← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 107

Sashe 18

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Wannan shafin nakine ke kad'ai yaya HAJJA CE,tareda y'an grp d'inki HAJJA CE NOVELS GRP
_24/25_
"Guy dan Allah kasaki ranka ayi komai agama shi lapia pls i beg of you kaji?!"
Nodding kansa kawai yareemah Aliyu Hydar yayi batare daya bashi amsa ba,a hankali drivern ke jan motar har cikin k'aton katafaran mansion d'in na Mai Alooma Ghaji,kai daka gani sekayi tunanin ko gidan shugaban k'asa ne saboda yadda ya tsaru ga fitulu ta ko'ina tamkar a turai.Tun daga gate xaka gane cewar lallai manyan bak'i sunxo saboda yadda aka baxa securities,mazan gidan da shi kanshi Mai Alooma Ghaji duk suka taresu cikin murna k'arasowa Mai Alooma Ghaji yai kusadasu tareda rungumesu duka kasancewar rabonsu da garin tun suna k'anana cikin farin ciki da jin dad'i yace masu;
"Welkm home my grand children"
Gaisheshi su Aliyu Hydar sukai ya amsa cikeda fara'a tareda kama hannuwansu suka doshi wani k'aton apartment manyan mazan gidan suka bisu abaya,suna shiga Mai Alooma yakallesu cikeda farin ciki yace;
"Ku huta kuci abinci gashi can a dinning later seku gaysa da grannies d'in naku da sauran family members"
"Toh Baffa"kamar yadda suke ce dashi...
Aliyu Hydar ya murmusa dak'yar domin gaba d'aya zuciyarsa babu dad'i sede yadaketa yadda babu mai iya gane yanayin dayake ciki daga haka su Mai Alooma suka fita shida sauran manyan y'ay'an nasa cikeda farin ciki domin shi yana cikin jin dad'in yadda za'a had'a auren yareemah Aliyu Hydar da yarinyar shi fatan Allah yasa ayi komai cikin kwanciyar hankali yai had'e da komawa wajen securities ya sake jaddada masu da su bawa sashen su yareemah Aliyu Hydar tsaro sosai...!
WANENE MAI ALOOMA GHAJI?!
Mai Alooma Ghaji k'anine ga mahaifin mai martaba shehu bulama wato mahaifin yareemah Aliyu Hydar,Mai Alooma Ghaji baya sha'awar sarauta kwata kwata shide yafison harkar siyasa tun wancen lokacin yayi sanata yayi d'an majalisa yakuma rik'e mai bawa shugaban k'asa shawara har na tsawon shekaru inda aka bashi matsayin ambassador for peace daxe wakilci Nigeria a Istanbul (Turkey) yajima yana rik'e da matsayin ambassador har na tsawon shekaru talatin sannan yai retire da kansa inda yanzu babban k'usa ne a k'asar Nigeria k'aton fili gwamnati tabashi bayan yayi retire agarin na Yola_jimeta inda ya tsantsara katafaren mansion d'insa babu abinda babu aciki har islamiyyar yara duk akwai ciki,matansa guda biyu ne Aunty majiiddah matarsa tafarko shuwa ce yar asalin T'chad ita kuma d'ayar matar tasa sunata Aunty inna wuro bafulatana ce ita kuma y'ar Gombe wadda akece da ita yafendo.. Aunty maijiddah tanada y'aya bakwai maza hud'u mata uku babban d'anta sunansa lamido se bello,bukhar,sekuma k'araminsu a maza Ahmad sukuma matan akwai khadija wadda akece da ita yakaka(babbar yaya)se Gumsu sekuma y'ar autar su Amiina wadda aka haifeta lokacin har ancire rai da haihuwar ma saboda bak'aramin shekaru manyan yayyun nata suka bataba duk yayyun nata mata sunyi aure mazan ma guda biyu sunyi aure saura biyu kawai daga bukhar se Ahmad suka d'aine basuyi aure ba..
Ita kuma yafendo tanada y'ay'a biyar duk maza ne Allah yabata babu mata har kuma haihuwar tata tatsaya,akwai muhammad se uthamn,Aliyu,Umar sekuma shehu wanda yaci sunan mahaifin su yareemah Aliyu Hydar ana kiransa da Bulama sekuma autansu Gidad'o wanda yad'an d'ara Amina da shekaru kad'an,acikin maxa biyar d'in datake dasu uku sunyi aure saura me sunan mai martaba kawai da kuma d'an auta Gidad'o. Gidan Mai Alooma Ghaji gidane dayake da had'in kai babu ware waren yan ubanci baxaka tab'a kawowama kishiyoyi bane domin babu kishi atsakaninsu kowacce tana xaune da yar uwarta cikin mutunci da dattako,tun Amina tana y'ar k'arama Aunty maijiddah tabarwa yafendo ita ganin batada mace ko d'aya awajenta takuma rik'eta tsakani da Allah kaikace ita ta haifeta..Bayan y'ay'ansa da matansa gidan Mai Alooma Ghaji cike yake da y'an uwa da y'ay'an yan uwa wanda yake rik'e dasu ciki harda k'anwarsa da mijinta yarasu shekarun baya gaba d'aya itada y'ayanta susu shida rid'a rid'a hud'u da k'anana biyu suke xaune agidan a b'angaren daya gina masu daga d'ayan sashen,kuma kullum abinci mai rai da lapia ake agidan babu harkar k'aranta duk juma'a ake abinci mai rai da lapia akai masallatai da mak'ota ga kuma Mai Alooma Ghaji foundation dayake dashi ake tallafawa marassa k'arfi na garin,ganin irin hidimomin da Mai Alooma Ghaji kewa garin na yola yasanya sarkin garin yimasa sarautar 'hakimi wato zannan yola'...
...............
Modu ne yaxubawa yareemah Aliyu Hydar ido ganin yadda yasa abinci agaba yana cakuna shi kwata kwata ko rabin rabi beciba kusan awa d'aya kenan da xuwansu siririn tsaki modu yasaki shide yareemah Aliyu Hydar ko kallon inda modun yake beyiba yade tasa shinkafar jollof rice agaba datasha sauce na roasted beef yana cakulata,wani tsakin modu yasaki akaro na biyu a kafule yace;
"Haba guy haba tun d'axu nina mance danaci abinci kai kaxauna sewani yafutarsa kake kamar ba cikinka xaka kaiba dan Allah kayi sauri bafa mugayda matan Baffa ba"
"Muje kawai"cewar yareemah Aliyu Hydar had'e da mik'ewa tsaye
"Ka k'arasa kawai"cewar Modun
"No I'm full"cewar yareemah Aliyu Hydar had'e da k'arasa sipping furar dake hannunsa
Atare suka fita suka fara nufar sashen Aunty maijiddah tana xaune gabanta d'auke da kayan itatuwa na turaren wuta parlorn se k'amshi yake Atare suka had'a baki suna gaisheta da fullanci nadaga kad'an daga abubuwan dasuka sani;
"Yallijam Aunty maijiddah??"(Anwuni lapia?)
"Jam Alhamdulillah"(lapia Alhamdulillah)tabasu amsa tareda fad'in sunayensu
"Noi fewol?(ya sanyi),Noi Basshi?(ya yara)"
"Jam Alhamdulillah"Aunty maijiddah tabasu amsa murmushi fadad'e a fuskarta a nutse tace;
"Noi kode(ya aiki)?!"tace dasu
Sosa k'eya modu yai sannan yace;
"Aiki tukunna de Aunty"
"Toh Allah yakawo nagari"tafad'a cikin hausarta dabata futa sosai
"Aunty kayan k'amshi kike had'awa ne??"
cewar modu dakebin kayan itatuwan gabanta da kallo had'e da d'aukar wani icen yana sunsunar k'amshin jikinsa murmushi Aunty maijiddah tai ahankli tashiga nuna masa kowanne da sunansu;
"Wannan gaf gaf ne ga irik ga kajiji ga hawi wannan misk ne se gallo ga dufur,wancan sandal ne se garin ambar se itacen duraf da al'ud wa'inan kuma khumrori ne na ruwa"tak'arasa zancen murmushi fad'ade a fuskarta
"Wow... Gaskia inason k'amshinsu"cewar Modu
"Ai sunada dad'in k'amshi"inji Aunty maijiddah
"Sosai sosai,more grease to ur elbow Aunty"
"Amin Amin"
"Aunty yayasu Gumsu agidajensu??"
"Alhamdulillah sunacan kowacce tana garin aurenta,y'ayansu ma sunxo hutun mid.term break inaga suna compound suna wasa bakuga taron yara ba awaje??"
"Okay. A'a gaskia bamu ganiba kila kosun bar wurin"
"Eh may be sunkoma b'angaren yafendo"
"Eh"modu yace had'e da d'akko wata hirar
Duk maganar da suke kanzil yareemah Aliyu Hydar bece ba kansa na k'asa harseda yaji modu namata sallama xasu je sashen yafendo tukun sannan shima yasa baki yamata sallama sannan suka mik'e suka fita xuwa sashen yafendo sunkusa kaiwa sashen yafendon suka fara jiyo sautin yara da alama rigima suke sunata tsokana suna guje guje suna fad'in;
"Ayye yaya meenal tabargazuzu yaya meenal tabargazuzu"
wasu guggun yara ne kebin wata yarinya suna fad'a mata haka ita kuma tana d'aukar duwatsun dake baje a k'asan wajen tana jefa masu,wasu daga cikinsu sund'akko kamannin barebari wasu kuma kamannin Fulani sukayo,
"Narantse da Allah yaro yasake bina yana tsokanata sena gunguri buroubansa"
Yarinyar dasuke tsokana ce ke fad'in haka tasaka hannunwanta akan k'ugu tana jijjiga kamar wata uwar mata,bayanta kawai su Modu suke gani kanta bad'an kwali kanad'add'en gashinta yakwanta har bayanta, riga da skirt ne ajikinta na atamfa sun d'an kama ramammen jikinta dayake kallo d'aya xakai mata kagane kwata kwata batada kib'a ko kad'an shapeless ce ta k'arshe sede tanada tsayi sosai tubarkAllah
"Amma aunty kefa kikace duk wanda yai loosing ayi mashi wannan wak'ar"wata yarinya ce ke fad'awa wadda aka tsokana haka
Uwar harara wadda suke cewa aunty Ameenan tawatsa mata xatai magana kenan wani daga cikin yaran dayafi Ameenan shekaru ne yashek'e da daria a gadarance yace;
"And we must continue cux haka kikace se anyi"
"Gidad'o.."
Ta furta da k'arfi dede lokacin sukuma su Aliyu hydar suka k'araso k'ofar daxa'su shiga sashen yafendon kasancewar awajen yaran ke wasa Wanda tacewa gidad'on ya bushe da daria san ransa sannan yace;
"Meeno tabargazuu.."
had'e da fecewa da gudu yabi tabayan su yareemah Aliyu Hydar danko lura dasu beyiba a zuciye Aminan ta kwaso jik'akkiyar k'asar dake cikin flower da aka bawa ruwa jikake yarrr tawatsa a kyakkyawan farin yadin dake jikin yareemah Aliyu Hydar dayasha d'inki saboda tsabar zuciya idanuwanta sunrufe batamasan wata watsawa d'iff kakeji yaran sunyi shiru suna kallon sarautar Allah,shikansa yareemah Aliyu rasa bakin magana yayi se jijiyoyinsa nakai dasuka tashi,duk surutun Modu indimi alokacin shiru yai saboda yasan dayayi magana kansa abin xe dawo,Amina dake gefe ganin b'arar b'aramar datai raba idanuwa tashiga yi jikinta se rawa yake shikwa Gidad'o arcewa yai yayi b'angaren aunty maijiddah dan kai rahoto,k'arar bud'e k'ofar da akayine yasa kowa juyawa yana kallon k'ofa banda yareemah Aliyu Hydar dakansa ke k'asa idanuwansa sun kad'a sunyi jajir ,Aunty yafendo ce talek'o da sauri tasa hannuwanta tadafe k'irjinta cikin fullanci tafurta;
"Handimin boni...(Nashiga uku) tareda sake bin kayan yareemah Aliyu Hydar da kallo dayai face face da jik'akkiyar k'asa....
#TeamSRKZI?!
Ignore my typos pls,banyi editing ba
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_*
Chapter 18 · 0% Book details