Sashe 70
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rasu wallahi kinji na rantse?kema sai kin bishi idan yaso sai nima a kasheni... Fitowar likita ne yasa hajja gajiram yin shiru cikin tashin hankali take tambayar shi,kallonta likitan yayi kafin cikin girmamawa yace, Rankishi dad'e muna son ganin bilkisu a ciki saboda ya damu hakan yasa muka kasa gano menene ya samu cikin nashi da yake ta faman rik'ewa amma yaki bamu had'in kai shi kawai bilkisu yake son gani,muna da tabbacin idan aka kawo bilkisun zamu samu mu gano matsalar har ya bamu had'in kai,so yanzu a kirata idan kuma tayi nisa muna son a yi duk yadda za'ai muganta a wannan lokacin. Wata muguwar harara hajja gajiram ta sakarwa billy wadda ke tsaye jikinta sai kyarma yake yi,cikin takaici ta kalli likitan tare da cewa, Ai gata nan likita,wannan ce bilkisun ita ce ke neman rayuwar shi muguwa azzaluma kawai... Dr imran najin haka ya juya yana kallon bilkisu dake ta faman zubar da hawaye,a hankali ya furta. Madam muje ciki ko?! Yana gaba tana bayanshi kirjinta na bugawa tamkar zai tsage,suna shiga taga yareemah babagana a kwance rik'e da cikinsa yana ganinta ya mik'amata hannunshi alamun tazo gurinshi billy ta kalli likitan cikin tsananin tsoro dr imran ya d'aga Kai alamar taje,a hankali ta k'arasa gurinshi babagana yayi saurin rikota tare da matseta cikin jikinshi murya a wahale yake magana, Please my billy dan Allah karki gudu ki barni ina sonki ina matukar kaunarki idan kika gujeni zan iya rasa rayuwata,ki yafemin duk abinda nayi miki son zuciya ne da rud'un shaitan dan Allah... Shiru tayi jikinta nata faman rawa har dr imran ya kallesu cikin tausatawa duk da besan abinda ke tsakaninsu ba ya dai fahimci cewar ita bilkisu bata son shi shi kuma yareemah yana sonta so mai tsanani.tana zaune ya damk'i hannunta tamkar wani zai kwaceta a haka aka fara dubashi ita dai billy kad'an ne ya hanata sakin fitsari dan tsananin tsoro da tunanin abinda yasa taji anacewa matar shice ita. Sai da aka gama treatment d'inshi sannan dr imran ya kallesu yana dariya dan abun yanzu dariya yake bashi yace, Sir ya kakejin cikin naka yanzu?! Normal dr ni tun zuwan matata gurin naji banajin komai yanzu ma gida zamu wuce. Cewar yareemah babagana yana yi idanunshi cikin na billy wadda ketafaman kallon wani kwalin magani,dariya dr imran ya kumayi kafin ya k'arasa kan wani table yayi rubuce-rubuce jikin wani file sannan ya dawo yana cewa, Okk zaku iya tafiya dama rad'ad'in naushin cikinne yasa kayi ta rik'ewa but maganin da kasha yanzu zai temaka maka sosai Allah ya k'ara lafiya ya tsare gaba. Amin..! Yareemah babagana ya fad'a wanda har lokacin yana manne da jikin billy itako sam bata kallonshi wani tsanar shima taji saboda rik'etan da yakeyi, fatanta a yanzu kawai taje gida ta sanarwa da babanta cewar saceta yayi ya kuma yi mata fyade har yake ikirarin cewar ita matarshi ce. Mak'ale da juna suka fito cikin sauri hajja gajiram tayi gurinsu, kwace hannun babagana tayi daga na bilkisu ta juya tana zabga mata harara ta rikoshi tana shafar fuskarshi cikin kulawa, d'ayan hannun yasa ya kamo billy tare da sanyata cikin kafad'ar shi ya kalli hajja gajiram data bud'e baki yace, Please Mami wannan itace zuciyata,janyeta daga gareni tamkar kin ciremin raina ne so please ki kyaleta... Mamaki da tashin hankali suka dirarwa hajja gajiram tana k arin yin magana saigasu hajja yakolo da sarki maimurabus sun k'araso wajan,kallon hajja gajiram hajja yakolo tayi fuskarta cike da alamun tambayar ta yadda akayi har ta taho nan batare da tasani ba bayan tasan suna tare acan wajan jakadiya mangu.Ganin sarki maimurabus nayiwa babagana magana yasa hajja yakolo janyo hajja gajiram tana tambayarta abinda ya faru cikin takaici ta fara gaya mata. Yoo banda sarkin gida yaje ya sanar min ai da tuni yarinyar can ta kashemin babagana,ina fitowa daga d'akin da aka kwantar da jakadiya basai muka had'u da sarkin gida ba,nan yake gayamin cewar ai matar yareemah babagana ta yimai aika-aika gatacen ma shegen sarkin nan yace a kaita gida,ina zuwa kuwa naga zata shiga mota na dawo da shegiya,shine shi kuma yake neman nuna min ta fini a gurinshi harda cemin wai zuciyar shice ita... Ta k'arasa maganar cikin b'acin rai,ita kam hajja yakolo rasa abin cewa tayi dan tsananin mamaki tabbas ada sunayin nasara akan duk wani abu da suke kullawa amma yanzu komai warwarewa yake duk kuwa da iya uban kud'in da suke kashewa akan duk wani aiki da za'ayi musu.wani mugun tsoro ne ya fara shigarta dan tana tsoran kar asirinsu ya tono tasan abun bazai kare da jin dad'i ba gashi tana son mijinta dan sarki maimurabus namijine tamkar da dubu. Suna tsaye suka ga maimartaba yaja hannun babagana wanda ganin mahaifinshi be sa ya saki hannun bilkisu ba,tare suka wuce apartment d'inshi sannan suma hajja gajiram suka bishi suna tattauna yadda zasu bullowa alamarin. *_ADAMAWA YOLA_* Zaune suke suna hira suyi dariya suyi jimami kawai Meenah 'yan son girman suka zo mata ta kalli gid'ad'o tace, Gid'ad'o kasan dai yanzu ni ba sa'ar wasanka bace bako?! Kallonta yayi cikin tsananin mamaki ya fuskanci tunda tazo garin take nuna mishi wani girma da fifiko dan kawai anyi mata aure,shafa keya yayi yana kallonta kafin yace, Eh amma nima yanzu idan akayi min aure babu abinda bazan iya ba ciki kuwa harda zamantakewar aure.. Da sauri Meenah ta zaro idanuwa tana kallonshi jin abinda yace,kai ta kad'a tana kallon gefe a hankali takai bakinta saitin kunnan shi tace, Gid'ad'o dama kai d'an iskane?! A kufule cikin jin haushinta yace, A'a nafi karfin iska d'an guguwa ne ni kinji ko?! Uhmmm! Cewar Meenah jin abin ya girmeta ko yaushe gid'ad'o ya zama d'an iska bata saniba?daga yin tambaya shine zai bata wannan amsar dan ya rainata,da badan karya k'ara narko mata wata babbar kalmar ba data kuma gaya mai wata sai dai taga shi dinma kyar yake ba kamar daba. Meenata zo kiji muyi wani secret. Cewar aunty yaruwaiya data shigo yanzu kasance war sunsake dawowa ganin Meenan,mik'ewa Meenah tayi tana dungurin gid'ad'o lokacin da taje zata wuce ta gefenshi,yayi kwafa snannan ya d'auki remote control ya fara canza channel.Meenah na zuwa wajan aunty yaruwaiya ta kama hannunta tare da shiga cikin bedroom d'in da take,zama suka yi sannan aunty yaruwaiya tace, Meenah kinga dai ni ba sa'arki bace ba kuma k'awarki bace ba kuma kanwarki bace ni auntynki ce amma na ajiye komai ina koya miki surruka da dabaru na zama da miji wallahi idan kikayi wasarara sai dai kiji ance baah hydar zai k'ara aure ke kuma sai dai abarki da aure akanki keba mai aureba ke kuma ba budurwa ba kin zama huto dake da babu duk d'aya, Kinga yanzu dole ki koyi yadda zaki damki mijinki ya zamana babu ta yadda zai ga abin kushewa a jikinki,kisan yadda zaki iya jan hankalinshi ya zamto koda yana cikin fada a zaune tunaninki bazai gushe a cikin zuciyar shi ba,yanzu naji ance jibi zaki koma da kin koma za'ayi biki ki tare saiki dage karki tsaya jin kunya mijinki ne d'an uwanki kuma yayanki kin ganeko?! Ajiyar zuciya Meenah ta sauke cikin turo baki tace, Aunty yaruwaiya jibi fa naji kina cewa?ni wallahi ban gaji da nan ba shi kenan daga zuwana za'a wani ce na koma sai kace ba'a sona...?! Tayi maganar tana turo baki cikin shagwab'a wadda ta zama jikinta, kallonta aunty yaruwaiya tayi cike da so da shakuwa tace, Eh kinsan dai halin Baffa yace shi bega zaman da kikeyi anan ba gara ayi bikin ki tare yasan yayi miki aure." Kaji kajifa Baffa ni wallahi ban shirya komawa ba kawai a kaini wannan gundumemiyar matar tashi ta dinga zazzaro min idanuwa wallahi bana sonta saboda ta fiye sa idanuwa. Toh ya zakiyi Meenah tunda zaman tare ya had'aku?ni dai fatana karki wani tsaya yin banzan kishi na hauka,kiyi kishinki mai aji sannan ki kwato zuciyar mijinki ya zamto kece a cikin zuciyar shi kin gane ko?! Eh.. Kawai Meenah ta fad'a amma iya kufula ta kufula dan batason komawa saboda ko gidajen kawayanta bataje bare a kaiga na yayunta amma Baffa yace ta koma shawarwari masu muhimmanci aunty yaruwaiya ta bawa Meenah wanda idan har tayi amfani dashi zataji dad'i zakuma mata amfani aduk inda ta samu rayuwarta. A cikin kwanakin da suka ragewa Meenah aunty yafendo ta fara tsumata gaba d'aya sun tasata a gaba aunty Maijidda nayi aunty yafendo nayi aunty yaruwaiya nayi gabaki d'aya Meenah ta sauya ta k'ara haske fatarta sai faman walwali da shek'i takeyi,jikin yayi luwai-luwai ita kanta Meenah jin dad'in tab'a fatarta takeyi dan tsabar taushin da ta kuma yi ga kamshin da ya kame jikinta ko bata saka kayaba haka zakaji jikinta nata tashin kamshi. i gobe Meenah zata koma duk suna zaune a katafaran parlorn Mai Alooma Ghaji kamar wasa Meenah ta tashi tare da cewa, Excuse me. Fita tayi tayi hanyar apartment d'in aunty yafendo dan d'akko wayarta tana son kiran su Ammi,tana yin kwana kawai taji anyi sama da ita ta bayanta nan da nan ta fara ihu tana shure-shuren sauketa amma ina saida aka danganata da cikin d'aki sannan taji an matseta ana shinshinar wuyanta,kyarma jikinta ya farayi hawaye kuwa tuni suka cika mata kunci yayinda kirjinta ya tsananta bugawa tamkar zuciyarta zata fito.A hankali kuma taji an sakala hannu cikin saman kirjinta an d'ora da alama sonjin yadda yake bugawa za'aji ita kam ta rintsa idanuwa jira kawai takeyi taji meza'ayi mata. My sweet wife. Taji muryar sarki Aliyu hydar sassanya mai dad'i ta daki dodan kunnanta Meenah tayi saurin juyowa cikin tsananin mamaki take kallonshi shi kuma ya rungumeta yana sake zura hannunshi cikin rigarta saurin turewa tayi tana turo mai baki cikin shagwab'a tace mishi. Kai!Ya Aliyu ni wallahi kabani tsoro na d'auka walakiri ne yadda naji ana neman d'aukar raina.. Uhmm My Meenah walakirifa kikace.. Toh ai kaine ka bani tsoro ni banma san na fad'a ba yaushe kaxo ya Aliyu?! Yanzu kuma bazan tafiba sai dake domin ina son ganinki a kusa dani,ace sarki guda amma ba shida mata. Nifa sai nan da 3weeks zan koma dan wallahi ban gaji da nan ba. Murmushi yayi wanda ya k'ara kawata fuskarshi sannan