← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 107

Sashe 13

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
_18_
Wannan shafin nakune Ammunah and Nusy from MU SHAA KARATU grp
da duk ma members na cikin grp d'in..nagaisheku kyauta
......
Modu indimi nasauke Kiara a gidansu yaja motar da k'arfi yai apartment d'in ma'aruf yana parking motar ya kife kansa akan sitiyarin fara tariyo abubuwan dasuka faru d'axu yafarayi yajima yana recalling abubuwan har seda ma'aruf yai knocking glass d'in k'ofar motar hangensa dayai tundaxu yadawo beji shigowarsa cikin gidan ba yasashi dubawa yaga ko lapia??button Modu yadanna yabud'e glass d'in k'ofar ma'aruf ya lek'o da kansa taciki yana masa magana;
"Aboki lapiar ka kuwa kusan k'arin awa d'aya kaifa acikin motar nan kome kake oho thought ko rik'ewa motar tayi don tasaba haka ina fatan lapia de ko?!"
"A.. Aboki la...lapiya yanzu dama xanshigo"Modu yabashi amsa muryarsa na d'an karkarwa
"Okay muje ciko to"ma'aruf yace hakan asanyaye yanabin fuskarsa da kallo
Fitowa Modun yai daga cikin motar ya k'ulle tareda bawa ma'aruf muk'ullin ahankali yace;
"Thank you.."
"Aboki meyake faruwa ne??kalli idanuwanka yadda sukai ja dan Allah menene yake damunka"cewar ma'aruf daya k'arasa xancen yanabin idanuwan Modun da suka kad'a sukai jajir da kallo..
"Nothing fa,kawai allergy ne kasan m allergic to butter cream cake shine kuma naci bada saninaba..."
Tab'e baki kawai ma'aruf yayi saboda yasan bahaka aininhin xancen yakeba shiga cikin apartment d'in sukai atare,ma'aruf yahaye kan kujera yaciga da kallon shirin 'greys anatomy'da ake a tv shikuma Modu yahau stairs yashige d'aki a bakin gado yaxauna yafara tunani da xancen filin daya saba shi kad'ai;
"Kona kira Layla nace nagansu da Basma a clubbing yau?! Kai a'a kuma idan nafad'i haka xasu gano akwai wata a k'asa... God damn it niyanxu yaxanyi?!" Yafad'i hakan yana sakin siririn tsaki
Ganin xancen nasa bana k'are bane yasanyashi tashi yashiga band'aki wanka yayi had'e da d'auro alwala yafito pajamas yaxura yahaye kan gado wayarsa yad'akko yai dialing number yareemah Aliyu Hydar ringing d'aya biyu ya d'auka;
"Hello....The charming prince yakake?!"cewar modu indimi
"Lapia Lou oga at the top"yareemah Aliyu Hydar yabashi amsa...
"Waneni wannan aise ku manya manya..."
Daria kawai yareemah Aliyu Hydar yai bebashi amsa ba.
"To ya gidah da kowa?! Yaya jikin baa Ngari??"
"Alhamdulillah..."yareemah Aliyu Hydar yabashi amsa a tak'aice
"To Masha Allah.. When are you coming back ne?!"cewar modun
"Idk guy.. Ina jiran baba haryanxu de.."
"Yeah correct..To Allah yasa muji alkhairi"
"Amiin.. Ya kagama compiling project d'innaka?!"
Sosai kai modu yai yana tunanin k'aryar daxe masa can yace;
"Bank'arasaba de bibliography kawai nake correcting wajen in-text referencing d'innan.."
"Oh okay..."
"Yup amma nakusa k'arasawa..."
"Congrats..."yareemah Aliyu Hydar yabashi amsa
"Ina Basma?! Nasan kananan kana mata wulaqancin daka saba"
"Sure.."cewar Aliyun
"To Allah yabaka lapia guy..Barin k'yaleka haka nasan ka matsu nakashe"
"You are sick.."cewar Aliyun
Daria Modu indimi yai san ransa sannan yace;
"Okay good night mr arrogant..."
"Ok night.."cewar Aliyun....
Modu indimi nakatse wayar yajefar da ita agefe kwanciya yai kansa asama yana tunanin mafita harde bacci b'arawo yasa ceshi...
WASHEGARI;
Da sassafe modu indimi yatashi daga bacci yafad'a band'aki yayo wanka kayansa yaxura yafeshe jikinsa da turaruka yanupi dinning area inda ma'aruf ke having breakfast jan kujera yai yaxauna bayan yabashi hannu sun gaysa,
"Aboki se ina haka?! Wannan sammako haka ko yau xaka koma ne??"Ma'aruf yace hakan yana sipping black tea d'insa
"No zanje school ne gurin project supervisor d'ina amma xandawo da rana kamar yadda kace d'in inaso na had'u da Arfat"
"Oh baka gama ba haryanxu?!Allah yatemaka to,karde kajima kasa yarinyar mutane jiranka"
"Nagama fa.Zanyi submitting ne kuma inason ganin supervisor d'in nawa shysa,nd Insha Allah da wuri zandawo"
"To Allah yasa..."
"Ameen"Modun yace
Had'e da jawo plate yashiga serving kansa da roasted egg,French sandwich se coffee yana gamaci yaiwa ma'aruf sallama yatafi Cambridge university makarantarsu.....
_19_
Wannan shafin nakine ~Kherdejerh
and the entire members of RANO ONLINE NOVELS nagaisheku gaisuwa mai yawa
.........
Bornu_Maiduguri_
Shehuri(Masarautar sarkin Bornu)
"yanxu yayya kina ganin hakan shine mafita?!"cewar yakolo dake maganar tana kallon gajiram jiran amsar daxatace
"Hakan shine mafita yakolo,saboda Idan muka nuna zalamarmu a fili ina tabbatar maki da cewa mai martaba baxe k'ara yarda da muba..."
Ajiyar zuciya yakolo tai tana k'wafa,murmushin dayafi kuka ciwo gajiram tai a hankali tace;
"Duk yadda kikakai ga k'ololuwar tsana akan shegiyar matarcen mekama da aljanu itada y'ayanta ina tabbatar maki da cewa yadda natsanesu yafi ga tunanin bil adama natsanesu natsani duk wani wanda xeso su nak'i jinin me furta kalmar data shafi sunansu banasansu banason cigabansu kwata kwata saboda haka inason ki kwantar da halinki kibada had'in kannan ninasan aikin boka na sambisa xeyi kamar yadda yace d'in,karki manta bayau yasaba mana aiki ba ko kinmanta??"
"A'a yayya banmantaba"
"To ki...."
Bata k'arasa xancen ba yareemah babagana yaturo k'ofar da k'arfi yashigo yana tafe yana tangad'i kamar ze fad'a akansu cikin muryar maye yasa yatsa yana nuna gajiram mahaifiyarsa yana magana yana layi;
"Saboda tsabar renin sence na....nace kibani huge amount of money xaki rubuta wani shir..shirmen check wal.. Wallahi se...sekin ba...bani su ko..kokuma naje nad'uka da kaina ainasan inda kike ajiyesu bayan kema.. Sa..satowa baba ku..kukeyi ko angaya mik... "Bek'arasaba hajia gajiram tamike tsaye ta kama kafad'unsa ta xaunar dashi
"Haba yareemah haba sarkin gobe haba maxan fama karka manta fa sarautar bornu takace se yadda kai da ita idan kahau karagar mulki,inde kud'ine karka damu xan k'aramaka kaji??"cewar gajiram data karairaya murya tanawa babagana kirari...
"Naji..."cewar babagana
daya mik'e yafice yana tangad'in giya
Uban tagumi gajiram taxabga,yakolo ce tadawo kusa da ita tana bata baki;
"Haba yayya karkice xaki dingasawa kanki damuwa dayawa ,komai ze wuce kamar yadda bokan sambisa yai alk'awari.."
"Hakane kuma..."cewar gajiram
Sun jima suna tattauna yadda xasu k'ara b'ullowa al'amarin sannan yakolo tai mata sallama takoma sashenta itada kuyangunta dake take mata baya,hajia gajiram nakishin gid'e bayan fitar yakolo 'Ayiya'yarta k'arama kuma auta acikin y'ay'anta baxata wuce shekara goma sha takwas a duniya ba tafito sanye cikin doguwar rigar da akayi shaping d'inta takoma fitted gown kanta yane da mayafi kalar rigar hannunta d'auke da muk'ullin mota da alama fita xatai cikin hanxari hajia gajiram ta mik'e tana binta da kallo cikin kanuri tace;
"Ayiya ndararo len3min?!(Ina xakije Ayiya?)"
Batare da Ayiya tadubi gajiram batace;
"Lakkaro leyin(Wani wuri xani)?"cewar Ayiya
"Shi gurin bashida suna?!"gajiram ta tambayeta
"Kai yayya nifa gaskia kina b'atamin lokaci must u knw all my whereabouts??ha'a"
Batajira cewar gajiram ba tai ficewarta waje k'wafa kawai gajiram tai had'e da komawa tai kwanciyarta ..
(k'alubale gareku iyaye mata yakamata ku k'ara sanya ido akan y'ay'ayenku musanmanma y'ay'aye mata sakaci da barin y'arki taita karakaina a yawon zuwa gidan k'awaye da sauransu bai kamataba ki kula sosai ta fannin k'awayen datake mu'amala da su wayar hannunta da sauransu... And to the bourgeoisies(masu kud'i)dake barin y'ay'anku suna driving luxurious motoci akan titi suna yawon bin joints da sunan wayewa wannan 20th century ne.uwargidah dan maman neelam tabawa neelam mota karkice kema sekin bawa y'arki mota taje duk inda taga dama hakan daga k'arshe shike janyo nadama da danasani alokacin da kuma babu wata hanyar da xa'abi iyaye ku farga ku kula da y'ay'ayenku domin kiwone Allah ubangiji SWA yabaku kuma dole yatambayeku abisa abinda yabaku kiyo,bance duka aka taru aka xama d'aya ba,aka sari abinda ke faruwa awannen k'arnin kenan,gashinan rashin tarbiyya yana dad'a k'aruwa shikuma aure yana k'aranci,da anyi tambaya yan unguwa xasu soke xance saboda yar gidan wance bataji,shaye shaye take,da yawon banxa ko kuwa yar lez ce..Which s true...Dan Allah mu kula da y'ay'anmu musanman mata dama harkokinsu nayau da kullum...!)
......
University of Oxford(United Kingdom)
"Babe jia kin birgeni fa,haka nakeso kidinga enjoying life d'inki"Layla taceda basma hakan
"Da nayi me?"tabata amsa tana k'arasa drying kanta da hand dryer
"Da kika dumurmushi kud'in Harrison mana"
"Oh.. Kema aikin dumamusa naki Peter yake kowa?shegiya mak'aryaciya hardasu cewa da saurayinki acan ashe k'aryane"
Daria Layla ta bushe da ita sedatai me isarta sannan tace;
"To ke aganinki waye saurayin?! Oud de besan wannan wajen ba tunda shi ba'anan yakeba,kuma yama xa'ai mufita da wannan outfit d'in tare dashi?haba nace miki da saurayina ne kawai dan kije,gashi kuma kinsamu lucky day harda sabon iPhone 7 gaskia ba'indiyannan ya mutu akanki dagaske sonki yake da aure k'awata"
Tsaki Basma tasaki tareda kashe socket d'in dryer hannunta ta d'ora d'ankwali akanta sannan tawani sha kunu tana kallon Layla dake jiran dabata amsa a tak'aice ta furta;
"Sede ya mutu wallahi,jikina da ruhina mallakar Aliyu ne seyanda yai dashi"
Tak'arashe xancen tareda shigewarta band'aki bata jira cewar Laylan ba,itama Laylan tsakin tasaki tana mitarta ita kad'ai;
"Seki jirashi ai banxa yanacan ya mance da ke da rayuwarki kinanan kina ihu bayan hari ga inda xaki dandali arziki ana kaiki kinak'i.."
Mtcew tak'ara sakin tsaki akaro na uku had'e da jawo wayarta tashiga daddannawa rai b'ace
.......
Caribbean Mart.....
"Yi haku'ri Arfat nak'ara five minutes late"
Cewar Modu indimi dakebin wata matashiyar budurwa da kallo looking so modesty yar kyakkyawa bak'a tayi lullub'i da mayafi kalar kaftan d'in jikinta da alama itace Arfatun ahnakali tace;
"Apology is accepted"cewar Arfat
Gyara xama modu yai bayan sungaysa yashiga fad'a mata abinda yasa yace tatemaka masa da sunayen matan ajinsu,yak'arashe zancen da;
"Inaso kifad'amin abinda kika sani akansu,I want nothing but to the truth plss"
Nande itama Arfat d'in tafad'i duk abinda tasani akansu Laylan tak'arashe xancen da;
"Even though ba wata mu'amala ce ke shiga tsakaninmu ba psychologically de is lyk Laylan itake influencing ra'ayin Basman,nasan duka basaji gaskia at all Amma laylan tafi Basman saboda maxa kala kala take tarawa abakin block na apartment d'insu wannan shine abinda nasani tsakanina da Allah.."
Godia sosai Modu indimi yaiwa Arfat yakuma gamsu sosai da abinda tafad'a don from her decent looks ansan bazataiwa wani k'azafi ba,ma'aruf suka kira yadawo don dama waje yabasu abinci me rai da lapia modun yasa aka kawo masu sukaci suka k'oshi sannan suka sauke Arfat a campus library bayan Modu indimi yacikata da alheri,gida suka nupa bayan yayi sallar magrib ne modun yasake fita wurin wani abokinsa dake final year d'insa shima a Oxford d'in dayake expert ne na b'angaren mata,Modu naxuwa yasake tambayarsa akan halin su Basman,shima same abinda Arfat tace haka yafad'a..Godia Modu yaiwa abokin nasa sannan yakoma gidah a daren yakira mai martaba kasancewar lokacin yammacine a Nigeria,ringing biyu mai martaba yad'auka nan Modu yake gayamasa yagama binciken daya sashi a nutse mai martaba ya furta;
"Nagode k'warai Modu,Allah yamaka albarka.Da sassafe xan aiko da flight amma ba a bornu xaku sauka ba kaje gidana na Abuja nima xanzo akwai meeting da xamuyi da shugaban k'asa da sauran sarakuna,bayan mungama Insha Allah xamu tattauna acan dakai .."Cewar mai martaba daya k'arashe xancen cikin dattako da sanin yakamata...
"To baba Allah yakymu goben,ahuta lapia"
Sallama sukai da mai martaban ahankali Modu yajanyo pillow ya kwanta yana tunanin yadda xata kaya goben.....
Team#SRKZI?lovers
Ina kike sis Nobeey?
nagaisheki sis Nobeey crush d'in Modu indimi
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo:
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!
Chapter 13 · 0% Book details