← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 107

Sashe 4

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfect writers)
nanahafsat.wordpress.com
5
Rungumesu yai shima yana jin son k'annen nasa na ratsa b'argon jikinsa, seda Affy da Aysa suka gaji da rungumar da sukai masa dan kansu sannan suka sake shi suna aika mashi da sak'on murmushi
Daka gansu kasan yan uwan junane kamarsu d'aya sede Aysa tad'an fisu hasken fata Ita kuwa Affy kamarsu d'aya da Aliyu Hydar har kalar jikinsa kamar yayi kaki ya tofar.....
Rik'e hannayensu yai atare suka shiga cikin gidah, lokacin da sukaje Ammi na sama tana wanka, haka su Affy suka tasashi suna zuba masa surutu dayake dama akwai su da labari,Affy k'aramar ciki shekararta goma sha biyu ita kuma Aysah shekararta sha shida... Ammi tad'an jima sannan tafuto sanye cikin dangasho blue anyi mata rigan bubu se k'aton mandil data yafa, kamarsu d'aya sak da Aliyu hydar sede ita tad'an manyanta kuma tafishi hasken fata, murmushi fal a fuskarta tafara sakkowa daga stairs d'in cikin parlorn tana magana cikeda nutsuwa;
"A'ah Hydar kaine ka k'araso?!nide ince naji ihun su Affy sama sama"tak'arasa cikin parlorn had'e da xama a doguwar kujerar 3 sitter k'irar royal!
Sakkowa Aliyu Hydar yai daga kan kujera yad'an durk'usa;
"Ammi inda watu?? Ahh u belan amma tusen gei"( Ina kwana Ammi?! Eh nashigo amma ban dad'eba)
"Okay to Allah yamaka albarka Aliyu sannu da zuwa"
Sund'an jima suna hira,kafin daga bisani ma aikatan gidan had'e da dogarai da kuyangu d'aya bayan d'aya suka shigo suna d'aukar gaisuwa,nan aka jere varieties na abinci akan makeken dining table se k'amshi ke tashi,
"Taso Hydar kaci abinci nasanka sarai dak'incin abinci kamar ba cikinka xaka kaiba,taso kaci"
"To Ammi ,baa Ngari(usman)yatashi kuwa?,su Affy sunce yana bacci"
"E likitansa be dad'e da barin gidan nanba yai mashi allura yasamu bacci"
"Allah ya k'ara masa lapia"
"Ameen ya mujeeb,zo ga abincin me xa'a zuba maka?! sokake kabagarar daxancen cin abincin nasanka sarai"
"Ammi komi ma aka xuba"
"Gashi akwai ingaji (brabusko),kimoniye(farfesun kayan ciki),indalayi,kisre ga miyan kub'ewa,yakuwa,peppered chicken se kunun gyada"
"Abani kisre da kimoniye"
"A'ah Hydar haryanxu kananan da rashin cin abincinka?!kisre kuma dabaya wani rik'e ciki Baride a k'ara maka da kunun ko?!"
"To Ammi"
Zuba masa abincin shidasu Affy tai seda sukaci suka k'oshi sannan su Affy suka tafi wajen malamin dake koya masu karatu a study room... sun d'an tab'a hira da Ammi sannan ya gyara xama a hankali a kuma nutse yace;
"Ammi,munyi magana da baba d'axu"
"To Allah yasa muji alkhairi Hydar"Ammi tace hakan getting more interested ...
"E farko de yafara min magana akan ciwon lupus d'insa wai zeyi murabus thou nibansanme hakan ke nupi ba..sekuma ...,,"
Be k'arasaba Ammi tafara magana ;
"Maganar lupus tabbas munyi dashi,saboda harta tab'a masa kidney ,k'arshen zuwanmu Germany ganin dr,dr d'in yace se anmasa dashen k'oda,kafin ayi dashen k'odar ma se anfaraiwa wajen remedy tukun"
"To Ammi yanzu ni mexanyi anan ko?!"
"Hydar mahaifinka yana nuna maka cewar kaine xaka gaji gadon sarautar "
Seda gaban yareeemah Aliyu Hydar yafa'd'i murya na rawa yafara fad'in;
"Ammi... Ba.. Ga..baa babss da baa Ngari(usman) ba"
"Kaima Kasan usman baxe iya mulkar garin nanba ,tunda bashida lapiar jiki,shikuma babagana shiriritarsa ta xarta yai mulki,kaide d'innan kaine ka cancanta domin kaikafi cancanta daka mulki sarautar borno"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..."shine kalmar da yareemah Aliyu Hydarketa maimaitawa a fili,zuciyarsa kuwa kamar xata faso don b'acin rai
"Se kuma me?"cewar Ammi
"Se maganar aure dayamin"yareemah Aliyu Hydar yace hakan muryarsa na rawa idonsa ya kad'a kai jawur
"To Alhamdulillah tunda yamaka magana dama nima inason jin tabakinka akan wannan batu,yaya kukai dashi?!"
"Ammi nace mashi akwai Wadda nakeso amma bamu gama dedetawa ba"
"Wacece ita?!a'ina take?!yar gidan waye?!"duk lokaci d'aya Ammi tamai wannan tambayr
"Ammi itama student ce a c'an Oxford tana karantar international economic relations ...Yar gidan commissioner of finance ce na kano state..." K'arasa maganar Aliyu Hydar yai tareda yin shiru yana jiran me Ammi xatace
Ajiyar zuciya Ammi tasauke,tad'an jima kafin tayi magana da alama tunani take,sannan tace;
"To yakukayi da baban naku wane hukunci yad'auka?!"
"Ammi cayai xa muyi magana ,amma kafin nan yace modu indimi yasanta?! Nace mashi a'a saboda shi modu a Cambridge yake kuma made bagama dedetawa mukai ba da ita..."
"To ba abinda xance sede nace Allah yaxab'i abinda yafi alkhairi,sannan Hydar duk abinda mahaifinka ya xartar ma'ana kowane hukunci yad'auka akanka,kad'au hakan amatsayin xab'i mafificin alkhairi,kada kabi SON RANKA_ZAB'IN IYAYE shine ZAB'I_ nagari Hydar ,kaita addua Allah yazab'i abinda yafi alkhairi kaji?!"
"Ehh Ammi Insha Allah .."
"To Allah yamaka albarka Hydar.."
"Ameen Ammi godia nake..!"
Yareemah Aliyu da Amminsa sun jima suna hira ,dan k'ararrawar d'akin yareemah Ngari ce ma takatse masu hirar da suke, k'ararrawar amfaninta yana nuna cewar yareemah Ngari yatashi daga bacci kokuma yana buk'atar wani abun.da sauri yareemah Aliyu yamik'e yanupi apartment d'in tilon d'an uwan nasa dasuke uwa d'aya uba d'aya.....!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: 2017, 8:06:21 PM: _Hafsat
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!
(A STUNNING LOVE STORY)
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of expert and perfect writers)
nanahafsat.wordpress.com
Yareemah Aliyu_Hydar natashi daga bacci ya fad'a band'aki yin wanka yad'au lokaci aciki kafin yafuto d'aure da bathrobe dakuma k'aramin towel yana tsane gashin kansa daya kwanta luf kamar gashin jariri,closet d'insa yabud'e yaciro shadda sky blue fesheta yadingayi da turare kamar ruwa sannan yashafa mai dasauran dangin su roll on, bayan yasaka kayan ne yakawo hularsa xanna bukhar dark blue yad'ora akai,safa yasaka sannan yakawo batozzi covered shoe dark blue yasaka bak'aramin kyau yayiba,chapette yagoga akan pink lips d'insa sannan yafice daga d'akin se bulala k'amshi yake ga kyau dayayi kamar wanda xashi gasar xab'en kyau..
Yana futa straight fada yatafi wajen mai martaba,bayan sun gaisane mai martaba yasa aka kawowa Aliyu abinci yaci sannan yad'anyi gyaren murya yafara magana;
"Aliyu..."
Dumm gaban Aliyu Hydar ya buga jin sunan da babansa yakirashi dashi a iya saninsa da Hydar mahaifin nasa yake kiranshi inde yakirashi da Aliyu to maganar daxeyi takai k'ololuwa a muhimmanci..
"Na'am baba" Aliyu Hydar ya amsa kiran da mahaifin nasa yai masa muryarsa har rawa take..
"shekararka nawa yanxu?!"
Seda gaban yareemah Aliyu yafad'i kafin yace;
"Baaba watan gobe xancika talatin"
"Masha Allahu ,To Aliyu magana nakeso muyi dakai ta hankali,sannan abubuwa biyu ne sukasa nace kataho daga makaranta Ina fatan kanajina?!"
Cikeda azama yareemah Aliyu ya kad'a kansa tareda fad'in;
"Inaji baba"
"To Masha Allahu,wato abinda yasa nace kazo abu nafarko de akan maganar murabus danake shirin yine zuwa wani lokaci k'alilan wanda tattaunawar damukai da waziri kenan jia,wanda kaima kasan shekara da shekaru Ina fama da ciwon 'lupus'( lupus is a chronic inflammatory disease that occurs when ur bodys immune system attack your own tissues and organs) sannan abu nabiyu kuma Aliyu inaso kafito da matar aure dan agaskia baxan bari ma ka koma can makaranta ba fyace ansa ranar aurenka tunda karatun naka yazo k'arshe 'modu indimi yafad'amin hakan yace project ma kuke correcting ko?!"
Tunda mai martaba yafara magana gaban yareemah Aliyu Hydar ke fad'uwa,ga wani gumi dake kwarara ajikinsa dukkoda sanyin na urar air conditioner dake turare d'akin... Maganar Mai martaba ce ta tadawo da Aliyu Hydar daga duniyar tunanin daya lula..
"Ko ba haka bane Aliyu?!" Mai martaba yace hakan yana tari ahankali tare da d'an dukan k'irjinsa
"Ha... Hakane baba gyara mukeyi ana i jibi xantaho muke maganar dashi..."
"To hakan yayi Allah yabaku sa'a Ina fatan kayi na'am da duk abinda nace?!"
"Ehh baba"
"To da akwai yarinyar da kuka dedeta ko kuwa?!"
Dumm gaban yareemah Aliyu yak'ara sarawa akaro na biyu,shide yasan duk matan dake mutuwa akansa ba sonsu yakeba sannan basma dayake d'an tausayawa suke magana itama ba wani kwanta masa tai araiba...
"Kayi shiru Aliyu,ko bakada tsayayyiya?!" Mai martaba yace da Aliyu Hydar haka ganin shirun nasa Yayi yawa...
"Baba gaskia bamu gama dedetawa da Ita ba.."
"Anan yerwa fato(maiduguri) take?!"
"A'a baba acan take itama tana second year d'inta amma yar kano ce"yak'arashe xancen yana susar k'eya
"Modu indimi ya santa?!" Cewar Mai martaba
"A'a baba aidayake modu shi a Cambridge yake yanade yawan zuwa school d'in tamu amma bansan koyasantaba dan bamu gama dedetawa ba"
"Too shikenan jeka xamuyi magana"
Rissinawa Aliyu Hydar yasakeyi yafara magana a hankali;
"To baba nagode Allah ya k'ara maka lapia da nisan kwana"
"Ameen Aliyu"
"Baba inaso naje wajen Ammi mugaysa"
"To shikenan sarkin tuk'i seya kaika ko?!"
"Da baba ni nakeso nayi driving dayake nad'an jima banyiba"
"To hakanma yayi,seka dawo..idan kaga sarkin dawakin tsakar gidah ka turo minshi"
"To Ameen baba,nabarka lapia.,xanturo shi yanxu..Yak'ara rissinawa sannan yafice
___Yareemah Aliyu Hydar nafita parking lodge ya hango sarkin dawakin tsakar gidah bashi sak'on mai martaba yai sannan yakarb'i key d'in benz new model yahau yasa key yafigeta se titi, be xame ko'ina ba se damboa road yana zuwa makeken gidan Amminsa guard men suka bud'e mashi tangamemen gate d'in ganin ko waye aciki gakuma tambarin h_r_h sb ajiki amatsayin number motar...
Yana gama parking motar affy da aysa suka fito aguje ganin sa da sukai ta cctv d'in cikin parlorn da suke xaune..
"Baa Hydar"affy da aysa suka k'walla masa kira had'e da xuwa subashi huge mammoth hug har seda yakusa fad'uwa ......!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo:
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE??

(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Wannan shafin nakune yan HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Allah ya k'aro maku hasken ido da d'imbin basira,Allah yabarmu tare
Chapter 4 · 0% Book details