Sashe 30
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* NANA HAFSAT (_*MISS XOXO_*) HASKE WRITERS ASSOCIATION (_*Home of expert and perfect writers_*) *Devoted to* cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*) *Tukwicine agareku*: *Billyn Abdul*(Tawan) & my beloved sis(ya *Hajja ce*) *particular thanks goes to my two adorable daughters*: *Bitti Feedhom & dota Billy S Fari* _44:45_ This page is urs *Aunty sis* Allah yaraya newly baby boi cikin k oshin lapia..! nanahafsat.wordpress.com ____________ _*University of Oxford (United kingdom)_* *H*ello Amma!lafiya lau,ok Amma love you too,Aha bye. Basma dake waya ta sauke a hankali tana kallon layla dake wajan mirror tana makeup,tsaki ta d'an ja kafin ta kuma kallon layla tana fad'in; Daddy sun sauka yanzu,Amma tace daya kammala abinda ya kawo shi zai zo ya d'auke mu and kinsan dai.... Layla tayi saurin katseta ta hanyar d'aga mata hannu,cikin yatsina fuska ta isa wardrobe tana d'aukar kaya tana cewa; Ni duk gashi nan kinja min wani komawa Nigeria, komai zaka yi ana sama ido ba wani freedom duk abi a dameka. Tayi maganar tana cillo kayan da zata saka a kan gado,Basma ta kalleta sama da k'asa sannan ta zuro kafafuwanta itama ta shiga bathroom ba tare da ta kuma kallon inda layla take ba. Sai misalin k'arfe 3:15pm daddyn Basma yaje cikin University d'in su apartment d insu ya nupa suna zaune shi kawai suke jira dan haka suna ganin shi suka tashi bare ma Basma da gudu taje tare da fad'awa jikinshi tana murna kamar yarinya k'arama. Daddy I love and miss you.! Basma ta fad'a tana d'agowa daga jikinshi,yayi murmushi kawai tare da kallon inda layla take tsaye sai faman nok'ewa take yi kamar ta Allah. Daddy ina yini? Layla ta fad'a cike da ladabi kai kace bata aikata wasu abubuwan,amsawa daddy yayi tare da tambayar su karatu daga nan suka wuce inda suka ajiye trolley bag d'insu aka zuba cikin taxi suka wuce airport, karfe 4:00pm dai-dai jirgin su ya d'aga zuwa Nigeria, inda ya sauka garin abuja daga nan suka wuce kano ta dabo jallah babbar hausa bayan sund au awanni goma shabiyu asararin samaniya *KANO* Suna sauka driver yazo ya d'aukesu Amma sai murna take ta kuma k'agara taga Basma matar prince sarkin gobe. Suna shiga kuwa yayunta da k annenta da 'ya'yan yayan daddyn ta duk suka fito suka yi mata oyo-yo,farin ciki ya cika Basma har ta manta tana cikin damuwa. Bayan sun zauna an huta tayi wanka ita da layla suka zauna a k'atan parlorn su Ana ta hira har bayan asubah kasancewar hud u suka iso na dare sannan kowannensu ya tafi makwancin sa wanda Basma da layla d'aki d'aya suka zauna,kwanan su biyu sannan Amma ta samu damar keb ewa da 'yar tata can cikin bedroom d'inta,kallonta tayi cikin kulawa sannan Amma tace mata; Basma ya yareemah Aliyu hydar d'in komai yana tafiya normal ko?! Kuka Basma ta saki tare da fad'awa jikin Amma bubbuga bayanta Amma keyi cike da tashin hankali,har sai da Basma taci kukan ta sannan tayi shiru cikin ajiyar zuciya take fad'in. Amma ni yanzu bana son shi I hate him,.. Ya...ya yama za'ai dan wulakanci tunda be sanar min ba sai yanzu zai ce min mu biyu zai aura? Ni dai Amma ku gaya musu na hak ura na barwa cousin d'in tashi suje can su k arata. Murmushi Amma tayi irin nasu na manya, juyo da fuskar Basma tayi suka kalli juna cikin ido Amma ta sauk'e ajiyar zuciya tace; Ashe Basma ke sakarai ce?a haka kamar wayayya ashe kawai a fuskar kine toh bari kiji mahaifin Aliyu hydar ya nemi yayi aure ne saboda yana son ya gaji sandar shi,idan baki san matsayi da darajar sarauta ba ina son kije kinemo tarihinta.Ashe bakya son ki zama matar sarki?, ki samu d'aukaka ta musamman kuma gashi kinyi sa'a shine da bakin shi yace ke yake so yake buk atar aura?sai kinyi hak uri koda kin aure shi saikin daure domin Allah ne ya yarjewa maza yin auran mata har hud u kinga kuwa sarakuna ma harda k arin k wark warori sukeyi,ke ba abin dad'in ki bane kije a matsayin uwar gida a gurin shi ba?Idan mafarki kike Basma ya kamata ki dawo cikin hayya cin ki don k arin mutuncinki ne da namu baki d'aya. A hankali Basma ta dinga sauke ajiyar zuciya cikin karayar da kai ta kalli mahaifiyar ta idanuwan sunyi ja tsabar kukan da tayi tace; Amma wancan fa daban,wannan fa at d same time za'a d'aura wannan ai cin mutunci ne ni dai gaskiya na hakura. Tayi maganar cikin sanyi kai da kaji kasan kawai na kishine,Amma ta mik'e tsaya tare da fad'in; Toh shikenan bari naje na sanarwa da mahaifin naki sai ya sanar musu kinga kinyi asarar matashin saurayi sarki mai nutsuwa dan nima nasa an yi min bincike akan shi. Tana kaiwa nan tabar d'aki yayin da tabar Basma da fad'awa zuzzurfan tunani ta dad'e a gurin kafin ta koma gurin layla ta fad'a kan bed tare da sakin wani kukan dan ta kasa hak ura gani take yi tamkar wulak anta ta yake shirinyi.muryar layla ce tasa ta tsaida kukan da take; Your sugar boo ya bugo miki sai dai na d'aga nace mai kina tare da mumcy d'inki,idan kinga zaki iya toh daya bugo ki d'auka kar ki tsaya kishi wallahi ya tattara ya barki gabaki d'aya in amsawa layla maganganunta tayi itama bata sake mata magana ba ta cigaba da sawa faratanta jan farce,ba dad'ewa kuwa sai ga shi ya sake kiran ta taki d'auka sai da takusa yankewa sannan ta d'aga tana yatsina fuska; Duk suka yi shiru shi yareemah Aliyu hydar kambun mulkin ne ya motsa ita kuma tsananin haushin shi da take ji ya hanata yin magana,sai da suka dad'e a haka shiru ba magana sannan taji yace; Okay fine,bye! Yana kaiwa nan ya katse kiran Basma tabi wayar da kallo,wani guntun text message taga ya turo mata; Zan dawo gobe. Tunani ta fara yi, Ina zai dawo London?oh no ni ai na dawo kuma be saniba Samun kanta tayi da kiranshi,kamar bazai d'aga ba sai taji ya d'aga tare da yin shiru kamar yadda yayi mata d'azu,cikin muryar alamun yin kuka tace mai; Ina kano na dawo gida. Yareemah Aliyu hydar ya sauke ajiyar zuciya,cikin daddad'ar muryar shi taji yana cewa For real kina Kano? Oya send me your home address asap,inason gobe nazo insha Allah it yakatse kiran,tana jin yace zai zo ta zabura ta mik'e da sauri,wani farin ciki ne ya saukar mata ta ruga da gudu tayi wajan Amma,rungume ta tayi cikin farin ciki tamkar ba ita bace ta gama kuka ba,Amma tace; Karfa ki kayar dani Basma,me aka gaya miki haka yasa ki farin ciki a cikin zuciyar ki?! Amma tayi maganar tana dafa saman kujera dan sauran kiris Basma ta kaita k'asa.Murmushi tayi sannan ta kamo hannun Amma ta rik'e gam tana cewa; Amma gobe zai zo, yace min zaizo na tura mai da address.! Cikin rashin fahimtar maganar ta Amma tayi ajiyar zuciya tana fad'in; Waye kuma zaizo Basma?! My prince...! Ta fad'a tana rungume hannu a k'irjin ta kai da ka ganta kasan tana cikin farin ciki marar musaltuwa Amma tayi mata wani irin kallo bayan ta tab'e baki tana kallonta tace; Au zaki aure shinne? Ni da har naje nasanar da daddyn ku cewar kinfasa auran,kuma inajin ya sanar da kawun mahaifin Aliyun ta yiwu akan zancen yace miki zaizo. Amma ta fad'a tana k'ok'arin barin wajan Basma ta zaro ido tana bin Amma tana cewa, Kai Amma nifa bada gaske nake yiba wallahi ina...ina...inason abuna fa ya zaki min haka?! Tayi maganar cikin inina kamar zata saki ihu,ita kuwa Amma tayi wucewar ta bedroom cikin rashin damuwa take cewa; Ah toh gani nayi Basma kina neman maida mu k ananan yara,kinga maganin kada ayi toh karma a soma dts y. Nashiga uku Amma ya zanyi? I swear I love him shine son raina Amma kitausayamin koda na fad'a ma lokacin kishi ne dan Allah ki.... Amma tayi saurin tsayar da ita ganin duk ta damu sannan tace; Lallai to ni wasa nake,nasan dama k'arya kike kina sonshi kawai kishi ne ya rufe miki ido, yanzu sai ku fara shirya-shiryan tarbar shi. Farin ciki ya kuma dirarwa Basma ranar haka ta yini tana nishad'i ita da sauran yara aka hau gyara da tanadar abubuwan da za'a sauki yareemah Aliyu hydar...., _*BORNU (SHEHURI)_* *M*aimartaba ne zaune a cikin parlorn shi gefen daman shi hajja yakolo ce hagun kuma hajja gajiram ce, kowacce sai faman shan kamshi tak'eyi shi kam yayi shiru dan jira yake ya gama karantar fuskar kowa sai dai hakan ya tagayyara domin kowacce sai faman hura hanci take,kishingid'a yayi akan tumtum dake kusa dashi sannan yayi gyaran murya yana kallon kowacce ya fara musu magana; Inason in shaida muku da cewar d'anku zai yi aure kwanan na,sai ku fara shirye-shirye domin mata biyu zai aura a lokaci guda. Gabaki d'ayan su saida suka nuna razana zuciyar su na bugawa hajja yakolo ce ta samu damar yin magana cikin rawar baki had'a da inina tana kallon maimartaba tace; Rankashi dad'e wa...wa...wane d'an namu a ciki?! Batare da yakawo komai cikin ranshi ba yace;. Yareemah Aliyu hydar mana, shine zai yi aure kuma su biyu zai aura sai dai d'aya ce zata tare k aramar kuma sai ta kammala secondary school insha Allah. Yareemah Aliyu hydar kuma? Ahayyeee nanaye lallai sai yanzu na gane nufinka,dama tuncan nasan baka k aunar yareemah babagana idan ba haka ba ai shi yakamata ayiwa tunda ya girmewa Aliyu nesa ba kusa ba toh wallahi da sake dan wannan nuna banbanci ne Hajja gajiram ke ta faman jaraba ta inda take shiga ba tanan take fita ba,bin ta kawai maimartaba yake da idanuwa ba tare da yayi magana ba,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru tana hucci tamkar wadda tayi uban gudu. Hajja yakolo ce ta tab'e baki dama ita sai taga hajja gajiram tayi abu tukunna take yi saboda karta rasa me goyan bayanta dan haka yanzuma tana yin shiru ta karb'e zancen; Haka ne kam wallahi yayya dama an dad'e ana 'yar wariya a gidan nan,toh wallahi a dinga yi ana duba gaba dan in yau anyi abu anji