← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 107

Sashe 106

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kuka tare da ruko Aliyu hydar wanda jikinshi yayi sanyi ganin yadda take kuka tace. Yaya ka yafemin kasan ance idan mutum zai haihu k'afarshi d'aya a duniya d'aya a lahira take,ni dai na yafe maka kace masu aunty Yafeendo su yafe min dasu Ammi da... Yareemah Aliyu hydar yayi saurin toshe mata baki yana girgiza mata kai zuciyar shi na bugawa yasa tattausan hannunshi yana share mata hawayen dake zirarowa a fuskarta yace. Ya isa haka Ajlal duk wannan abun ba zaisa ace mutum ya mutu ba, idan kika duba layla ta haihu gata nan da d'anta Bilkisu ma biyu ta haifa kuma duk suna nan da rai, ga Aisha (kiara) ma ta haihu lafiya kema insha Allahu Ajlal lafiya kalau zaki haihu kinji kiyi ta addu'a kina innalillahi wa inna ilahirr rajiun kinji?! Shiru kawai tayi mai ba tare da tace komai ba dan hankalinta a mugun tashe yake,nurses ne suka zo suka janye gadon Aliyu hydar ya bisu suna zuwa labour room aka dakatar dashi suka shiga da ita tana ta kiran sunan shi ya tsaya a bakin k'ofar hankalinshi a tashe yanajin tamkar ya rushe da kuka. Yana tsaye a reception sai faman addu'a yake mata sai ga kiran Basmah, da kyar ya zaro wayar daga aljihunshi ya kara akunne yaji Basmah na tambayar suna ina. Hospital.. Haka kawai ya iya ce mata cikin tashin hankali tace, Aminatu ce zata haihu?! Ya sake fad'a daga haka ya ajiye wayan Basmah najin haka itama ta taho bayan ta bugawa layla waya ta gaya mata. Basmah na shiga dai-dai lokacin aka fitowa da Aliyu hydar baby d'inshi a cikin shawol nurse ta mik'e mai tana fad'in, Congratulations sir. Kan na k'asa yayi saurin d'agowa yana bin hannun nurse d'in da kallo baki bud'e ya kasa karb'a sai Basmah ce ta k'araso da sauri ta k'arb'i boy d'in, kallon nurse d'in yayi yana kallon k'ofar d'akin da Meenah ke ciki kamar ta gano abinda yake son tambaya tayi murmushi tace, "Don't worry sir your wife is fine and she says to give you this.. Karbar farar paper hannunta yai yana dubawa Thanks nd by the way I hate you .. shine sakon da Meenah ta rubuto a bashi.. Sai a lokacin Aliyu hydar yayi murmushi dan ya gano ma anar sakon Meenah ya juya yana kallon jaririn dake hannun Basmah yana cewa,. Tell her I love her beyond her wildest expectations.. Jin ya amsa yasa nurse d'in juyawa ta koma room d'in tana dariya da murnar an gane sakonta. Sai da aka gyara Meenah sannan aka basu damar shiga bayan an maida ita wani gadon... a Allah ya zubawa yaron Meenah kyau sede ace tubarkAllah kawai domin har kyauta asibitin suka basu kancewar anjima ba a haifi kyakkyawan jinjiri irin sa ba,sosai yake yanayi da Aliyu Hydar sede sumar kan sa ta Meenah ce hade da yanayin manyan idanunsa duk na Meenan ne, Yareemah Aliyu Hydar yad au son duniya ya dorawa babyn har d an haushi mutuniyar taku takeji don gab anci,jirgi biyu yan uwa da abokanan arziki sukai zuwa kasar France don halartar sunan baby boy, Ranar suna yaro yaci sunan Mai Alooma Ghaji wato baby Alooma Aliyu Hydar SB domin bai manta halaccin da baffan nasa yai masa a duniya ba shine yai ruwa yai tsaki akan auren sa kuma ta tsatsonsa ne ya hadu da abokiyar rayuwar sa wato Meenah wadda takasance zabin iyayensa abun alfaharinsa,Sultan shine sunan da xa a dinga kiran babyn dashi anci ansha an wataya an kuma aje record don duk wata kafar yada labarai ta media xancen sunan baby sultan akeyi don harta sarki Ngari Shehu sedaya halarta shida gimbiya Asmy wanda ke kunshe da nata cikin.. Baby sultan yanashan dawainiya awajen mahaifinsa da kuma Basma wadda takejinsa har magudanar jinin ta don kusan kullum yana wajenta se xesha mama tukun sannan take maidashi wajen Meenan... Se bayan sati biyu cif sannan Basma takoma England cike da kewar baby Sultan,Aunty yaruwaiya itace ke xaune da Meenan har se Meenan tacika kwanaki arbain sannan xata koma Sosai take yi mata duk wata kulawa da ya kamata abawa mai jego ga gyara na musanman da ake mata ciki harda gyaren jiki kamar wata sabuwar amarya daka rabeta xakaji kaima ka kamu da kamshin.. Yareemah Aliyu Hydar kuwa hak uri kawai yakeyi domin yana azabtuwa rashin kusantar Meenah daya rabeta xe rage xafi aunty yaruwaiya xata fitittikeshi dolensa ya fice yana gunguni shiya fara jin haushintama Allah Allah yake kwanakin su kare ta tattara tatafi tabarsu,don takaici ma London yatafi wajen Modu nan yai weekend d insa ranar litinin da safe suna having breakfast Aliyu se tsaki yakeja ba kakkautawa takaici ya ishi Modu kamar ya tashi yarufeshi da duka a kafule ya dubeshi yana harararsa, Kaga pls niba tsaka ba ne,ka cikawa mutane kunne da tsakinka na gaira babu dalilii Mtcew shima yaja tsakin cikeda takaici, Guy aunty yaruwaiya is getting on my nerves ta hanani na.. sekuma yai shiru yana girgixa kai kawai Tuntsirewa da daria Modu yai hardasu rik e ciki yana magana yana cigaba da dariar, Tayimun dede tunda kaidin mutumin banxa ne Cikeda takaici Aliyu yai murmushin gefan baki, How I wished Meenah bata wani jinin bik i kai kaga yanda takara kyau kuwa sam bana controlling kaina idan Ina tare da ita,Ita kuma annoying aunty yaruwaiya nan dede da minti d aya bata barinmu idanunta k yar akaina wallahi ko kunya bataji haba ni banmasan meyasa akace itace xata xauna da mu ba wallahi,duk ga tsofaffi nan amma arasa wanda xa a bari se ita cewar Aliyu Hydar cikeda takaici, Daga kafada Modu yai alamar ko ajikinsa dinnan hade da daukar cup din tea d insa yashiga sipping hankalinsa kwance seda yashanye tea d insa tsaf sannan yadubi Aliyu Hydar dake faman karkada kafafunsa kaida kaganshi kasan yana cikin damuwa, Allah sarki aunty yaruwaiya guy baruwan aunty aciki wallahi believe you me tsabar nacin abun kasa aranka kawai,banda kai da abunka ma ai gata ake maka m sure gyaren da ake mata don kai akeyi mutumina karuwar kace kuma ma ai ba ita kadaice matar kaba akwai uwargidah Basma kuma tana garin nan.. Shiru Aliyu Hydar yai kawai batare da yabashi amsa ba jin shirun yayi yawa ne yasanya Modu mikewa tsaye yana kallon agogonsa sekuma ya saki murmushi cikeda tsokana yadan bugi gefan inda Aliyu yake xaune, Toh Guy barinje gidah wajen Aisha mu gwangwaji amarci later on naje wajen my layla itama mu kashe arna abinde se sam barka kawai mutumi na Tsaki Aliyu Hydar ya saki sannan ya mike yai tafiyar sa don sosai Modun ya kular dashi nan yabar Modu tsaye yana kwasar daria yasan ko banxa ya kular dashi.... Seda aunty yaruwaiya tai kwanaki hamsin cif sannan takoma Bornu,ranar Aliyu don dadi har zuba ruwa yai akan marbles yasha,a daren nan Meenah ta gane kuranta don bai mata adadi ba se gaf da subhi ya kyaleta shima baby sultan ne yaceci mamansa da kukan yunwar abashi mama, Watan baby sultan uku su Aliyu suka dawo Bornu banda Basma da bata kammala hada masters d inta ba Meenah an sake xama y ar gayu ga iya kwalliya da kissa,satinsu uku suna xaga dangi ciki hardasu ziyarar Hajja gajiram da aka maida ita gombole gidan iyayenta donsu kula da ita,yakolo kuwa ba gani ga kuma paralysis amma Alhamdulillah takan godewa rabbi ahalin da take don tana samun kulawa dede gwargwado wajen mijin nata dakuma su Ammi don sam basa kyamatarta kome yi mata suke tunda batashi take yiba, A daddafe Aliyu ya k arasa yin wata d aya a Bornu daganan suka tattara suka koma Abuja unguwar wuse 2 ademola adetokunbo kusada Rock view hotel dan datsetsan duplex ginin macce d aya nanne gidan da Meenan xata xauna while wani gidan benan a unguwar maitama ganges street nanne ya ajiye amatsayin na Basma wadda xata tare idan ta kammala masters d inta tadawo, Satinsu d aya agarin Aliyu yaiwa Meenah da Affy registration na Baze university domin shehu Bulama ne ya bukaci hakan kancewar duk wani Online school dasu Meenan xasu yi shirmene gwara suyi makaranta sosai Petrochemical engineering shine course din da Affy xatai Ita kuma Meenah tasamu Medicine,successfully suke karatunsu babu wata matsala, <><><><> Ya Aliyu ka kyaleni pls cewar Meenah dake turo masa baki gaba Xaune suke akan kujera mecin mutum biyu Rabin jikin Meenan a kan Aliyu yake se yamutsa ta yake son ransa yana wani lumshe ido cikin wata irin murya yace, Pls kibari na kara kinga gobe xan tafi Bornu Bata ce masa komai ba tade saki jikinta kawai nan yagane ta amince aikwa awajen komai ya kwana kukan sultan ne yasanya aliyu kyaleta tabashi mama sannan suka tsarkaka jikinsu ya jasu sallah uku nayi ya saukesu itada Affy a sch wadda tadawo gidan itama saboda school daki d aya Aliyun ya gyare mata take xaune aciki, <><><><><> Months later, Sosai garin bornu suke alfahari da mulkin sarki Uthman Ngari,mutum ne shi me gaskiya da son gaskiya baya wasa da duk wani hakkin wanda yake k'ark'ashin shi hakan ya k'ara kwantar da hankalin maimurabus. Sarki Uthman Ngari yana zaune a cikin fada ya gama solving wani case na mata da miji aka aiko mai cewar uwar gida na asibiti, duk da cewar zuciyar shi na son zuwa wajan nata sai dai yak'i tashi saboda kunya yana daga zaunan ya dinga yi mata addu'a da fatan Allah ya sauketa lafiya aikuwa ko mintuna 30 ba'ayi ba aka sake zuwa aka ce mishi ta haihu ta samu baby boy itama a nan ne ya tashi aka rakashi zuwa asibitin dan gano lafiyar su. Anyi murna sosai musamman Ammi tayi farin cikin ganin tsatson Ngari dan basu rab'a zaton zai tashi ba bare har yayi aure tayi murna har ta kasa boyewa sai da mutane suka gano, anyi suna yaro yaci sunan Muhammad cewar sarki Ngari albarkacin mai sunan yana kuma fatan yayiwa addinin musulunci hidima,su Meenah ana exam sai pic's ta gani tana tajin haushi akayi taro lafiya aka gama lafiya. Bayan suna da wata d'aya aka yi bikin Falmata kasan cewar ta samu wani mijin hamshak'in d'an kasuwa ne yace yaji ya gani zaiyi shahada zai aureta sai
Chapter 106 · 0% Book details