwa ba. Mai Alooma ya juya yana kallonta har da 'yar hararar wasa sannan ya kalli aunty Yafendo wadda ta saki baki tana firfito da ido jin yace koda ta kashe Meenah. Sanar dani kinji Maman Meenah. Mai Alooma ya fad'a cikin sanyin murya. Ina tsoran karya wulak anta min yarinya sanin kanka ne Meenah yanzu take sanin menene rayuwa,sannan yanzu ne take karatu na tabbatar wadda yareemah Aliyu hydar yake so tafi Meenah girma, ilimi,wayewa,wayo da dabara, Meenah ba abinda ta sani na rayuwa bare aje ga batun rayuwar aure,kawai tana jin shine amma bata san ya yake ba bare tasan muhimmancin shi.Meenah rawar kai,fitsara,rashin kunya ni ba abinda yake bani takaici irin rashin tsoronta kwata-kwata banga abinda take tsoro ba. Aunty yafendo ta fad'a tare da tallafo hab'arta ta rik'e. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cire mata tagumin da tayi yace; Karki damu da wannan, koda anyi bikin baza ta tare gidan shiba sai ta kammaka karatunta na secondary school a gurin Ammin shi kinga lokacin ta k'ara hankali kuma rawar kannan ina saka ran zata denashi so worry not kinji?! Cikin jimami aunty yafendo tace; Allah yasa alkairi ne zamu ci gaba da yi musu addu'a insha Allahu. Amin nagode muku ina alfahari daku a cikin rayuwata,nasan ko bayan raina bazaku tab'a watsan k'asa a ido ba. Murmushi suka yi dukkan su kafin suci gaba da hirar duniya cikin so da shak uwa..., *Z*aune suke a wani waje da aka ware cikin gidan mai masifar kyau gurine da za'a iya kiranshi da love garden saboda yadda aka k awata shi harda zanan heart a k'asan grass carpet d'in dake gurin.Modu ne da yareemah Aliyu hydar kishingid'e cikin wasu lafiyayyun kujeru da aka kewaye gurin dasu ko wanne manne da waya a kunnen shi kai da ka gani kasan hirar soyayya suke. Meenah ce ta doso wajan kasan cewar taje neman Modu har apartment d'insu ta tarar baya nan tazo wucewa ne suka had'u da Bulama take tambayar shi ko yaga su Yaya Modu yace mata suna garden shine ta tafi harda wak ar ta. "Yaya Modu..!" Meenah ta kwad'a mai kira cikin kunnan shi kasan cewar idanuwan shi rufe suke bega zuwanta ba sai kiran da tayi mai wanda ya kusan kashe mai dodan kunnen shi.da sauri ya mik'e yana murza cikin kunnan shi ita kuma sai dariya take mai hakan yaja hankalin yareemah Aliyu hydar ya zare wayar a kunnen shi bayan ya yanke kiran. Meenah meye hakan eh?! Yaya dawa kake waya hakan sai wani murmushi kake kana girgiza k afa?! Hararar ta Modu yayi tare da cewa; idan kinzo muna tare ba gurina zaki fara zuwa ba sai kinje kin gaida shi sannan ni kina jina?! Yatsina fuska tayi tana mai wani irin kallo mai cike da ma'anuni da yawa sannan ta d'anyi tsaki kad'an ta zauna gefen shi tana cewa; Ni wallahi kai zan kula ai kaine kawai kake kulani shi wannan baya magana wallahi bana son marar yiwa mutane dariya. Meenah yayan kine fa dole ki dinga gaida shi. "Tabdijan..!" Meenah ta fad'a tana hararar side d'in yareemah Aliyu Hydar wanda shima ya had'e fuska dan karta kawo mai raini. Modu yayi mai signal da girarshi alamun ya saki ranshi sai ya k'ara had'e fusa tare da mik'ewa tsaye yabar musu gurin.Meenah ta bishi da kallo tare da kallon Modu indimi tace; Yana da kyau amma baya dariya dan Allah kace ya dinga yi zai fi k'ara kyau." Mik'ewa Modu yayi tare da fad'in; zo muje ki gaya mai ni baya jin magana ta. Idanuwa Meenah ta zaro tare da dafe talin gashin kanta tana rintsa