Sashe 15
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
nanahafsat.wordpress.com
21
This page is urs FADEELA LAMIDO,writer of bugun zuciya
.......
Bornu(Maiduguri)
Shehuri(masarautar sarkin Bornu)
Kodah mai martaba yakoma haka yawuni sukuku ba walwala atattare dashi,duk wani k'ara da y'an k'orafe k'orafe da aka kawo masa waziri yad'ora akai yace yayi,daga k'arshe ma ya tattarra yakoma sashensa saboda bayasan a takura masa wunin ranar shehurin de duk gatanan gatananne ba dad'i narashin walwalar sarki,kodah yareemah Aliyu Hydar yaje gaisheshi ma bawani sakar masa fuska yaiba shikansa yareeman jikinsa yayi sanyi rashin ganin fara'ar mahaifin nasa saboda be tab'a ganinsa ahaka ba,sukansu gajiram da yakolo sunsha jinin jikinsu ganin sarkin ahaka saboda a'iya shekarun mulkinsa baxaka tab'a kawo rana d'aya ace fuskar sarki ta canxa ba, saboda shi mutum ne adali me sanin yakamata kuma faran_faran dashi kullum fuskarsa cikin annuri take da dattako kamar ba sarki ba bashida girman kai ko d'aure fuska sam bahaka yake ba shiysa har award aka bashi a London na sarkin dayafi kowa a nahiyar Afrika,yadda Mai martaba yaga rana haka yaga dare idanuwansa basu runtsa ba,dayayi juyi akan gadon alfarmasa ba abinda yake tunanowa se maganganun da modu yagayamasa akan Basma,daga k'arshe ma mik'ewa yai yashiga band'aki yayo alwala yafara sallar nafilfili...
WASHEGARI;
Da sassafe mai martaba yashrya ko takan fada bebiba,balle yatsya cin abinci,sarkin tuk'ine yajashi se damboa road gidan hajjagana mahaifiyar yareemah Aliyu Hydar suna zuwa aka bud'e masa gate b'angaren yareemah Ngari yafara shiga bacci yake amma Alhamdulillah yad'an fara murmurewa bakamar daba ficewa yai daga b'angaren bayan yawa Ngarin adduar samun lapia,sashen hajjagana ya nupa bayan jakadiyarta tayi hanxarin fad'a mata gafa mai martaba nan,yana danna kai cikin parlorn k'amshin turaren wutar ambar yadaki hancinsa lumshe idanuwa yai har cikin zuciyarsa yaji dad'in k'amshin bakuma yau yasaba jin gidan hajjaganar cikin wannan k'amshin ba nantake wani yanki na b'acin ransa ya ragu,cikin hanxari ma'aikatan gidan sukahau gaisheshi d'aya bayan d'aya,lokacin Affy da Aysa sunata shararar baccinsu saboda safiya ce ainun danko takwas batayiba...
Zaune Ammin take akan dinning table tana jera abinci sanye take cikin laffaya multi color se tashin k'amshin khumra take,lokaci d'aya tajiyo suka had'a ido murmushi tasakarwa uban y'ay'an nata had'e da xuwa ta tarbeshi cikin girmamawa tagaisheshi bayan sungaysa ne Ammin takawo masa warmers cikeda varieties na abinci da flask na shayi da finjal(cup d'in tea)gaban shi ahankali tashiga serving d'inshi da dadd'adan abincinta kakkauran tea tahad'a masa dayasha kayan k'amshi gefe d'aya kuma funkaso ne da miyan yakuwa da yaji naman kasuwa d'ayan plate d'in kuma soyayyar doyace da k'wai se sauce na hanta d'ayan plate d'inkuma farfesun kaji ne da snacks hannu Ammin tawanko tashiga bawa mai martaba abincin abakinsa bashiri yabud'e baki tashiga zura masa abincin se lumshe idanuwa yake jin dad'in abincin tatass mai martaba ya lode abincin nan se snacks kad'an daya rage,sosai Ammin talura mai martaban nacikin damuwa dukkoda wai ahakanma taragu hira tashiga bashi harde tasamu yarage damuwar sosai har yake bata labarin taron da sukai a Abuja da sauran sarakuna... Bayan nanne kuma yagyara xama yafad'awa Ammin komi na binciken dayai akan Basma amma bece mata Modu indimi ne yai binciken ba,k'warai matuka Ammi ta gamsu da hukuncin da Mai martaba yayanke takuma ji dad'in yadda Mai martaban yad'au abin da muhimmanci harshi dakansa yasa agudanar da bincike,ya k'ark'are mata zancen da ko Aliyun bai nunawa yadda binciken yakasance ba seyanzu.. Cikeda k'arfafa masa gwiwa Ammin tace;
"Hakan yayi gaskia kuma aiba se yadda yakeso xa'ayiba duk hukuncin daka xartar shine daidai"
Nannauyar ajiyar zuciya Mai martaba yasauke a hankali yace;
"Kinsan hukuncin dana yanke yanzu a xuciyata?!"
"A'a"cewar Ammin a tak'aice..
"Ni ina ganin kawai zan had'a auren Aliyu da y'ar gidan kawu Alooma dake yola ko yaya kika gani?!"
Murmushi fad'ade a fuskar Ammi tace;
"Wannan hukunci yayi bak'aramin dad'i najiba kuwa ubangiji Allah yasa matarsa ce"
"Kina ganin babu matsala ko?"cewar mai martaba
"A'a ko d'aya wallahi hakan yayi daidai tuwona maina kenan aiba son ransa xa'a biba duk zab'in daka zartar shi za'abi saboda sab'in iyaye ai shine mafificin alkhairi"
Murmushi mai martaba yai cikeda jin dad'in kalamanta yace;
"Kira shi sakaran yazo yanxu ba se anjima ba"
"Toh"Ammin tace had'e da mik'ewa tai hanxarin d'akko wayarta tashiga dialing number yareemah Aliyu Hydar....
Team#SRKZI?!lovers
Kai Kai Kai Nagode mentor da wannan gundumemiyar kyauta da kikaimin na sadaukar da littafinki me d'imbin fad'akarwa agareni
I love and adore you
you are just a perfect person your heart is huge and you care so deeply for everyone you let into your life with such gentle kindness. I am in love with absolutely everything you are and do. You are a gift of person that I am lucky enough to call my own
Allah yabarmu tare har abadah
Allah ya k'ara maki basira acigaba da suburbud'o mana;
ALWASHI(LABARIN HAFSAT)
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo:
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of expert and perfect writers)