← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 107

Sashe 19

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

_*A STUNNING LOVE STORY_*
_*NA_*
NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(_*Home of experts and perfects writers_*)
_* Devoted to_* :
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_* :
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_28/29_
This page is for you my beloved sweetheart
I love you to the moon round and back(_*ASMY B_*)Allah ya k'aro d'imbin basira acigaba da suburbudo mana _*NEESA_ADEEL_*
nanahafsat.wordpress.com
____________
*_WASHEGARI_* :
Bayan sun idar da sallar asuba yareemah Aliyu hydar yayi karatun alqur'ani kamar yadda ya zame mishi wajibi,komawa yayi kan makeken gadon da aka tanada a cikin bedroom d'in wanda Modu ke kwance a gefe shima ya koma baccin.Kwanciya yayi yana sauke ajiyar zuciya gaba ki d'aya gidan ya isheshi yana son komawa gida kodan yaga jikin d'an uwanshi yareemah Ngari, be tab'a mantashi ba koda na sakan d'aya ne.
Pillow ya janyo tare da d'ora kanshi, tunani kawai yake yadda zasu k'ark'are da Mai Alooma yau idan sunje gurin shi.A zahirin gaskiya baya son a rabashi da Basma, gashi anan be son wadda za'a bashi ba cuz yana da choice na irin Matar da yake son ya aura, addu'a kawai yake Allah yasa Mai Alooma karya matsamai dan indai ya tambaye shi zai gaya mishi gaskiya cewar yana da wadda yake son ya aura.
Ya dad'e yana tunani hakan ya hanashi komawa bacci, misalin k'arfe 8:00am yareemah Aliyu hydar ya mik'e, bathroom ya shiga tare da sakarwa jikin shi shower.Wanka yayi sosai da sabulai masu k'amshi sosai sannan ya fito k'ugunshi d'aure da towel mai d'an girma sai karami yana tsane gashin kanshi har ya dangana da dressing mirror daidai time d'in Meenah ta shigo neman su bako knocking bare abata izinin shigowa..
Abin da ya faru Mai Alooma yayi ta kiran phones d'insu babu wanda ya d'auka, yana son jin ko suna lafiya gashi duk mazan basu fito ba sai da Meenah ta shiga bayan ta gasheshi ne yace taje ta gano kosun tashi, shine dalilin zuwan Meenah apartment d'in har ta shiga ciki.
Bata gansu ba a parlor,kitchen nanma duk basa nan kawai ta doshi bedroom ta shiga ba tare da tayi sallama ba kasan cewar k'ofar room d'in a bud'e take.
Modu indimi ta fara hangowa akan bed yana ta sharar bacci, kwata-kwata bata lura da yareemah Aliyu hydar ba dake tsaye jikin dressing mirror yana shafa mayuka a jikin shi. Muryarta kawai yaji ba tare da yaji motsin shigowar ba ta tana cewa;
"Tab lallai ma rainin hankali,bacci ma kuke yi bayan Baffa na can yana jiranku d'an rainin hankali."
Meenah ta fad'a tana
k'arasawa gurin gadon da Modu ke kwance, hannu takai zata tashe shi sai taji motsi hakan yasa tayi saurin kallon gurin.
Karaf sai taga yareemah Aliyu hydar yana k'ok'arin komawa bathroom, cikin rashin damuwa da yadda ta ganshi tayi mai magana,
"kai kai wait...!"
Cak yareemah Aliyu hydar ya tsaya ba tare da ya waigo ba dan beso ta ganshi a yadda yake ba, dan baya k'aunar yaga wani yaga jikin shi a haka.Gefe d'aya kuma zuciyar shi ke tafasa wai kai sekace wani k'aninta lalle yarinyar nan tagama renashi,Be juyo ba ta fara tafiya zuwa inda yake tana tab'a baki dan tunowa da kama mata gashin da yayi, ta bayan nashi ta tsaya tana mai magana;
"Yanzu dama idonka biyu amma kanajin Baffa na kiranku a waya kak'i d'auka?!"
Yareemah Aliyu hydar ya tsuke baki ba tare da ya juyo ba yace:
"get out from this room stupid girl." Yana fad'in haka ya shige bathroom ba tare daya rufe shi ba.
"Wallahi sai naje nace mai kana ganin kiran kak'i d'auka, shi kuma d'ayan bacci ma yake...."
Yareemah Aliyu hydar yajiyo ta fad'a sannan kuma tabar d'akin. Shima fitowa yayi cikin b'acin rai dajin sharrin da zataje tayi musu ba tare da sun san abinda suka yi ba, lallai yarinyar nan tana son kafin yabar garin ya nuna mata ko shi waye. Cikin zafin rai ya d'akawa Modu idimi duka tare da komawa wajan trolley d'in.
"Guy mene haka?"Kasan dai ban..., da sauri yareemah Aliyu hydar ya dakatar dashi cikin b'acin rai ta hanyar cewa;
"Kaga fa,katashi ka nemo mana solution yadda zamu fitar da kanmu wajan Baffa." Modu yayi saurin sauka daga kan gadon ya k'arasa wajan yareemah Aliyu hydar da d'inbin mamaki.
"Guy ban gane ba, what's going on...?!"
Yareemah Aliyu hydar ya ja numfashi tare da sauke shi, nan ya bawa Modu labarin yadda aka yi cikin takaici ya d'ora da fad'in.
"Sai na koya mata hankali kafin mubar garin nan tunda naga alamar bata da kunya." Shima Modu ba k'aramin mamaki yayi ba, bathroom d'in shima ya shiga yana mamakin sharri irin na Meenah.
Modu na fitowa yaga har yareemah Aliyu hydar ya gama shiryawa cikin wani had'add'an boyel mai kyau da tsada wanda aka yi mai d'inkin da ya amshi jikin shi, kamshi sai fita yake ya koma bakin bed ya zauna yana saka covered shoe d'inshi.
"Guy nifa banga wani mafuta ba dan bamu san sharrin da taje tayi mana ba." Cewar Modu yana saka kaya a jikin shi, shi dai yareemah Aliyu hy
dar be ce komai ba dan yasan duk iya sharrinta baza'a doke suba.
Tare suka fito zuwa parlor nan suka ga anjera musu kayan breakfast a saman dinning table, k'arasawa suka yi kowa ya d'ibi abinda zaici. Suna kammalawa suka mik'e sai da suka fara shiga gurin Aunty Maijidda, zaune suka same ta kamar jiya tana k'ara had'a turaruka. Sosai suka gaisa sai dai tana d'an jin kunyar su nan tayi musu tayin wani abincin suka ce sunci yanzu.
"Aunty bari muje mu gaisa da aunty yafendo sai mu k'arasa gurin Baffa."
Modu ya fad'a suna k'okarin tashi su fita,cikin dattako Aunty Maijidda tayi sallama dasu sannan suka nufi side d'in aunty yafendo yau kam ba kowa suka shiga bayan sunyi mata sallama tace su shiga.
Sai da suka zazzauna sannan suka gaisa tayi musu ya gajiya sannan ta k'ara bawa yareemah Aliyu hydar hak'uri akan abunda ya faru jiya, murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.Modu ne yayi dariya yana kallon Aunty yafendo cikin kalle kalle yace;
"Aunty yau banga kowa ba hope komai lafiya duk banga yaran ba?!"
Aunty yafendo tayi murmushi itama tare da cewa;
"suna cikin islamiya nan da 12:00pm zaka gansu sun dawo."
Shi dai yareemah Aliyu hydar baya cewa komai ji yake ma tamkar d'aure mai baki ake har suka yi mata sallama suka nufi apartment d'in Baffa Mai Alooma Ghaji...
Directing d'in su aka yi cikin k'aton parlorn Mai Alooma wanda tsayawa fad'in kyawunsa alk'alami ba zai iya rubutawa ba saboda azabar tsaruwar shi,hatta yareemah Aliyu hydar sai da ya ky'asa parlorn a haka suka zazzauna cikin royal kujerun dake zagaye suka zauna Modu sai faman santi yake tare da yiwa yareemah Aliyu hydar sha'awar irinshi. Sun d'an jima zaune kafin Mai Alooma ya sallami visitor's d'inshi ya k'araso inda suke cikin fara'ar shi.
K'ok'arin gaida shi suka yi yana amsawa tare da tambayar ya suka kwana a b k'wan guri
"Baffa lafiya lau ai nan ba bak'on mu bane." Cewar Modu yana satar kallon yareemah Aliyu hydar dake ta faman murmushi k'asa k'asa.
"Naji sak'on ku gurin Meenah amma nasan halinta shi yasa ban yadda ba."
Mai Alooma ya fad'a yana binsu da ido,cikin zumud'i da son jin me tazo ta fad'a Modu ya gyara zama tare da fad'in;
"Lahhh Baffa me tazo ta gaya maka?!"
Mai Alooma ya kalle su sannan yace;
"cewa tayi duk wayoyin ku suna hannuwanku amma kuna ji na kira baku d'auka ba,shine tace min marar surutun shine me cewa karku d'auka,sannan tace ina kiran ku again marar surutun ya daka mata tsawa yace tabar musu d'akin koya b'allata."yafad'a yana k'ok'arin gimtse dariyar data taho masa
"Wallahi Allah Baffa k'arya take mana dan ni time d'in wallahi bacci nake shi kuma yana wanka amma ba haka bane abinda ta zo ta fad'a." Cewar Modu indimi cikin gasgatawa,
Murmushi Mai Alooma yayi dan dama can be yadda ba Allah ya gyara mai Aminatu ya fad'a cikin ranshi.
Yar dariya yayi sannan yace;
"kayya bar rantsuwa Muhammad nasan halin Aminatu trouble maker ce ta k'arshe kodata fad'a ma korata nayi nace tatafi..."k'arashe xancen yai had'e da gyara zama tare da maida hankali gurin yareemah Aliyu hydar yace;
"Aliyu ya maganar ina fatan dai ba dole mahaifinka yayi maka ba?!"
Shiru yareemah Aliyu hydar yayi dan har ga Allah dole aka mai sannan shi baya son ya cuci kanshi, maganar Mai Alooma ce ta dawo dashi daga zancen zucin da yake yi;
"Aliyu karka damu kankafa,ni kaina baxan yadda ayi maka auran dole ba kasan cewar yanzu kai ya waye ilimi ya yawaita, 'yancin kai ya samu ka gaya min kana son auran Meenah da ra'ayin kanka ko kuma a'a kana da wadda kake so zaka aura?"
A hargitse yareemah Aliyu hydar da Modu indimi suka kalli juna, cikin tsananin rud'ani Modu na rawar baki yake cewa "Baffa wacce Meenahn?"
Mai Alooma na lura da yanayin su,murmushi yayi tare da cewa ;
"Meenah dai k'anwarku da na aiko d'azu, Aliyu bana son ka rufeni ka gaya min gaskiya idan kanada wadda kake so."
Zama Modu ya gyara yana jiran jin amsar da yareemah Aliyu hydar zai bawa Baffa. K'irjin yareemah Aliyu hydar sai bugawa yake tamkar zai fito, namijin k'ok'ari yayi wajan sunkuyar da kai yayi ma Baffa bayani;
"Baffa bawai bana son Meenah bane a'a kawai na riga nayiwa wata alk'awarin aure ne kuma wallahi Baffa saboda ni bata kula kowa... Amma kuma baba abisa binciken dayai...."Shiru yai yakasa k'arashe maganar cikin sanyi a ranshi kuwa cewa yake;
Da Meenah gara ya zauna beyi aure ba, yarinya babu kyan fasali abu kamar zanan one...
Babu wani damuwa ko rashin jin dad'in maganar yareemah Aliyu hydar a cikin zuciyar Mai Alooma domin shi mutum ne me san gaskiya da gaskiya baya san kabar abu cikin ranka. Cikin kulawa yake kallon yareemah Aliyu hydar yace;
"Karka damu Aliyu insha Allahu nine zan nemo maka auran matar da kake so, kabari ni zanje na samu baban naka na fahimtar dashi kar wani abun ya dameka kaji ko?!"
"To Baffa na gode Allah ya k'ara girma na gode Allah yajik'an mahaifa amin."
Duk suka amsa da Ameen mamaki kuwa ya kasa barin zuciyar Modu dan be tab'a tunanin yareemah Aliyu hydar zai k'i karb'an zab'in iyayen shiba,haka Mai Alooma ya dinga jansu da hira har wajan 1:49pm sannan suka tafi masallacin cikin gidan dan gabatar da sallahr zuhur.
...............
Suna komawa apartment d'in su dama yareemah Aliyu hydar ya gama fahimtar Modu magana ce da tuhuma fal cikin shi hakan yasa suna shiga parlor ya zauna. Modu ya kalle shi cikin tsananin fushi wanda be tab'a yi ba tsakanin shi da hydar d'in ba ya fara magana;
"Ko a mafarki ban tab'a tunanin cewar zaka yi abin da ka aikata yau ba, why yareemah ka watsawa baba k'asa a ido? Yanzu _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE_*zaka bi? Nayi nadamar rakoka da nayi wallahi yanzu bansan da wane idanu zamu kalli baba ba aikin banza kawai."
"You're sick Modu!; kai da kanka ka fara kawo k'orafi akan yarinyar nan kafin ni na bud'e baki na fad'i wani abun akanta, and idan kana ganin nayi laifi me yasa baka canjeni ba kace kai a baka ba? Please karka takura min domin nima inada zab'in raina ka gane ko!"
Cewar yareemah Aliyu hydar tare da shigewa bedroom ko takan abincin bebi ba saboda tsananin b'acin rai.
Tsaki kawai Modu yayi cikin takaici ya fad'a kan kujera yana furzar da iskar cikin bakin shi. Shi kam yareemah Aliyu hydar wanka ya shiga, ya k'agara gobe tayi su tafi gara yaje yasha fad'an baba domin yasan dole ya fuskanci matsala tunda gashi Modu ma ya nuna b'acin ranshi akai. A ranar haka suka wuni suna 'yar shariya duk da cewar Modu na k'arfin haline dan baya son yin fushi da yareemah Aliyu hydar hakan yasa da dare yaje ya same shi har sai da ya tabbatar sun shirya sun koma kamar da, daga nan kowa ya d'auki phone d'inshi ya kira girlfriend d'insa,Amma fa kowanne zuciyarsa cike takeda fargabar abinda xeje yadawo wajen mai martaba hakade kowannensu yaketa sak'awa da warwarewa sallah ce kawai ke tashinsu suyi su sake dawowa suci gaba dayi harde dare yai nisa bacci b'arawo yasashesu...
_*SAFIYA TA GARI_*
Yola_Jimetaa(Mai Alooma Ghaji Residence)
SRKZBI?!fans
Team#Basma/Meenah?
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_*
Chapter 19 · 0% Book details