← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 107

Sashe 26

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* NANA HAFSAT (_*MISS XOXO_*) HASKE WRITERS ASSOCIATION (_*Home of expert and perfect writers_*) _*Devoted to_* cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*) _*Tukwicine agareku_*: _*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*) _*particular thanks goes to my two adorable daughters_* : _*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*... _38/39_ nanahafsat.wordpress.com ____________ *Y*ana d'agawa yareemah Aliyu hydar ya fara gaida shi cikin girmamawa harsai da suka gama gaisawa sannan Mai Alooma Ghaji yace mai; Aliyu kana kusa ne?! Da sauri tamkar yana gaban shi yayi k'asa da kai yana fad'in; Eh Baffa ina apartment d'in mu,ko na zo kana son ganina?! Yareemah Aliyu hydar ya tambaya yana d'an fito da idanuwa waje,Modu ya d'auke kai daga kallon shi da yake yi dan karma yace yazo ya raka shi,Mai Alooma yayi murmushi yace; Eh Aliyu ka k'araso zuwa parlor na,ina son yin magana da kai. Yareemah Aliyu hydar ya mik'e yana gyara wuyan rigar shi dan kar ma Modu yayi mishi rashin mutunci yasa yayi tafiyar shi gurin Baffa ba tare daya ce yaraka shiba tafiya yake yana sake'saken kome Baffa zai gaya mai Allahu a'alamu gawai be ankaraba yaji yayi tuntub'e da abu a k afarsa yayi saurin kallon gurin sai yaga Meenah a tsugunne tana tsintar 'yan tsakuyoyi bugetan da yayi ne yasa ta kifawa a k'asa cikin masifar ta tayi saurin mik'ewa tsaye tana fad'in; Kai! Kakai kakai!! Tab' to wallahi bazan yadda ba ai babu abin da nayi maka zaka turani na fad'i. Meenah ta fad'a tana kallon yareemah Aliyu hydar daya d'an dafe goshi alamar shima ba haka ya soba,ta kalle shi tare da rik'e k ugunta tana turo mai baki da yayi niyar bata hak uri sai ya fasa ya wuce ta gefenta cikin daddad'ar muryarta ta juya tana cemai; "Yaya Aliyu hydar take a look at this ...!" Be kawo komai ba ya d'auka wani abun zata nuna mai yana juyawa kawai yaji ta watso mai duwatsun data tsinta tare da rugawa da gudu tana mai dariyar mugunta. Wani tukuk'in takaici yaji ya makale mai a wuya,da k yar ya samu ya had'iye shi tare da nufar hanyar parlorn Baffa. Bayan yayi sallama Mai Alooma ya amsa mai tare da cewa ya shiga.Sai daya samu guri ya zauna sannan ya kuma gaida Baffan nashi cikin girmamawa. Aliyu na kiraka ne daman dan na sheda maka cewar na sanar da Aminatu kuma cikin hukuncin ubangiji ta yadda ta amince,ina fatan Aliyu zai rik'eta amana kamar yadda zaka kula ka rik'e Basmah *SON RANKA*,ko Yaya ne Aliyu ka daure ka fita hakk'in Aminatu nasan ita d'in ba *ZAB'IN KA* bace zai yi wahala ka yadda da ita musamman yadda take da rashin ji da kafiya akan abu,shi yasa tun anan zan rok'eka alfarmar kula da ita daidai gwargwadonka. Mahaifinka na san mu k'ara zama abu guda d'aya hakan yasa ya kafe akan had'aka da k anwarka,za'a d'aura muku aure sai dai bazata tare a gidan kaba har sai lokacin da ta kammala secondary school inasha Allahu. Mai Alooma ya fad'a yana nunawa Aliyu hydar cewar ya daure yayi biyayya.Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke jin cewar har sai ta kammala secondary school za'a kawo mishi ita wani farin ciki ya sauka cikin zuciyar shi har yaso ya fallasa kanshi ya dai daure da k yar yana sunkuyar da kai. Toh Baffa insha Allah zaku sameni me biyayya a gareku nagode Allah ya k ara girma." Amin Aliyu tashi kaje sai ka nemi kanwartaka idan ka fita ko?! Toh Baffa zan nemeta na gode Allah ya kara girma da lafiya. Amin. Mai Alooma ya amsa yana murmushin jin dad'i yareemah Aliyu hydar ya mik'e yabar parlorn zuwa apartment d'insu ko takan neman Meenah beyi ba... _*BORNU(SHEHURI)_* Gabaki d'aya hajja gajiram ta matsawa kanta ta hanawa rayuwarta jin dad'i fatanta da burinta be wuce yadda zata ga sun kawar da yareemah Aliyu hydar ba domin boka na sambisa ya tabbatar musu da cewar shine sarkin gobe. A fusace tayi apartment d'in babagana ko kuyanginta bata bari sun bitaba,tana zuwa ta tura k'ofar bedroom d'in wanda yasa tayi saurin jan baya tana faman dafe k'irjinta zuciyar ta tamkar zata fito dan tsananin tashin hankali tayi saurin jingina jikinta da bango saboda numfashinta neman dena aiki yake yi. Tana jiyo yarinyar na ihu tana bashi hakuri amma yak'i sakinta har dukanta tajiyo yanayi. "Nashiga uku ni gajiram wannan wane irin bala'i ne yau take gani? Babagana ya wulakantata,yaci zarafinta tana can tana fafutukar neman mai mulki shi yana nan yana b'ata yaran mutane cikin takaici ta fad'a cikin d'akin tana tafa hannuwanta idanuwan ta sai zubar hawaye suke. A hankali babagana ya d'ago yana kallonta bayan ya rufe jikinshi da blanket kallon yarinyar dake kwance tamkar matacciya hajja gajiram tayi taga bata da niyar suturce jikinta sai ta matsa kusa da ita da niyar d'auketa da mari nan taga idanuwanta a kafe bata ko k iftawa hankalin hajja gajiram ya k ara tashi ta kalli babagana dake k arin janyo pajamas d'insa zai sa tace; Dan ubanka ka kashe musu yarinya,sannan ka tsaya kana kallo na yar gidan uban wacece ka d'akko musu eh? Ta tambaye shi bayan ta k'arasa ta rufe jikin yarinyar gorar ruwan eva ta hango sai a lokacin tayi tunanin shafawa yarinyar ruwa,da sauri tayi abinda zuciyarta ke gaya mata aikuwa cikin sa'a yarinyar ta farfad'o tana ta ihu tana cewa; Yareemah dan Allah karka b'atamin rayuwata,karka rabani da *Martabata* dan...dan...dan ahhh. Yarinyar ta saki wata razananniyar k ara wadda tasa hajja gajiram juyawa da gudu zata bar d'akin taji babagana ya dakawa yarinyar tsawa hakan yasa ta tsayawa.mik'ewa yarinyar tayi tana janyo kayanta ta sanya rigar duk ta yage saboda kokawar da sukayi tana gama sanyawa tayi yunk urin mik'ewa ta kasa sai ta kuma sakin wani kukan gashi ta kasa kallon hajja gajiram sai itace tayi k arfin halin cewa yarinyar; Ke dallah rufemin baki sakarai kawai uban waye yace ki biyo shi ai da saninki kika zo ya lalataki shine dan munafinci kin ganni zaki dinga yiwa mutane kuka,tunda kika b'atamin yaro dan ba halinshi bane kema sai kinci ubanki yau d'innan sanar dani ya akai kika shigo cikin gidan nan har cikin d'akin nan?! Hajja gajiram tayi maganar tana kafeta da idanuwa ranta a b'ace,shi kuwa yana gama sanya takalmi da kaya beyi wani tunanin yin wanka ba yasan ya kai yabar gidan ko takan su bebiba.cikin kuka yarinyar tacewa hajja gajiram; Suna na Bilkisu sheriff bunu mai agogo mu y an unguwar bulunkutu y an nono ne ana kirana da billy ni d'aya ce 'ya mace a gurin iyayena mun samu tarbiya da ilimi both boko da Arabia wata rana na dawo daga gidan yaya na akan hanyata ta komawa gida shine naga ana bina da mota sai nayi saurin tsayawa dan naji tsoro saboda motar bata k ananan mutane bace gashi babu mutane a layin sai mai motar yafito ya karaso inda nake tsaye jikina har rawa yake saboda ban saba tsayawa a waje ba,kallon da naga yanamin ne yasa na k'ara tsurewa na shiga cikin tashin hankali bud'ar bakin shi sai cewa yayi min; am in need of you baby." Billy ta kuma sakin kuka tare da toshe bakinta tana faman girgiza kai,hajja gajiram dake tsaye jikinta sai karkarwa yake ji take tamkar ta shak'e billy dan tsananin takaici,bata k aunar taji ana cewa babagana yayi wani abun Allah tsine sai dai ya zata yi tunda ita kanta ba tsoranta yake yiba,muryar billy ta katse mata zancen zucinta inda ta cigaba da cewa; Inajin ya fad'i haka na fara jada baya cikin sa'a kuwa na kwasa aguje ban tsaya ba sai a tsakiyar d'akin Maman mu,nan tayi ta faman tambaya ta akan abinda nakewa gudun ban b'oye mata komai ba tace min daga yau ko naga mota na bina na dinga guduwa karna tsaya nace mata tom.tun ranar ban sake ganinshi ba sai yau da asuba na shirya zan tafi tahafiz banji motsin shiba kawai sai ganin shi nayi rik'e da hijjab d'ina kafin nayi yinkurin guduwa ya toshe min bakina inda ban sake sanin komai ba sai a cikin d'akin nan.... Bilkisu ta k arasa maganar cikin kuka mai ban tausayi amma dan rashin imani irin na hajja gajiram sai taja wani uban tsaki tare da nuna billy da yatsa tana cewa; Ki shiga hankalinki,kisan abinda zaki dinga fad'a wannan maganar taki duk kamekame ce domin babu abinda na yadda dashi a ciki yanzu zan baki kud'i masu yawa wanda zaki yi amfani dasu ki rufe wannan shegen bakin naki idan kika kuskura kika sanar da wani cewar ga wanda yayi miki wannan abun baza ku sake kwana d'aya a cikin duniyar nan ba dake da iyayanki kina jina ko?! Cikin bak in ciki da zafin zuciya billy ta d'aga kai alamar toh tana share hawayanta,da haka hajja gajiram ta mik'e tsaye tana cewa; Ki shiga bathroom kiyi wanka kizo ina jiranki a parlor. Tana kaiwa nan tabar d'akin waya ta d'auka tana neman jakadiya,tana d'agawa tayi mata bayani tare da cewa; Ina son yanzu kije gurin boka na sambisa kice ina son yanzu a d'auke hankalin yarinyar ta kasa fad'ar wanda yayi raping d'inta. Jakadiya ta rissina har k asa kamar tana gabanta tace; An gama rankishi dad'e.. Billy na fitowa kanta a k'asa hajja gajiram ta mik'e tayi gaba billy na biye da ita tana tafiya tamkar 'yar kaciya har suka shiga apartment d'in hajja gajiram,kud in ta d'akko masu yawan gaske ta damk awa billy dake sharar hawaye sannan ta kalle ta cikin kask anci tace;. Kiyi gida karki k'ara koda mafarkin gidan nan bare kiyi tunanin shi kinajina...?! Tayi maganar a fusace billy ta d'aga kai tana hawaye cikin muryar kuka tace; Toh..! Da k yar ta fito daga cikin shehurin ta samu me napep lokacin tasha bak'ar wahala saboda akwai nisa kafin ka fito daga cikin palace d'in tana shiga cikin gida komai ya tsaya mata cak ta kasa tuna waye yayi mata wannan abun haka har su abban ta da 'yan uwanta suka gane abinda ke faruwa da ita akai akai tafad'a tayi shiru duka,lallami duk tayi shiru sai kuka da take yi....... _YOLA (JIMETA)_ *K*wance yake akan makeken gadan su baki
Chapter 26 · 0% Book details