Sashe 88
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*74* *S*ake gurfane Mangu tai cikeda nutsuwa tafara magana kanta a k asa, Hak'ik'a rankishi dad'e manzon Allah (SAW)yayi gaskiya da yace mai hakuri yana tare da nasara hakurinki yayiwa wad'anda basu dashi mugun ciwo ne domin har kullum dai kece a saman su duk kuwa ta inda aka bullo miki.Nikam naga ishara koda na sanar miki yanzu nasan an cuceki a baya sai dai nasan ked'in mai afuwace dan Allah rankishi dad'e ki gafarce ni,wallahi duk wani tuggun da ake shirya miki tun daga kanki har zuwa 'ya'yanki rashin lafiyar yareemah Ngari wallahi duk sihiri ne wanda ni suke aikawa wajan k'arb'o musu shi. Jakadiya Mangu ta rushe musu da kuka Ammi ta bita da kallo cikin tsananin mamaki,cikin masifa aunty yaruwaiya tace, Suk'e turaki ki k'arb'o su suwa ye?! Hawaye basu bar zubowa daga fuskar jakadiya Mangu ba jikinta sai b'ari yake tace musu. Su...su...su abokan zaman nata wallahi su Kansu a had'e yake duk tare suke yin komai sai dai a baya komai sukayi boka yana basu sa'a sab'anin yanzu da duk abinda suka b ullo miki da shi rankishi dad'e baya faruwa a kanki sai ya koma kansu musamman ma ita wadda take sawa ayin wato hajja..hajja mahaifiyar yareemah babagana,sam bata kaunar taga kin cigaba dake da 'ya'yanki da duk wani wanda ya rab'eki dan Allah rankishi dad'e kiyi min afuwa kinga nima tsautsayin daya afka min duk ta sanadiyar zuwa k'arb'o abinda za'a cutar daku ne, Wallahi Allah hajiya hatta rashin samun haihuwar matar maimartaba na yanzu wato maryamu da batayi ba duk makircin sune da suka dinga d'orata akai na cewar zata mallaki mijinta zai sota kamar babu wata d'iya mace a duniya ita kuma da yake yarinya ce sai ta yadda har suka illatata amma wallahi rankishi dad'e itama ba laifinta bane duk makircin sune akwai abubuwa da dama rankishi dad'e wanda ake ta shirya muku wani ma bakina bazai iya fad'ar shiba sai dai nace kiyi hakuri ki gafarta min gashi ban karu dasu da komai ba sai asarar sashen jikina da nayi. Jikin aunty yaruwaiya har kyarma yake yi saboda tsabar kid'ima bakinta sai motsi yake da alama rashin mutunci take son yiwa jakadiya amma idon Ammi ya hanata dan tasan da ta fara zata katseta, duk gurin babu wanda be shiga cikin tashin hankali ba dajin wannan bayani na jakadiya sab'anin Ammi da take ta sakin murmushi wanda duk cikinsu babu wanda ya gane kona meye.kallon jakadiya Mungu Ammi tayi cikin jin dad'i da nuna kamar babu abinda taji tace mata. Toh sai muyiwa Allah godiya daya sa kika gane cewar abinda kuka aikata ba dai-dai bane Alhamdulillahi kuma na yafe miki jakadiya duniya da lahira har dasu d'inma duk na yafe muku,Allah ya ganar dasu suma su gane cewar Allah shine kadiran alaman yasha,duk mulkinka duk matsayinka duk tarin dukiyarka indai har baka sa Allah a cikin lamarinka ba toh ka tab'e tun anan duniya na kuma k'ara yadda da lamarin ubangiji domin dashi na dogara yau gashi ba wani takura muku akayi ba a'a da kankin kanku kuka fallasa abinda kuka b'oye Allah ya shirye mu ya shiryi duk wani musulmi dake fad'in duniyar nan. Amin Ammi. Cewar Aysa yayin da Yaya gumsu tayi caraf tace.. Wallahi basu isaba kanbala'in can!yo ai dama da walakin goro a miya dama sai da nace abincika matan nan amma k'iri-k'iri aka wani ce zato zunubi toh wallahi sai sunyi zaman gidan yari,muza'a wulakanta kema munafuka ba ciwon kafa ba ko ciwon me kikeyi wallahi sai kin k'arbi hukunci tunda kece munafukar,bulalai da xaman gidan kaso shiya kaman ce ku Yi shiru haka gamsu,ni aka yiwa kuma nace na yafe ba shikenan ba,a koda yaushe ana son mutum ya kasan ce mai afuwa da yafiya Allah yana son mai yawan yafiya kuma kuyi hakuri kunji ko banasan ma maganar nan ta fita daga cikin parlorn nan na gaya muku. Ammi wannan ai ba maganar da za'ayiwa shiru bace, naji duk abinda kuke cewa ni kaina ina bayanki yayya gumsu. Cewar Modu daya dad'e tsaye a gurin bayan duk ya gamajin komai tun sanda jakadiya take magana,duk gaba d'aya suka juya suna kallon hanyar shigowa parlorn fuskar Modu a had'e zuciyar shi na zafi sai b'allawa jakadiya harara yakeyi wadda tunda ta fara magana har kawo yanzu bata d'ago ta kalli kowa dake cikin parlorn ba. K'araso ciki Mommodu. Ammi ta fad'a tana kallonshi,kusa da ita ta nuna mai ya k'arasa ya zauna sai faman uban nishi yakeyi tamkar wanda akayi danbe dashi cikin sanyin murya Ammi tace. Haba Mommodu!Idan rai ya baci ai bai kamata ace hankali ya gushe ba,meye ribarmu idan muka ce zamu tozarta su?kaga duk mun zama su kenan babu me hankali da tunani a cikin mu.Ina son kuyi hakuri musamman idan kuka yi duba da ganin yadda suka dinga k'ok'arin ganin sun rabamu da Maimartaba amma hakan Allah besa ya kasan ce ba, suka kuma yi k'ok'arin nakasa d'an uwanku toh shi sun samu nasara sai dai tashi kaddarar kenan kuma ya rungumeta, sannan sukayi kokari wajan hana Aliyu ya zama sarkin yanzu amma duk Allah be basu nasara ba kunga sai mu godewa Allah domin yana tare damu kuma yana amsa mana duk wasu addu'o'in mu hakan yasa nace kuma kuyi hakuri ku yafe musu. Amma kuma Ammi ai... Ammi tayi saurin katse aunty yaruwaiya ta hanyar d'aga mata hannu sannan ta maida kallonta wajan jakadiya tace, Nagode jakadiya zaki iya tafiya Allah kuma ya k'ara sauk'i ya k'arb'i tubanki. Cikin tsananin murna jakadiya ta kuma duk'awa tayiwa Ammi godiya sannan ta mik'e tana rarrafawa da sauri Ammi ta danna wata k'ararrawa a gefenta sai ga wata baiwa ta shigo cike da ladabi tayi gaisuwa sannan Ammi tace, Temaka mata ki kaita har clinic. Baiwar ta kuma rissinawa alamar amsawa sannan ta Kama jakadiya wadda ke ta faman kuka tana godiya a haka suka fita, kamar dama jira sukeyi yayya gamsu da Modu suka fara mita kamar zasu tashi sama ita kuma aunty yaruwaiya abin da ya kona mata rai ne ya hanata cewa komai can kuma tace. Kai gaskiya wallahi Ammi wai harda yi mata godiya, kota mecece kuma oho. Duk Ammi najin su tayi dariya kawai tana kallonsu cikin son bagarar da zancen Ammi tace. Wai Mammodu ina matan naka?! Sai yanzu ma ya tuna da cewar tare suke sannan ya sosa sajansa tare da furzar da iskar bakinshi yace. Wallahi Ammi sabida b'acin raima ni na manta tare muke dasu, sabida muna shigowa naji ana magana sai nace duk su zauna a waje. Ammi ta zaro ido cikin mamakin shi tace, Waje kuma Mommodu?! Yace, Eh wallahi Ammi,ah toh ai naga su ba huruminsu bane magana ce ta cikin gida. Da sauri Ammi ta mik'e tayi waje tana cewa, Subhanallahi surukan nawa zaka bari a waje kai kuma ka shigo ciki dan dai ku yaran nan hankalinku a kaurinku yake.. Ta k'arasa fad'a tana mai barin cikin parlon, zaune ta tarar da su layla ta mik'ar da kafa sabida sun d'an kumbura yayin da kiara ke mammatsa mata sai hira suke suna dariya da alama basuji haushin barinsu da yayi ba Ammi tayi murmushi cike da jin dad'i sai taji inama ace matan Aliyu hydar suma zasu yi haka lallai da tafi kowa jin dad'i amma kullum tana kan yi musu addu'a Allah ya dai-daita tsakaninsu. Kai! kukuma sai kuka biye mishi kuka zauna anan?maxa kutashi ku shiga ciki. Lahh Ammi ai ba komai wallahi idan kuka gama sai mu shigo. Cewar layla ita kuma kiara ta mik'e ta k'arasa wajan Ammi tare da rungumeta cikin ladabi tace, Good-evening mah. Ammi tayi murmushi tare da dafa kanta tace, Oya kushiga ciki sai Mu gaisa. Komawa kiara tayi wajan layla ta kamo hannunta suka shiga ciki Ammi sai kallonsu take cike da sha'awarsu suna gaba tana bayansu,suna shiga layla ta zauna a k'asan carpet yayin da kiara ta wuce kusa da Modu sai da ta fara kaimai peck a goshi sannan ta zauna kusa dashi ya shafa kai saboda kunyar Ammi tare da basarwa. Zama sukayi aka ci gaba da tattauna zancen lokacin gid'ad'o ya shigo parlorn kusa da Ammi ya zauna cikin rad'a-rad'a yace. Ammi tunda ku bazaku koma gida ba gaskiya ni yau a kusa da baah Ngari zan kwana. Kallonshi tayi tana dariya kafin ta riko hannunshi tace, A'a ka bari ai gobe zamu koma muma haba kaida za'a bar mana kai a nan. Gaskiya Ammi ni tafiya zanyi anayin sallar isha. Ammi tace, Toh autah yadda kace haka za'ayi. Dariya yayi sannan ya mik'e yana cewa, Su Meenah anji lafiyayyan bed harda fad'owa k'asa tim.! Aunty yaruwaiya da Yaya gamsu suka tuntsire da dariya dan sun gane su amma Ammi dasu Modu sam basu gane ba. <<<>>>>> Gaba d'aya hajja yakolo ta gama fita a hayyacinta domin ganin yareemah Ngari yayi mata wahala mik'ewa tayi da kudirin zuwa duk yadda zata yau sai ta ai watar da,aikin nan tunda gashi har sunyi waya da hajja gajiram ita har tayi guda d'aya amma ita ta kasa yin nata. A hankali ta fita kamar wata mai ciwon jiki ta k'arasa sashen tana zuwa security d'in ya kalleta cikin rashin saninta yace, From where?! Hajja yakolo taji wani kudum a k'irjinta ciki rawar murya tace, Ni..ni..'yar..'yar uwar Ammin shi ce nazo dubashi ne yanzu muka yi waya da ita tace tana shehuri, Allah yasa dai ba bacci yayi ba dan a kan hanya nake wucewa zanyi... Kallonta security d'in yayi fuskar nan tashi a had'e kamar bazai bariba sai kuma yaga ai tunda ta wuto get yasan da gaske take gashi babbar macece wadda idan ka ganta kasan lallai daga babban gida ta fito,cikin girmamawa ya matsa mata ta wuce ciki wanda hakan ya kuma sanya jikinta yin rawa tamkar ana girgizata. Tafiya take a hankali tana faman waigowa bayanta har ta k'arasa ciki, parlorn babu kowa sai k'arar naurar sanyayya d'aki ga wani uban kamshi da yake standard ta fara rarraba idanuwa,sannu a hankali tana tafiya harta k'arasa kusa da bedroom d'inshi,ido d'aya ta kanne tana leken ciki zaune ta hangeshi saman sallaya yana lazimi dan idar da sallarshi kenan kasan cewar yanzu kam alhamdulillah yana iya yin wasu abubuwan da kanshi ba