← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 107

Sashe 100

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bayanta ya rik'e mararta na faman tsirawa,tashi tayi da kyar tana dafe ciki zata shiga toilet Ummanta ta ganta cikin mamaki ta tambayeta, Bilkisu lafiyar ki kuwa ina zaki haka...?! Bata juyo ba ta shiga toilet tana cewa, Umma kashi nakeji wallahi. Shiga tayi sai da ta dad'e sannan ta fito rik'e da baya kafin ta zauna ta sake komawa Umma tace, Ina kuma zaki koma bilkisu?! Wayyo Umma fitsari wallahi kashin ma yak'i yi kuma inajin shi. Bata dad'e ba ta sake fitowa tana k'ok'arin sake zama ta kuma cewa fitsari Umma na ganin haka ta fara kokarin kiran abba a waya yana d'auka tace, Malam sai ka dawo gida domin ga bilkisu nan ta fara nak'uda. Ai abba yana jin haka ya taho gida a hanya ya bugawa yareemah babagana aikuwa a tare suka dira motocin su a kofar gidan domin dam a shima yareeman yana hanyar zuwa gidan. Umma kuwa ta d'an harhad'o duk kayan da tasan za'a buk'ata dan haka abba na shiga lokacin abun yayiwa Billy tsamari ya kamota bayan an sanya mata hijjab, a motar yareemah babagana ya sata suka tafi shida Ummi abban kuma suka tsaya k'arasa d'aukan abin buk'ata sannan suka bi bayansu. Cikin ikon Allah suna zuwa aka wuce da ita labour room,drip kawai aka sanya mata da wasu allurai a ciki (inducing)kafin wani lokacin billy ta haifo kyakyawar 'yarta, wani nishin akaji tana yi nan fa aka kuma dukufa shima ba jimawa sai ga baby ta biyu, sunsha mamaki dan duk sanda sukaje scanning cewa akeyi d'aya ne ashe Allah ya boye abinsa. Sai da tasha d'inki daga nan wani wahalallan bacci yayi awan gaba da ita, lokacin da aka kawowa yareemah babagana yaran ya gansu ya tuna cewar nashi ne halak malak sai kawai ya saki kuka baji ba gani abba ya buga aka sanarwa da shehu bulama kafin wani lokaci sai ga Ammi,Allah sarki Ammi inuwar giginya ce kowa yana shigarta yasha inuwa mai dad'i. Shiga yayi cikin d'akin hutun da aka kaita, bacci takeyi hankali kwance fuskarta tayi fayau yareemah babagana ya rik'o hannunta yana hawaye yasan da idanunta biyu sai ta mazge shi sabida ta tsaneshi bata son ganinshi, a hankali ya tashi ya kwanta a jikinta ba tare da ya sakar mata nauyinshi ba.ya dad'e a haka kafin ya zauna kusa da ita kaunarta da soyayyar na k'ara bin sassan jikinshi anan su Ammi suka shigo suka tarar dashi. Sai bayan sallar magrib sannan billy ta farka idanta tar akan yara guda biyu dake hannun kanwar Umman ta wato yakumbo Dije murya k'asa-k'asa tace, Yakumbo nah. Yakumbo ta mik'e da sauri da yaran a hannunta ta k'ara bakinta bud'e tace. Sannu 'yarnan sannu kinji Allah ya saukeki lafiya mun gode mishi. Yakumbo kuma biyu na haifa a cikina?! Eh kuwa bilkisu gasu ma kuwa yaran sak mahaifinsu farin ne kawai naki. Nan da nan billy ta saki kuka haka ta dinga yi ba k'ak'autawa sai da tayi mai isarta lokacin su Ammi sun dawo aka samu ta basu nono suna sha tanajin wani kaunar yaran tana shigarta,bayan sallan isha'i suna zaune a d'akin yareemah babagana ya shigo be kalleta ba ya kalli Ammi yace, Ammi ku d'akko yaran mu tafi gida. Ai billy najin haka tayi saurin rungume guda d'aya a jikinta tana kokarin kwatar d'ayan a hannun Ummi yareemah babagana yai saurin rigata ansa yace, Meye naki a ciki? Da bakinki kika ce bakya so kin tsanesu dakin haihu za'a kaisu gurin mahaifinsu, toh yanzu kin haihu zan tafi da yarana na samu me shayar dasu bani d'ayar. Ta fad'a tana kokarin kwace ta hannunta, kuka ta farayi tana buge mai hannu cikin tashin hankali da kuka tace, Wallahi karya ne ni bance haka ba kabar min yarana wallahi baxan baka ba ai ba wani ya haifar min suba nawane... Mutanan d'akin suka fara musu dariya ganin yadda take kuka ne yasa shi mik'a mata d'ayar babyn tayi saurin karb'a tana sauke ajiyar zuciya dama can haushin shine ya shafi cikin. Kwananta biyu a asibiti aka sallamesu, babagana yayi matukar yin k'ok'ari daga 'ya'yan nashi zuwa uwar harma da iyayanta ta,sai dai da kyar maimartaba mai murabus ya taushi zuciyar shi aka sanyawa d'aya sunan hajja gajiram wato hasanar usainar kuma sunan Ammi aikuwa tayi murna da farin ciki,sannan da ita akayi komai bata kyamar talaka mutane har mamakinta sukeyi yadda suka ga ta zage sai abubuwa take taya su.Anyi suna lafiya su Meenah, Basmah,layla, Aisha (kiara) duk sunje suma anyi suna dasu hakan ya k'arawa babagana kaunar Ammi duk wani abun suna kuma sai da Ammi ta d'auka akaje aka turawa hajja Gajiram cikin kejin da take, wani taci wani ta b'arar wani ta yagalgalashi haka ta dinga yi calander hotunan yaran kuma ta cire d'ankwalinta ta goya wai tayi yara Allah ya kawo sauki. Ranar wata weekend Aliyu Hydar da Meenah sunje asibiti awo daga nan suka biya gidan yareemah Ngari dake wani sashe a shehurin xaune suka samu Ngarin da matarsa Asmy a garden dinsu suna xaune kayan marmari a gabansu hankalinsu kwance sunyi mugun dacewa,zaune yareemah Ngarin yake yayi xaman k asaita ita kuma Amarya Asmy tayi pillow da cinyarsa hannunsa kan gashinta yana shafawa suka jiyo sallamar su Aliyun akansu da sauri Asmy ta mike xata tashi Ngari ya rik e ta, Babe Ina xaki?! Mon Amour I need to cover my head,scarf dina yana ciki Oh.. cewar Ngari sannan yai pecking dinta a kumatu ahankali kamar me rada cikin kunnenta yace, I love you...come back soon Kashe masa ido d aya tai sannan ta mike tashiga ciki,karasawa su Aliyu sukai dake faman shasshshafa keya murmushi Ngari yai bayan ya buga masa jarida akai, Da magana abakin ka bruh Baa Ngari bakomi wallahi kawaide Ina admiring kinda love dnku ne Allah yabar ku tare Oh Yayi kyau.. cewar Ngari don bai cika magana ba Ahankali Meenah dake gefe tace, Barka da rana baa,munsa meku lapia?! Lapia lou sisturh,Mungodewa Allah ya k arfin jiki?! Cikin jin kunya Meenah tai shiru kawai hade da sake sunkuyar da kanta k asa mintina kadan Asmy tadawo bayanta wata baiwa ce dake dauke da trays da drinks da snacks akai ajiyewa tai agabansu sannan ta koma gefe ta xauna, Sannunku da xuwa,Barka da yamma ranka ya dad e maman baby hope babyn mu yananan lapia? Amsawa Aliyu yai itade Meenah murmushi kawai tai kanta akasa don duk sanda aka ambaci ciki kunyace take lullubeta..Sund an taba hira tare daga bisani Asmy taja hannun Meenah suka koma cikin gidah suka bar yan uwan junan tare nan suka shiga hirar zumunci cike da kaunar juna abinde se sam barka kawai.. Kodah suka koma gidah sashen Basma ya wuce yaga yadda take tukun sannan ya wuce fada a k ofar fada ya tarar da Modu xe shiga ciki nan suka gaysa sannan suka k arasa shiga ciki suka baje akan kujeru kasancewar ba kowa a fadar yamma tayi,Modu ne ya kece da daria yana faman shafa gemunsa tsaki Aliyu Hydar yai yana harararsa,cikin takaici da isa yace, Kaga Malam idan bawani almuhim abune yakawoka ba katashi kabani waje plss Guy meyai zafi wani abune natuno ne daya faru a yola da muka je Yola kukaje kenan?! Nah tun yolan da mukaje dakai,kalmomin shekaru ukun nan still suna mun yawo akai abun har yau daria yake bani.. Wane abune plss guy don t ruin my mood abeg Katuno sanda kace idan ka auri Meenah baby sitting xakai don raino xa a baka?!shine nake tunowa kuma yanzun yadda kai dying akan sonta dama na fada maka ai kaki yadda yanxu wa gari ya waya?! Modu ya k arasa fada yana sake kecewa da dariya.. Dogon tsaki Aliyu Hydar yaja lokaci d aya kuma kyakkyawan murmushi ya fad a a fuskarsa cikin wata irin murya yace, so ne yasani fadar haka believe it or not Kobah so ba Kai kasanni ai,kuma kasan yadda nake idan inason abu...Meenah means the world to me,to cut the long narration bantab a son mace kamar yadda nakeson Meenah ba I love her so much I can sacrifice anything for her love.. I hope tasani ko?! No sena samu time tukun she knws I loved her amma batasan son da nake mata yaxarce wanda take tunani ba Then warra you waiting for?!tell her mana kamar ba namiji ba No sena gama da abunda nasa agaba tukun Kai guy banajin baaba xe yadda da abinda kake shirin yi Seka hanashi ai.. Nason is not easy but you just have to calm your self d... Be k arasa ba Aliyu yai saurin katseshi, Kai I can t aswr i can t i I i i I just can t guy bana samun time din kaina dana family dina for example Meenah yanzu tana bukatar kulawa agareni.. Somehow true.. Bawani somehow gaskia ne kaji To Allah yaxaba abinda yafi alkhairi Insha Allah rabbi alkhairinne ma.. When xaka samu baban yacemun ze koma germany ko Yeah!kafin yatafi de zansameshi May be gobe ma idan Allah yakymu To Allah yakymu goben lapia Ameeeen Da wannan suka shiga wata hirar daban sunayi suna tafawa.. _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB IN IYAYE```
Chapter 100 · 0% Book details