← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 107

Sashe 89

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tare da an temaka mishi ba.hannu ta zura ta ciro kullin abinda boka ya basu ta kalleshi sannan ta cije lips tare da sakin wani kayataccen murmushi ta fara warwarewa cikin sauri. Innalillahi wa'innailaihir raji'un Umm..umm..Umma! Hajja yakolo taji an fad'a cikin d'aga murya,da sauri ta waigo tare da sakin abinda ke hannunta idanuwanta sunyo waje alamun rashin gaskiya maganar da akayi yasa yareemah Ngari saurin fitowa be kai ga k'arasa fitowa daga d'akin ba Aysa tace, Baah wait.! Cak ya tsaya cike da mamaki, nan da nan gid'ad'o ya zaro waya tare da matsawa ya kira Ammi tana d'agawa Aysa ta karb'e wayar jikinta na rawa tace, Hello Ammi gashi nan za'a k'arasa kashe baah.... Kasa k'arasawa tayi saboda kukan daya kwace mata, cikin tashin hankali Ammi tace, What.?! Aysa kuna ina? waye yake kokarin kasheshi? sannan duk ina security's d'in gida?! Kashe wayar Aysa tayi dan tafison suzo su gani bawai su tsaya tambayarta ba. Ai kuwa kafin kace mene tuni ta sanarwa da maimartaba mai murabus lokacin shi kuma yana tare yarremah babagana yana ta kwantar mai da hankali,yana jin haka suka mik'e duk a parking lot suka had'u dan haka dasu Ammi su yayya gamsu suka tafi a motar maimartaba maimurabu irin zungura-zunguran motocin nan masu tsadar gaske suka nufi dambu road. Suna zuwa gate man ya wangale musu gate lokacin duk masu tsaron gidan suna cikin side d'in yareemah Ngari sun hana hajja yakolo motsawa sai faman rantse-rantse take musu amma sam basu kulata ba,shigowar su Ammi ne yasa k'irjin hajja yakolo kuma bugawa a take ta hau kuka yayin da Maimartaba ya tsaya yana kallonta cike da mamaki jikinshi har rawa yake yi yasa hannu d'aya ya dafe saitin zuciyarshi. Aunty yaruwaiya da jikinta har rawa yake cikeda masifa tace, Dama ance rana dubu ta b'arawo ce,guda d'aya dal ta me kaya ce yau gashi Allah ya tona muku asiri a idon duniya, wallah baba ba ita kad'ai keyi ba harda Mami duk bakin su d'aya. Shi kam maimartaba sam kasa magana yayi gashi yana son nuna fushinsa amma ya kasa yin hakan sai dai yadda yakejin zafin a zuciyar shi har gara ace a fili yake nunawa yadda kowa zai gani yasan halin da yake ciki,cikin sark'akk'iyar muyar wadda ta shak'e yace. Ya haka?me kike yiwa kuka yakolo?! Sai a lokacin hajja yakolo ta d'ago kai ta kalleshi tunawa tayi da cewar hajja gajiram ta shaida mata cewar ta samai na cikin abinci yaci tayi saurin mik'ewa tare da k'arasawa kusa dashi cikin kukan kissa take cewa, Yauwa gara da Allah ya kawoka,yanzu ni yarannan zasu kallah suce wai nazo zan kashe yaron nan daga zuwa dubiya?! Da mamaki hajjagana ta kalleshi jin abinda zaice sai taga ya kamo hannuwan yakolo cikin lallashi yana cewa. Kiyi hakuri yara ne wata kira ko gamo sukayi sukaga kamar wani zai kasheshi ya b'ace shine suka ce kece,yi hakuri kinji. Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar hajja yakolo yayin da hajjagana ta kallesu zuciyar ta na zafi sabida ganin ga gask'iya k'iri-k'iri amma an taketa nan fa yayya gamsu ta fara bala'in nata aunty yaruwaiya na taya ta,kallon k'ofar bedroom d'in Ammi tayi taga yareemah Ngari tsaye cak ya kasa gaba ya kasa baya tabi gurin da kallo cikin zafin zuciya wadda takeson dannewa dan karsu fahimci halin da takeci tace, Karka fito ka bari ina zuwa. Juyawa tayi ta fita duk suka bita da kallo apartment d'inta ta shiga tana share hawaye da mayafin jikinta harta k'arasa wajan dustbin ta d'akko tsintsiya da parker ta wuce ta d'akko moper sannan ta shiga bedroom d'inta ta d'akko zam-zam da ganyen magaryar da ake mai magani da ita ta d'ebo,kitchen ta kuma biyawa ta d'ibi kanwa ta zuba cikin kofi tare da zuba ruwa tayi hanyar apartment din baah Ngari dasu. Tana zuwa bata kula kowa ba har su yayya gamsu da suke masifa bata kula suba ta fara share bakin k'ofar sannan ya yayyarfa ruwan kanwa a wajan sai da ta bi ko'ina na gurin da ruwan kanwa sannan ta k'arasa gurin yareemah Ngari tare da kamo hannunshi suka fito,fatanta koma me tazo dashi ya k'are mata a kanta tunda ai ba zuwa gidan suke ba bare ta tabbar da cewa lallai dubiya tazo. Ya kamata dai mu koma ni banga amfanin zuwa nan ba sam. Cewar maimartaba yana k'ok'arin juyawa ya fita, babu wanda ya tanka bare yajuya su tafi sai hajja yakolo da har lokacin jikinta be dena rawa ba,ganin har ya shiga mota amma basu fitoba yasa shi tura security guda d'aya yace yaje ya kirasu idan ba haka ba zasu tafi, koda yaje tarar dasu yayi duk sun zauna suna mayar da yadda suka ganta ya rissina bayan yayi sallama ba tare da ya kallesu ba yace. Ma'am Maimartaba yana jiranku. Kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, Kace mai mun dawo gaba d'aya. Ya kuma russunawa sannan yafita,koda ya sanar da maimartaba be nuna damuwa ba saidai hamkalinshi ya tashi amma bazaka gane hakan ba sai a cikin ranshi drive yaja suka bar gidan hajja yakolo kuwa kirjinta banda bugawa babu abinda yake yi har suka isa gida kowa ya wuce apartment d'inshi. Sam hajja yakolo k'in bari tayi su had'u da hajja gajiram sabida batama san abinda zata ce mata ba,da k'anwarta ta buga mata waya cewar gata nan zatazo sutafi sai tace mata kawai ta wuce gida ita tagama abinda zatayi ta tafi wani gurin a haka suka rabu shi kuwa sarki Aliyu hydar sam bema san abinda ke faruwa ba suna ciki shida Meenah sai wasan b'uya suke yi dan sam Meenah tak'i bari su k'ara had'a idanu. Cikin dare ko'ina tsit kakeji a cikin shehuri musamman idan ka fito wajan lokacin ne Hajja gajiram ta fito hannunta d'auke da maganin da boka ya bata wanda ta sanya shi cikin buta,sanye take cikin doguwar riga mai d'an girma ta yafa wani zani a kanta a haka ta sulale tayi apartment d'in Maimartaba sarki Aliyu hydar ... A hankali ta dinga tafiya har ta shiga ciki duk da cewar akwai dogarawa amma basu hanata shiga ba tunda suna ganin itama uwace a gurin shi, tana shiga ta fara lek'awa parlor sai ta hangeshi kwance kan three seater tayi murmushi sannan ta koma baya sam bata san ba bacci ya keyi ba dan gaba d'aya zuciyarshi babu dad'i saboda sosai yaga tsoran shi cikin kwayar idon Meenah ya rasa meyake mishi dad'i ya mik'e da kyar ya fara zagaye d'akin kamin ya wuce bathroom wanka yayi tare da alwala ya shimfid'a pray-mat ya hau ya fara sallah,ita kuma hajja gajiram tana waje tayi sib'itir tana aikin da boka yasa ta tana k arin binne maganin da dubura yana sallah yaji ana magana a waje tun yanaji kad'an-kad'an har dai yajiyo sosai yayi saurin sallamewa ya fito wajan dai-dai lokacin yareemah babagana shima ya shigo dan yaga shigowarta sannan kuma side guda maimartaba sarki Aliyu hydar ya bashi anan cikin nashi kan cewar kafin billy ta dawo,da sauri ya shige d'aki jikin shi na rawa idanunshi ya fara kankancewa kafin yaji ya sulale a k'asan gurin ya fad'i murya k'asa-k'asa yake furta, Mami! Mami!! Mami...!!! Shima maimataba sarki Aliyu hydar yana ganinta ya fara waige-waigen ko zaiga mutane ganin babu kowa yasa shi furta kalmar innalillahi'wa'inna'ilaihir raji'un Daa k'arfi hakan yasa hajja gajiram yin wurgi da layar hannunta tana zaro ido ganin sarki Aliyu hydar a tsaye a kanta ya juya mata baya. Rigarta ta raruma ta sanya a bai-bai tsabar k'id'ima ta fara niyar guduwa maimartaba maimurabus ya shigo apartment d'in ganin zata gudu yasa shi saurin rikota,kamar wasu yara haka suka dinga ja in ja Allah ya temaki shehu Bulama ya rik'eta kam kafin ya fara k'ok'arin janta suka koma nashi apartment d'in har yajata ciki tana turjewa tare da furta kalmar hakuri karya tonamata asiri ta tuba tabi Allah ta bishi amma fur saida ya sadata da d'akinshi ya wuce can kurya cikin wani kyakyawan akwati ya bud'e tare da janyo wata zungureriyar takobi sai faman shek'i taki yi ya koma kusa da ita sai faman runtuma mai ihu take yi ya sanya mata cikin hannunta tare da kwanciya a k'asa yace. Kasheni ki huta da duk abubuwan da zasu dinga sanyaki aikata shirka. Wallahi baba tana kashe ka nima zan kasheta sannan in kashe kaina damani k'arashe ne sannan naga duk abinda ya faru akan idona na gani. Dirim dim!!! Suka jiyo muryar yareemah babagana a bakin kofa yana hawaye idanunshi sunyi jawur tamkar garwashi dama shine ya kirawo mahaifin nasu yaje ya gani,shi kuwa sarki Aliyu hydar da sauri ya koma ciki,d'akin Meenah yaje ya bubbuga taji shi cikin wani irin murya hakan yasa taje ta bud'e tana bud'ewa ya fisgota seda ya rarumi labbanta yashiga sumbata na wasu yan dakikai nutsuwa tashige shi sannan yajata suka fita suka bi bayan babagana anan suka had'u duk suna cikin tashin hankali.... _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB IN IYAYE```
Chapter 89 · 0% Book details