Sashe 77
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
```Edited by```: ```Ya hajja ce``` _*wannan shafin sadaukarwa ne ga duk wani kanuri/barebari dake fad in k asar nan..Musanman yan yerwa fato..Nagaisheku Nagaishe ku dangin k amshi gaisuwa mai d imbin fatan alkhairai_ *71* *B*ilkisu na zuwa unguwarsu taga baki d'aya yanayin unguwar ya canza daga yadda tasanta,a k'ofar wani had'add'an gida mai matukar kyau jikin shi duk tiles nan taga driver d'in ya tsaya tare da fitowa da sauri ya b'ud'e mata murfin kofar yana cewa, Rankishi dad'e gamu munxo Allah ya k'ara miki lafiya. Jinta tayi wani gingirin ganin yadda yake tayi mata sannan yana nuna mata gidan a matsayin wanda zata shiga,sake kallon driven tayi sannan cikin tsoro tace, Dan Allah malam ina ne nan ka kawo ni?! Ranshi shi dad'e ai cewa akayi na kawoki gidan mahaifanki toh kuma gashi munzo Allah ya temakeki. Ya fad'a cikin gazgata mata abinda ya fad'a,sake kallon gidan tayi sannan ta girgiza kai alamar bata yadda ba ganin tak'i fitowa yasan kuma ba haka takeyi ba yasa shi k'arasawa cikin zauran gidan ya kwad'a sallama,Ummi ce kanwarta ta fito dan ganin wanene tana ganinshi da kayan sarauta ta durkusa har k'asa tana gaidashi ya amsa tare da cewa. Yauwa 'yan mata kinga ga yayarki bilkisu tak'i fitowa daga cikin mota ko zaki je idan ta ganki k'ila ta fito?! Ai da sauri Ummi tayi waje murfin motar a bud'e yake nan billy ta ganta tayi saurin fitowa da sauri suka rungumi juna cikin murna kafin Ummi taja hannunta suka shiga babu wanda yayi magana a cikin su dan tsabar murna sai da suka shiga cikin gidan. Umma ki fito ga Yaya Bilki tazo. Cewar Ummi cikin d'aga murya suka k'arasa cikin parlor suka zauna yayin da bilkisu keta faman kallon yanayin gidan tana mamakin yadda rana d'aya Allah kan sauya al'amura bata gama mamaki ba Umman su ta shigo parlon tana murmushi tace, Ke dai bilkisu bakya son zama duka-duka yaufa kwanaki uku kenan da kuka zo gidan nan amma yauma har kin kuma fitowa. Sakkowa billy tayi daga kan kujera ta fad'a jikin Ummanta tana kuka nan da nan hankalinta ya tashi ta kalli inda Ummi take tace, Tashi kije ki d'akko mata ruwa da abinci. Ummi ta tashi jiki a sanyaye yayinda billy ta maida hankalinta wajan mahaifiyarta cikin kuka take cewa, Umma ya cuceni ya b'atamin rayuwar da kuka dad'e kuna kula min da ita wallahi Umma ba laifina bane saceni yayi ya tafi dani masarautarsu ya aikata zina dani Umma ya b'ata rayuwata dama ace na mutu kar naga rayuwata ta gaba dan nasan sai tafi haka muni da wulakanta...!l Sai faman surutai takeyi daga gani hankalinta ne ya dawo dan haka Umma ta barta sai da tayi kukan sosai har ya haddasa mata da ciwon kai sannan Umma tace, Kiyi shiru Bilkisu kiyiwa Allah godiya daya dawo miki da tunaninki bayan kin kwashi tsawon shekaru sannan kiyi min bayanin shin waye kike maganar yayi miki duk wad'annan abubuwan...?! Umma waye kuka bashi aurena?! Tayi maganar hawaye na sake zubowa Umma ta rungumeta cikin sanyi jiki da tunani kala-kala tace mata. Bilkisu abin labarine mai tsowo a yanzu haka ked'in matar yareemah babagana ce ke.. Na shiga uku lallai sai yanzu na kara tabbatar da cewar wannan mutumin azzalumini macuci da besan hakkin d'an Adam ba,wallahi Umma shine ya cuceni ya b'ata min rayuwa bayan mahaifiyar shi ta goya mai baya shine ya lallabo kuka bashi aurena bayan kunsan ina cikin halin kunci da bakin ciki....?! Innalillahi wa'inna'ilaihir rajiun yanzu bilkisu kinason kicemin yareemah babagana shine yayi miki wannan aika-aikar?Lallai na yadda ba'a gane mutum a fuska sai an yi mu'amula dashi da zuciyar shi,amma yaron nan ya cika macuci a haka kamili kamar zai bauta mana ashe ashe sakayyar Allah ce ta fara riskarshi tun a nan duniya.. Anan bilkisu ta bawa su Umma labarin abinda ya faru har kawo yau data ganta tare dashi sannan itama Umma ta sanar mata iya abinda suka sani har yadda akayi auran da kuma yadda shi yareemah babagana ya gyara musu gidan ya zuba musu komai na rayuwar zamani sannan ta sanar da ita yadda sukaga yana tarairayarta kamar zai maida ita cikinsa sannan Umma ta k'arkare da cewar, Mu bari abbanku ya dawo yaji sannan kuma mujira hukuncin da sarki zai yanke domin idan kowa ya yarda ni kam bazan yadda ba sai na kwato miki hakkinki.. Wani sanyi ya ziyarci zuciyar Bilkisu ta kuma kwanciya jikin mahaifiyar tata tana fatan kar Allah ya kuma yin sanadin komawarta gurin babagana bata fatan hakan ta kasance koda kuwa zai mutu.har dare suna tare makota zai zuwa kwasar gaisuwa sukeyi har lokacin da Abba ya dawo shida yayunta nan suma sukaji duk abinda ya faru saidai tunanin Umma dana Abba ya ban-banta domin shi cewa yayi, Alhamdulillahi dole mu godewa Allah dan tun anan duniya ya saka miki bilkisu,da ace Allah yayi watsi dake da ko gaskiyar al'amari ya bayyana bilkisu bazamu iya ja da gidan sarauta ba dan da ace munsan gaskiyar tun a baya sai dai muyi Allah ya isa domin zuwa kai k'arar d'an sarki kotu ko police station abun akanmu zai kare dan kila idan shi ba'a d'aureshi ba Mu a kullemu kuma babu me fito damu sai yadda Allah yayi damu,amma kunga sanda abin ya faru sai Allah ya dasawa yaron soyayyarki mai zafin gaske ta yadda ya kasa sukuni har saida yaga ya mallakeki bayan da tuni ya lalata miki rayuwa kuma sannan ya barki da gorin duk wani namijin da zaki aura amma yanzu fa?asirinki a rufe namu arufe amma ni bazan goyi bayan ki kashe auranki ba sannan kuma nayi alkwarin bazan tilasta miki komawa ba dan ba abin hannunshi nakeso ba rufin asirin gidana da mutuncina nake so. Bilkisu najin haka ta kuma rushewa da kuka,Umma tace, A gaskiya ni banason ta kuma komawa wajan shi domin hatta mahaifiyar shi ba son auran takeyi ba kuma batada imani bare tausayi gara kawai a rabasu Allah ya had'a kowa da rabonsa. Gaskiya kam dan hakan ne zaisa ya gane cewar ba arzikinsa muke so ba. Cewar yayanta Bashir wato yana goyan bayan Umman tasu akan ra'ayinta,yayin da Abba yayi murmushi mai ciwo dan yasan shi abinda ya hango su duka basu hangoshi ba dan haka ya mik'e tsaye tare da cewa, Zan jira naji hukuncin da mahaifinshi zai zartar duk kuwa da cewar nasan shi besan da wannan abunba. Yana kaiwa nan ya fita cikin tsananin mamaki da alajabi sam be tab'a koda hasashen cewar wai babagana ne yayi wa gudan jininshi haka ba sai dai tunawa da yayi cewar ranar dubu ta b'arawo d'aya tal ta me kaya da wannan tunanin ya cigaba da harkokinshi yana son jin sakon kira daga gurin mai martaba maimurabus. *MEENAH S WEDDING EVENTS* Sosai ake shagalin biki sai dai yadda kukasan Modu ne angon dan dashi ake yin komai shi kuma sarki Aliyu hydar maimartaba maimurabus ya hanashi zuwa a cewar shi kar yaje dan kar asamu abin fad'a a cikin al'umma yace yayi zamanshi har a kawota d'akinta hakan yasa duk abubuwan da aka tsara 'yan uwa da abokan arzuk'ane keyin komai.A gurin bikin harda mahaifiyar Basmah domin tazo itama anan ne kuma ta kuma tabbatar da cewar babu wanda yasan rabuwar sarki Aliyu hydar da Basmah ta yadda taji kowa yana tambayarta wai ya karatun Basmah yashe zata dawo sai dai kawai tace musu tana can bata dawo ba da haka ta ja bakinta tayi shiru tana son idan komai ya lafa ta samu maimartaba maimurabus ta bashi hakuri kafin wa'adin iddar ta ya kare yasa ya maida ita. A b'angaran Aliyu hydar kuwa bini-bini ya kira Modu shi kuma sai ja masa rai yakeyi hakan take yanzu ma sai faman waya yakeyi mai amma sai da ta kusa tsinkewa sannan ya d'aga yana mai dariya yace, Guy wai meyasa sai faman takura min kakeyi ne ehyi?! Mtww duk kayi ka gama yanzu ina ita Meenahn take ina son inji muryarta please Yaya Muhammad. Wata mahaukaciyar dariya Modu yayi wadda tunda yake be tab'a bud'e ta haka ba jin Aliyu hydar har da ce mai Yaya,yanajin shi yayin da shima d'in yake zaune a bedroom yana murmushi shi kanshi daya fad'a sai da yaji banbarakwai amma ba yadda zaiyi dole ya lallab'a har ya samu ya had'ashi da Meenah sabida ya kira wayarta akashe ya kira gid'ad'o yace baya tare da ita ya nemi aunty yaruwaiya tace mishi tana gurin baba shida Mai Alooma tana had'a musu abinci hakan yasa dole ya kira Modu tunda ance suna tare da ita da layla da kiara da sauran wasu kawayanta abokai da yan uwa. Guy idan bazaka had'a muba sai na ajiye phone d'in kaji?! Idan ka ajiye anjima idan naga ana shirin kawo maka ita sai nace bakajin dad'i kace a bari sai gobe you know me zan iya tsab wallahi ka lallab'ani.... Ok ai ni dama yanzu nasan baka sona guy but kayi daga yaune zamu had'e kuma sai na rama. Dariya Modu yayi yana hangen Meenah dake zaune tana shan fresh milk sannan yace, Mr arrogant kasan dai yanzu baka da wani time na yin ramuwa sabida kullum kana fada amarcin ma ba barinka za'ayi ka more ba da anji kayi kwana biyu baka zuwa za'a fara yi maka fassara kala-kala. Ya k'arasa fad'a yana dariya, kin kula sarki Aliyu hydar yayi sannan Modu ya kira Meenah gefe ya bata wayar sannan ya matsa ya koma wajan matan shi domin sun had'e kai sosai suna kuma bashi kulawa ba kamar kiara da batajin kunyar kowa ko gaban waye idan ta ganshi sai ta sakar mai peck shine dai ake bari dajin kunya dan wani sa'in ji yake kamar ya nutse. Yah?! Cewar Meenah bayan ta kara wayar jikin kunnanta,yana jin muryarta ya sauke wani marayan numfashi sannan shima tace mata, You. Me! To fa What?!l Ina son kizo side d'ina ina son ganinki now kuma karki gayawa kowa kinji ni ko?! Kamar yana ganinta ta zaro idanuwa tare da dafe kirji sannan tace, Nazo fa kace?! Eh kuma yanzu. "Tab wallahi ni bazan iya zuwa ba gaskiya amma kai kazo mana. Ke!ni d'in kike cewa nazo bayan nine mijin ke kuma