Sashe 96
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
magana ka barta duk abinda take yi ta sani. Shiru gurin yayi sai kukanta da yake tashi yayin da hajja yakolo tayi tsomu-tsomu da ita jikinta sai rawa yake yi Ammi na kallonta sai dai kawai ta girgiza kai Shehu Bulama ya fara da cewa, Alalhak'ik'a dole ne na fara godewa Allah subahanahu wata'ala daya bani ikon yin numfashi a doran k'asa,ya bani lafiyar yin aure abisa sunnar ma'aiki sallawa'alaihi wasallam,ya kuma albarkace ni da yara masu yawa masu albarka Alhamdulillahi a kullum ina gode mishi, A cikin daddad'ar rai da rayuwar da ya bani dama ya sanar damu cewar akwai kaddara a duk jikin bayi masu rayuwa a doran k'asa, nasani Allah ya jarabce ni da mata da 'ya'ya wad'anda nasan suna d'aya daga cikin kaddarata kuma na karb'eta banyi fushi kojin haushi ba amma kaf cikin ilahirin iyalina babu wanda bansan halinshi ba sai dai duk abinda kayi zan maka nasiha bazan nuna maka cewar nasani ba idan kaji falillahil hamdu idan bakaji ba bani na fad'a ba fad'ar Allah ce yau gashi asiri ya tonu kowa ya fito da halinshi na fili dana b'oye. Tari ne ya sark'eshi ya fara yi ba k'akk'autawa da sauri Ammi taje ta zuba mai ruwa ta bashi yasha sannan yayi shiru sai da ya lafa kowa nayi mai sannu sannan ya cigaba da cewa, Yau gashi tun tsawan shekaru da wad'annan bayin Allah suka d'auka akan rayuwar abokiyar zamansu da ba ita ta kawo kanta ba,kamar yadda na auro su har gaban iyayansu haka itama na aureta.sannan kamar yadda'ya'yansu suke nawa haka itama nata nawane halal malak amma sai suka sanya mata idanuwa daga ita har yaranta basa san ci gabansu tun suna k'anana har kawo jiya da idanuwana dana yaronsu ya gane musu mummunan abu wanda bazan iya sanar daku ba sai dai bana fatan hakan ya sake faruwa koda kuwa a mafarki. Shigowar Modu ne yasa kowa kallon kofar ya shiga yana sunkiyar da kai domin shi bashi da labarin meeting d'in sai yanzu da sarki Aliyu hydar yayi mai text message sannan yaga na baban ma wanda yayi mishi da dare, ya samu guri ya zauna sannan baba maimurabus ya ciga ba da yin magana, Yau gashi hakuri da tawakkali yasa komai ya warware cikin hukuncin Allah,sai dai Allah ya jarabce ni da d'a/'ya wanda aka samo min shi ta hanyar da be dace ba. Sannan Allah ya jarrabi d'ana da soyayyar wata baiwar shi wadda itama hakkinta ne Allah ya biya mata yau gashi yana cikin halin takura da nadama Duk cikin tuggun wad'annan bayin Allah suka jazawa baiwar Allah har suka ja mijinta ya rabu da ita alhalin suna son junansu amma su basu ga hakan ba,shin wai me suke nema na kasa ganewa?! Baba Allah ya k'ara maka hakuri ya kuma k'ara maka tawakkul muma ya bamu irin hakurinku. Suka jiyo muryar Modu wanda yayi k'arfin halin yin magana duk da cewar besan silar maganar ba. Baba maimartaba ya d'ago yana kallonshi yace, Amin ya rabbi kullum fatana Allah yayi muku albarka. Amin baba. Duk suka fad'a Aliyu hydar dake zaune sai satar kallon Meenah yake yi ita kuma da sun had'a ido zata turo mai baki cike da shagwab'a duk abinda suke yi Ammi na kallonsu gaba d'aya ta rasa gane waye wawan a cikin su dan tsabar wauta sai yi suke yi tamkar ba sarki ba soyayya ce fal a cikin idanunshi da gangar jikinshi ta d'auke kai tare da tab'e baki cikin ranta tace. Allah yasa ma suna jin abinda ake fad'a. Falmata ta mik'e ta k'arasa gurin mahaifinsu cikin kuka ta durkusa tana neman gafararsa yace, Ai ni falmata ban rik'e kowa ba nawa da wanda ba nawa ba fatana muyi sa'a Allah ya yafe mana duk kurakuran mu,sai dai bansan yadda zaki yi rayuwa da wannan cikin dake jikin ki ba gashi kuna final year. Sai a lokacin kowa ya gano wadda aka ce ta samo d'a/'ya ta kuma rushewa da kuka dama hajja gajiram bata yi shiru ba har lokacin tamkar ma bata cikin hayyacinta dan yadda takeyi tana faman harare-harare tana sosa cikin kunnanta tare da yarfe hannu,baba maimurabus yace. Ni yanzu ban san yadda za'ayi ba sai dai ki ajiye jarabawar domin fitarki da wannan abu shine tonuwar asirina na uku baya ga na mahaifiyarki dana d'an uwanki dan ma shi Allah yayi mai lud'ufi ya samu ya aureta harda rabo a tsakanin su, sai dai ta gujeshi alokacin da shi d'in yake tsananin buk'atarta. Kaza...kaza..Kazan...ub....can! K'arya ne wallahi Allah ni za'a yaudara dan kaza...kazan uw... Can?toh wallahi kunyi karya domin sai hajjagana tabar gidan nan,sai Aliyu yabar kujerarshi yabi duniya yayinda Ngari zai k'arasa barzahu,wallahi tallahi sai 'ya'yanta sun shiga duniya dagani sai 'ya'yana mune zamu zauna a cikin shehurin nan, Sannan nace bana son bilkisu kai babagana shegen taurin kaine dakai tamkar d'an gidan fir'auna nace maka bana son bilkin nan amma ka nace tun sanda na kamaka akanta shine yanzu dan ubanka harda yi mata ciki ko? itama yakolo da muke aikin tare so nake mu kammala komai itama na koma kanta hahahaha ho ni shegiya..! Suka ji hajja gajiram na fad'a idanuwanta sunyi jajawur gashi sunyi manya tamkar zasu fito waja yayin da hajja yakolo ta zaro idanuwa tana kallon hajja gajiram cikin tsananin mamakin jin kalamanta. Alhamdulillah kayk'ayi koma kan mashek'iya Allah ya mayar muku da abinku Allah ya k'ara. Yaya gumsu ta fad'a cikin tab'e baki tana hararar su, baba maimurabus ya dafe kai tare da dafe k'irji jin irin surutan da hajja gajiram keyi da sauri yareemah Ngari da Modu suka k'arasa wajan shi suna k'ok'arin gyara mai zaman sukuma sauran yaran sai kuka suke yi dana gajiram d'in dana yakolo sai Affy yayin da Meenah ta mak'ale jikin aunty yaruwaiya jikinta sai tsuma yake ganin tamkar hajja gajiram ta samu tab'in hankali. Kayya gumsu kiyi shiru dan Allah.. cewar Ammi, Sake gyaran murya shehu Bulama yai xe cigaba da magana kenan hajja Gajiram tasa ki wata bahaguwar kara sekace bijimin sa tanayi tana shusshura k afafuwa, Ammi da Ayiya ne sukai kanta don ganin tana k arin yage kayan jikinta cikin suratai tafara magana tana bubbuge hannayensu daga jikinta, Jakadiya Mangu Allah ya isa tsakani na dake Jakadiya mangu kilan kece kika hak o asirin da mukai akan Ngari dake rijiyar kauyen damboa... Dafe kai Ammi tai tana k arin rufe bakin Gajiram dake surutai,wani tsalle Gajiram tai tatashi akan k afafunta duk kowa na parlorn ya bita da kallo cikin soshe soshe da cixgar gashin kai tashiga reto maganganu, Mune muka raba hajjagana daga gidan nan munso fitar da ita gaba d aya to bokan ta yafi namu Tsaki aunty yaruwaiya ta saki kafin tace, Wallahi yayya da Allah ta dogara wahidin Ahadin domin shi din mabuwayine gagara misali Daria Gajiram ta saki cikin rawa tacigaba da magana tana sosar kai kamar me kwarkwata, Mune muka nakastar da yareemah Ngari tun lokacin shayinsa mukai amfani da jinin don cinma manufarmu akansa,mune muka sanyawa shehu Bulama ciwo domin ya mutu babagana ya gajeshi a mulki sede kassh hakan be yiwu ba domin shegen d an na hajjagana da mukaso yaxama dan iskan daya gagari iyayensa shine yanxun akan karagar mulkin bornu Daria Gajiram tasake kwashewa da ita itade yakolo dake gefe jikinta se bari yake ganin bilhaqqi da gaskia gajiram din taxama me tab un hankali tatas sihirin da suka aikata se xayyano su take, Ni Gajiram nida Yakolo da temakon amintacciyar jakadiya ta wato Mangu mune nan muka shiga tsakanin Aliyu da matar sa wato Basma itama da yake idonta ya rufe ta aikata duk abinda mukace gashi yanxun tayi biyu babu babu haihuwa ta sanadiyar toshe mata mahaifa da mukai da kuma rabuwar igiyar aurenta da Aliyu.. Sake fashewa tai da daria,Babagana dake gefe kawai girgiza kansa yake yana hawaye hakama sauron yayan nata gaulayen kuwa se tabe tab e suke ya xungorota da k afa ita kuma ta cuno baki tana janye kafar tasa Aunty yaruwaiya dake kallon su take taiwa gumsu sign da ido girgiza kai kawai sukai suka cigaba da jin xancen sabuwar tabi wato gajiram.. Ni Gajiram nida yakolo mune nan kwananan lokacin tarewar figaggiyar yarinyar can wato Meenah muka tafi har kauyen gombole muka hadu da sabon boka yabamu aiki Kan idan har muka aikata tofa komai namu xe dedeta idan har kuma aka samu akasin haka to yana tabbatar mana da cewar reverse s d case,,heheh akan iyalan hajjagana kaf mukai aikin dama shehu Bulama domin cinma burinmu wanda muka dade muna muradi, Yakolo akace ta binne abu a karkashin inda Ngari yake kwana da kuma farfajiyar gidan hajjagana ni gajiram.. sekuma ta fashe da daria tana nuna kanta dayan hannun kuma tana sosa duburarta dashi, Ta jima tana soshe kafin tacigaba, Ni Gajiram ni bokan nan yabawa aiki yasa nadena sallah da duk wani aikin ibadah nabawa shehu Bulama maganin acikin abinci batare da yayi basmala ba kamar yadda boka ya umarta yanzu ...Yanzu...Yanxu abu na ukun xan aikata xan binne laya da duburata batare da wani yaganni ba kuma ba kaya ajikina xanyi a farfajiyar sashen Aliyu.. Tana gama magana ta arce waje da gudu tana ihun, Karku bari tsinannun sugani aradun Allah se zuriyar hajjagana kakaf ta wulakanta.. Binta abaya su Ammi sukai domin sitirce mata jikinta don duk ta cire kayanta ta xubar a bakin kofa xigidir haihuwar uwarta da alama de kwakwalwarta ta tab u,Parlorn yakoma daga shehu Bulama se su Affy da hajja yakolo dake faman mitsitsika idanuwa da tafukan hannayenta girgiza kai kawai shehu Bulama yai hade da ajiyar zuciya yajima kafin ya dubi yakolo ya soma magana, Ina fatan kinji duk abinda Abokiyar xamanki take cewa shin duk abinda tafad a ki fadamin wannene be koma kan tata xuriyar ba?! Ba cin fuska ba duk abinda tafad a yafaru akan yayanta kinsani nasani kowa yasa ni,to ked in wacce ribar kika samu inbanda koma baya tur da hali irin naku Allah ya shirye ku shine magana ta kawai.. Ya k arasa magana yana jinjina kai,kuka yakolo ta soma tana girgiza kai, Toh dan Allah ku kunna fitilar parlorn kada ku azabtar dani wallahi tilastani tai.. Me..?! cewar shehu Bulamaa hade da sakin siririn