← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 107

Sashe 2

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
_2_
***Shehuri(shehun borno palace); convoy d'in motocin su yareema Hydar nashiga fadawa sukazo suka taso suka saka bayan babbar rigunansu suka kareshi suka shigar dashi cikin masarautar, agajiye yake lik'is ganin mai martaba na fada suna meeting da wazirinsa yasa kansa tsaye ya wuce cikin gidah part d'insu, yana xuwa ya xaro handkerchief d'insa yai hanxarin toshe hancinsa as usual parlor d'in anyi littering d'inshi da leftovers na abinci se robobin lemuka kala kala duk a barbaje ga kwalin aspen taba awajen kamr parlorn mahaukata,dogon tsaki yareema Hydar yaja ganin haryanxu step brother d'insa yareema babagana yananan da halinsa na k'axanta da shaye shaye...
Compound yakoma na sashensu, a sukwane bayi/dogarai sukayo wajensa had'e da yin gurfane inda yake...
"Gaisheka yareema Hydar d'an sarki jikan sarki,d'an g...."basu k'arasaba yareema Hydar ya tsayar dasu..
"Sarkin gidah inaso kazo da dakaran tsafta yanxu kuyi hanxarin gyaran sashenmu...."
"Angama yareema Hydar kaga d'an sarki wanda xe gaji g..."
Basu k'arasaba yai saurin d'aga masu hannu don inda sabo yasaba jin wannan kirarin... A sukwane suka kwasa aguje sukai cikin gidah b'angaren su Hydar.Gyara sukahau yiwa wajen seda suka gyarashi tatas sannan suka bar sashen,se asannan ya shiga cikin sashen nasu yai hanyar d'akinsa,tafkeken d'aki ne komai fari had'e da parlor aciki kujerun blue da kayan kallo,band'aki yashiga yai alwala yai wanka sannan yai sallah, yad'akko abin turaren wuta ya jona ya bulala turaren wuta tuni d'akin yahau k'amshi ,ba'a jimaba mai martaba yak'are meeting sannan yareema Hydar yaje suka gaisa har sukaci abinci tare sanin halin kishiyoyin uwar tasa ba bashi xasuyiba seda yad'an caccakuna yaci ba lefi dayake ba ma'abocin abinci bane sannan mai martaba yace yaje wajen sauran iyayen nasa ya gaishesu ...
Sashen hajia gajiram yafara xuwa wacce itace uwargidah, kafin yashiga seda jakadiya tai masa iso Kamar wani bak'o,yashiga ko ajikinsa had'e da d'an tsugunnawa cikeda girmamawa cikin harshen kanuri yace;
"Yayya inda dubdo?!(Ina yini yayya?!"yafad'a hakan cikeda ladabi..
Seda Hajja gajiram tacika ta batse kafin ta amsa da kyar kamar me ciwon magana;
"Kelewa selai...(lapia Alhamdulillah)" tak'arashe maganar cikeda tsana tana kuma wurga masa harara ta k'asan idonta
Bedamuba ya mik'e don yasan hakan xata faru inda Sabo yasaba ganin beyond hakama,sashen hajja yakolo yanufa itama ya gaidata same abinda tamai kenan, ko ajikinsa itama Haka ya mik'e yakoma sashensu,yana xuwa yaciro sim d'insa yasaka yai dialing number mahaifiyarsa hajia hajjagana ringing d'aya biyu tad'auka...
"Salaam alykm Ammee inda dubdo?!"
"Kelewa selai Hydar,kazo garine?!" Ammee tafad'i hakan cikin nutsuwa da dattako
"Ehh Ammee"
"Dafatan komi lapia de?!"
"Lapia Lou Ammee,bamuyi magana da baban bade may be se xuwa da safe"
"To baranem(barka de)Hydar, dafatan kaci abinci ?!"tace hakan with care saboda tasan halin kishiyoyin nata
"Ehh ammee munci da baba.."
"To shikenan Hydar kaje ka kwanta seda safe xamuyi magana"
"Okay Ammee Allah tashemu lapia.."
Katse wayan yai yakoma yakwanta akan gado had'e da lumshe idanuwansa,basma ce tafad'o masa arai,siririn tsaki yaja sanin alk'awarin dayai nakiranta, dialing number ta yai yasa a handsfree ringing d'aya be gama ba tad'auka sounding so happy tafara magana kafin ma ya kulata;
"Sugar boo... "Taja boo din cikin sigar soyayya
"Basma" shine abinda yace kawai
"Kaxo lapia sugar boo?! Yasu baaba?!"
"Komi qalau Alhamdulillah... It's kinda late here, so goodnyt"
"Sleep tight boo boo,I love you beyo...."bata k'arasaba ya katse kiran had'e da jan duvet yarufe kansa saboda sanyi dagarin yai dakuma sanyin split dake d'akin daya k'ara sanyaya d'akin.. Cikeda takaici da naci irin na basma haka bacci yad'aukeshi..
Da asubah yareemah Aliyu Hydar yatashi daga bacci band'aki yafad'a yayo wanka had'e dayin alwala,bud'e akwatinsa yai yaxaro jallabiya fara k'al yasaka yafita cikin d'akin parlorn daxe sadaka da qofar fita yaga yareema babagana akwance a rigingine hannunsa rik'e da kwalbar guiness wine da alama yasha ta'isheshi se surutai yake shi kad'ai kamr zaucacce,cikeda takaici yareemah Aliyu Hydaryad'an fara doka kujerar da yareemah babagana yake;
"Baa(Yaya)babss(Dayake haka sukece dashi),baa babss wake up, lokacin sallah yayi fa.."
Babagana cikin matogagin giyar dayasha yafara magana;
"Those boobs..inkaga yarinyar nan oh bouy kaya dey oooo..."babagana yafad'i hakan yana D'aga hannayensa sama yaname sake tuttulawa cikinsa giyar
Dogon tsaki yareema Aliyu Hydar yaja had'e da ficewarsa zuwa masallacin fadar,cikeda takaicin halin yareemah babagana ashe yananan da xuwa club d'insa da harkar mata, bayan sunyi sallar asubah and'an tab'a karatu yareemah Aliyu Hydar yaraka mai martaba zuwa sashensa dayake har gari yayi haske wajajen bakwai,sake gurfane yai ahankali cikeda ladabi yasake gaishe da mahaifin nasa cikin harshen barbarci/kanuri;
"Baba inda watu?"(Ina kwana baba?!)
"Kelewa selai,ka tashi lapia Hydar ?!"
"Eh babaa Alhamdulillah!"
"To Masha Allah, jeka samu bacci Hydar xuwa wayewar gari xamuyi magana da kai dalilin dayasa nasa aka d'akko ka daga makaranta...."
"Shikenan baaba,Allah ya kaymu anjiman"yafadi hakan cikeda ladabi da girmamawa
"Allah yamaka albarka Hydar"
"Ameen Ameen baba"sannan ya mik'e yatashi yafita..!
Cikeda so da k'auna mai martaba yabi d'ansa da kallo,hak'ik'a duk cikin y'ay'ansa babu wanda yake masa ladabi da biyayya irinsa,tattausan murmushi mai martaba yasaki ahankali yasake furta ;
"Allah yamaka albarka Hydar.....!"
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo:
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!

(A STUNNING LOVE STORY)
Chapter 2 · 0% Book details