← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 107

Sashe 21

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Mai-martaba beyi ba,cikin nuna halin dattako ya fara magana; "Lalah ba haka ake yiba,idanka duba yanzu kai ya riga ya waye.ilimi ya yawaita idan aka yiwa namiji auran da baya so zuciyoyin da ake son gyarawa sune zasu b'aci domin zaman lafiya da jin dad'in da muke son ayi baza suyi shiba saboda zaman lafiya a gida mijine ke fara samar dashi,yana da wadda yake so sai abashi ni da kaina zan kuma bincikawa akan ita yarinyar da yake so." "Nariga nayi duk binciken da za'ayi an kuma tabbatar min da hakan,sannan hatta yaron nan Modu da idanunshi ya ganta,ka kuma san bazai min k'arya ba..." Cewar Mai-martaba cikin tabbatarwa,yana son d'an uwan nashi ya fahimta ya kuma bashi goyan baya akan had'in da yake son suyi. "Duk da haka dai zan sake bincike akanta,banason a dinga yiwa yara dole bayan nan gaba sune manya. Karka damu dan ta Ameenatu me sauk'i ce saboda ita macace bata da wuyar tank'warawa" "Kawu bawai jayayya nakeso nayi dakaiba a'a sam bahaka bane kawaide nariga nayanke hukunci ne kuma ina mai farin cikin son wannan abu yatabbata" "Karka damu insha Allahu komi ze tafi yadda kakeso inde xancen Aminatu ne kad'auka kamar anyi angama ne se abu nabiyu kuma akan d'ayar yarinyar da Aliyu ke so nizan k'ara bincike akai kuma idan har kayadda wannan abu yatabbata ba k'aramin jihadi kaiba saboda kaceto ran dake shirin fad'awa halaka wallahi kaji rantsuwar musulmi aurenta da zeyi ze zamo silar rabuwarta da miyagun k'awaye da duk wani aikin alfasha kuma ba k'aramin lada xaka samuba kai yanxu misali ace Aminatu ce ke haka kuma sai shi Aliyu yadage akan ita yakeson ya aura tsakani da Allah ba rufawa juna asiri zamuyiba ayi Auren hakane ko bahaka bane?!" "Hakane Kawu"cewar mai martaba jikinsa duk yayi sanyi Ganin jikinsa yayi sanyi yasanya Mai Alooma Ghaji gyara zama yashiga yi masa nasiha mai d'imbin ratsa b'argon jiki ya k'ark'are da; "Karka manta har ma'abota littafi Allah ya halarta mana mu aura danmu karkato hankalinsu izuwa ga addinin islama dukkoda tarin k'azantar dake tattare dasu na rashin musulunci,kaga yamin ita wannan yarinyar bata fisu ba?!" "Tafisu Kawu"yafad'a murya a raunane "Toh wannan shine abinda nakeso ka fahimta har kullum idan d'an uwanka musulmi yana shirin fad'awa ga aikin halaka sauri kake kai jihadin ceto rayuwarsa da duk abinda yakamata,tunda har yarannan suna son junansu yakamata mu mara masu baya wata k'ila hakan shine silar canxuwar rayuwar ita yarinyar muna fatan hakan da yardar Allah,Ina fatan kafahimta??" "Eh Kawu" "To Allah ya k'ara maka lapia da nisan kwana,Insha Allahu gobe idan mai duka yakaymu da rai da lapia nizan fara gudanar da bincike akan gidansu yarinyar yaya cikakken sunanta yake??" Mai Alooma yace hakan with confidence "Wai Basma Basheer Mai_Kano" Murmushi fad'ad'e a fuskar Mai Alooma yace; "Atoh komai yazo da sauk'i kenan domin Basheer Mai kano yaro nane yyi aiki a k'ark'ashina lokacin ina ambassador bazan mantaba bayan nayi retire nine naje har can kanon wajen gwamnan dayake shima nad'anyi mashi alkairi lokacin campaign nace dan Allah yabawa Basheer d'in aiki me tsoka yaron kirkine hakan kuwa akayi yabashi commissioner of finance" "Allah sarki..." Mai martaba yace hakan cikin jin dad'in daga gidan mutunci Basman tafito... "Saboda haka kabarmun wuk'a da nama komi ze dedeta insha Allah..." "To Allah yasa..." Mai martaba yace hakan tareda yin k'asa da kansa alamar tunani ajiyar zuciya yasauke shide Mai Alooma bece masa komaiba yanade naxartarsa,d'ago kansa yai ahankali yace; "To kawu Ameenan kuma fa.......?" Murmushin Mai Alooma ne ya fad'ad'a a nutse yace......... WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_*
Chapter 21 · 0% Book details