Sashe 48
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ```HASKE WRITERS ASSOCIATION``` _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` ```Wannan shafinma nakine my yahajja,har kullum baxan gaji da sadaukar maki da page ba domin ked in tadabance azuciar nana hafsatu``` *59* *S*hirya shiryan biki aka soma yi both sites hajja gajiram ma tana yi dan taga take-taken babagana nason tona musu asiri a wajan mijin su,hakik'a anyi b'arnar dukiya sosai maimartaba da Mai Alooma har da sarki Aliyu hydar sunyi namijin k'ok'ari domin Modu har hawayen dad'i yayi dan hanashi yin komai suka yi hatta d'inkunan da zasu saka yi musu aka yi d'aurin aure kawai suke jira. Shima yareemah babagana hidimar shi kawai yake yi,komai ya samu bilkisu duk tsadar abu haka zai siya yace na bilkisu ne.sarki Aliyu hydar kuwa tsaf ya shafe babun mahaifiyar shi da 'yan uwan shi kwata-kwata baya tuna su yanzu duk abinda su hajja gajiram suka ce mai shi yake yi hatta maimarbata mahaifinshi yanzu baya mai biyayya kamar yadda yake wa hajja gajiram da hajja yakolo domin yadda ake dirka mai asiri yayi over hakan yasa suka ci galabar shi. Tsaf su Ammi suka shiryo suka dawo palace dan yin hidimar biki,Aysah ce kawai babu tana school. Apartment d'in da take sauka idan ta zo nan suka yada zango kasan cewar sauran sati d'aya kuma za'a fara event gobe shi yasa suka taho. Aunty yaruwaiya ce ta janyo Meenah suka kule cikin wani d'aki babu wanda ya sani,kallon Meenah aunty yarwaiya tayi tare da cewa; Aunty Meenah kin shirya zaki yi abinda na ce miki?idan har zaki yi aunty Meenah yau a yanzu nake so ki fara bana son ki bani kunya da mamaki so nakeyi ki nunawa duniya cewar kema 'ya ce kuma matar sarki mai biyayya da sanin darajar mutane sannan kuma *ZAB'IN IYAYE* ba abun wasa bane please Meenah kice zaki yi... Wiki-wiki Meenah tayi da idanuwa domin tun da aunty yaruwaiya ke mata wannan hud'ubar take jinjina irin iskancin da ake son koya mata,duk da cewar yanzu tana s.s 3 kanta ya k'ara wayewa iliminta ya kuma bunk'asa sannan ta fara sanin meye aure da yadda ake yin shi amma bata yardarwa zuciyarta cewar zata iya yin abinda yaruwaiya take cewa tayi ba,duk da cewar itama yanzu takan yi missing d'in fad'an su da sarki Aliyu hydar sai dai batajin zata iya yin abunda take nuna mata. Aunty Meenah kinyi shiru ko kema baki son mu tsamo Aliyu hydar daga halaka,sannan bakya son ladan da Allah ke bawa mace idan tayi wa mijinta da 'yan uwansa biyayya?! Cikin kid'ima Meenah tace bakin ta na rawa, Aunty yaruwaiya ina so amma gaskiya ni bazan iya ba kuma mugunta yake min indai ya ganni. Tayi maganar tana turo biki wanda ya riga ya zama jinin jikinta,cikin takaici aunty yaruwaiya ta mik'e tana cewa, Wai ke dallah can sai yaushe zaki hankali kisan meye dai-dai da rashin dai-dai? Ke kanki taya aka sameki inda ba aure da tattab'a juna tsakanin miji da mata ba?Ko kin d'auka kina zaune a gida kiyi abinci ki gyara gida kiyi sallah shine kawai aure da musulinci?Toh bari ni zan nuna miki abu na farko da nake son ki fara yi kuma idan baki ba wallahi wallahi zaki ga abinda zan miki wawuya kawai. Figar hannun Meenah aunty yaruwaiya tayi ranta duk a b'ace,ita kuwa Meenah banda turo baki ba abinda take yi a haka suka k'arasa kitchen, fridge ta b'ud'e ta d'akko kankana da dabino b'arewa tayi sannan ta cire kwallan dabinon gabaki d'aya ta had'a tayi blending d'in su,tacewa tayi sannan ta zuba peak milk da sugar d'an kad'an, cikin wani kyakyawan glass jug transparent ta zuba sannan ta kalli Meenah dake tsaye tana kallonta tace, Ki d'auka yanzu kije ki kaimai yana can corridor ko Matar shi Basmah karkiji tsora idan kin ganta ki wuce gurin shi wannan abun dana gaya miki rannan shi zaki gwada yau,wallahi Meenah idan baki yi ba ina kallonki kin dai son banida mutunci gara ma kiyi kuma karkiji tsoron shi kinji ko?Oya d'auki kije 'yar albarka... Hararar tray d'in Meenah tayi kafin ta d'auka tana kunkuni kasancewar tasan halin aunty yarwaiya hakan yasa ba tayi mata gaddama da musu ba tabi ta baya inda ba mutane sosai. Meenah na hango shi taji k irjin ta ya buga da karfi abinda bata tab'aji ba kome hakan ke nufi, a hankali ta k'arasa har inda yake bakinta d'auke da sallama kanta a k'asa tana kallon tray d'in hannunta, jin sallama ne yasa shi d'agowa a hankali cak ya tsaida idanunshi akan fuskar Meenah,da sauri ta kalli bayanta dan ganin ko aunty yaruwaiya na kallonta ganin ba kowa yasa ta k'arasawa inda yake fuskarta a shagwab'e ta dire mai tray d'in a gaban shi.juyawa tayi tana kallon k'ofa nan tayi ido hud'u da aunty yaruwaiya tana kara zare mata ido tayi saurin juyawa a fili ta furta Kalmar, Wayyo Allah na shiga uku.. Kallonta ya kuma yi a yatsine tamkar be santa ba ta kalleshi itama kamar gaske tace, Habba rankashidad'e har zuwa aka yi aka ce ma munzo amma ko kaje sai ka zauna anan kai kad'ai, anyway ni gani nazo harda drink na kawo maka saboda ka rage kad'aici.. Tayi maganar tana tsiyaya mai a k'aramin cup mai matukar kyau wanda mahad'in jug d'in ne,sai data zuba sannan ta mik'a mai yabi hannun da kallo wanda yasha jan lalle harya fara zama kalar maroon a yatsun hannun, ganin yak'i karb'a yasa ta waigawa still aunty yaruwaiya na kallonta sai ta kuma matsawa kusa dashi wanda har tana tab'a kafarshi daya mik'ar da ita. Haba rankashidad'e wai kurma ka zama ne yau naji baka magana? Ni dai zuwa nayi in tayaka hira amma naga kamar baka so. Ta fad'a kamar wata babba,can taji yayi magana kamar baya so, Ke!Waye ya turo ki nan gurin?! Saurin kallon shi tayi ganin kamar ya harbo jirginsu tayi saurin juyawa bataga kowa ba hakan yasa ta kuma kura mai ido wanda shima ita yake kallo, matsawa tayi har suna gogar kafad'an juna wannan karan da gaske take yi bawai teaching d'in aunty yarwaiya bane dai-dai kunnan shi ta rad'a mai, No body kawai nazo ne, toh ai nima matarka ce kuma aunty yaruwaiya tace zan iya tab'aka harma lada za'a rubuta min. Bakinta yabi da kallo wanda yasha pink d'in janbaki yayi kyau gashi sai motsashi take yi,hannun shi yasa ya damk'i gashin kanta sannan ya matso da fuskarta sitin tashi har hancinsu na gogar na juna sannan ya sake maimaita mata kalmar d'azu, Waye ya aiko ki nake tambaya?!trouble maker kawai Meenah ta saki k'ara a hankali tana rintsa idanuwa saboda zafi ya kuma ja mata cikin axaba ta zura hannunta ta sakalo wuyan shi tare da saurin fad'awa kirjinshi tana mai karar zafi,ta baya Basmah ta biyo nan idanunta suka yi mata mugun gani kasan cewar idan ta baya ka taho zaka zata mouth to mouth kiss suke yi,wata irin kara ta kurma tare da rufe idanuwanta da hannunta, aunty yaruwaiya na gani ta tuntsire da dariya ita sam tama manta da cewar Basmah zata iya zuwa wajan amma hakan sai ya Kara mata jin dad'i domin tasan yau ta tunawa Basmah cewar akwai wata Matar fa bayan ita. A razane suka saki juna nan Meenah taga Basmah tayi katuwa da ita ga uban kumatu da tayi sam bata ganeta ba ta kalli Aliyu hydar cikin b'ata fuska dan har lokacin kanta be dena zafiba tace, Ya Aliyu wannan wacece?! Ta bayanta taji Basma tace, Uwarki ce ke bakida kunya zaki zo nan gurin har kina bashi baki yana tsotsa? Toh na rantse da Allah... Bata k'arasa ba Meenah ta mik'e tare da kama shamilallan kugunta tana girgiza shi tace, Wallahi ba dai uwata ba dan gobema zata zo sai dai ni ki zageni haka kawai,toh...toh mai ai Yaya nane kuma uhmm...uhmm mij....mijina ne kuma. Amina...?! Basmah ta furta dan duk basu san juna ba tunda Basma ba zuwa gidan Ammi take ba sai dai kullum tana wajan su hajja gajiram dan gani take sonfi kaunarta akan Ammin. Yes thats ma name. Meenah ta bata amsa tana murgud'a baki,kallon Meenah sarki Aliyu hydar yayi cikin b'acin rai yace, Ke!Matar tawa kikewa wannan farin da ido?! Da sauri itama Meenah ta kalleshi tana turo baki tace, Toh..toh ai dai nima matarka ce ehe. Zaune ya tashi ganin haka yasa Meenah kwasa da gudu tana kiran Ammi har ta shiga kofa da aunty yaruwaiya taci karo nan da nan tayi saurin fad'awa jikinta tana sauke nishin wahala hannunta dafe a kirjinta,cikin jin dad'i aunty yaruwaiya tace, Kin min daidai tawan duk da banajin abinda kuke cewa amma aikinki yayi kyau zoki wuce sauran na gobe tawan ki denajin tsoro ko shakka kinji ko?! Meenah jin an yabeta yasa ta bud'e hakora tana dariya sai wani farin ciki take yi sannan suka shiga cikin sauran dangi aka ci gaba da yin komai tare. Basmah kuwa ganin Meena tabar wajan yasa ta kallon sarki Aliyu hydar tare da juyawa da sauri tana matsar hawaye, shima mik'ewa yayi kamar an tsikare shi yana kokarin shiga kofar parlor yaga Modu ya tare hanyar da zai shiga fuskar shi a had'e yana mai wani kallo,kasan cewar babu bafadai a wajan yasa babu wanda ya hana Modu yin hakan, Kallon sarki Aliyu hydar yayi tare da nuna takaicin shi afili yace, Kabani kunya uwa uba kuma mamaki,tun kana ciki suke d'awainiya dakai har ka girma kayi wayo suka yi maka aure sannan baba ya sauka daga kan mulkinsa ya baka duk dan ganin da suke maka mai hankali kuma adali ashe nan gaba zaka nuna musu iyakar su,wallahi nasha mamaki sannan kuma kabi a hankali domin alhakinsu a kanka bala'ine a gurinka, idan kaga dama kaje ka gaida mahaifiyarka idan baka ga dama ba kabi matarka ciki. Modu na fad'a ya bashi hanya,ga mamakinsa gani yayi ya shiga ko kallanshi beyi ba,girgiza kai Modu yayi tare da cewa, Allah ya kubtar dakai domin an saka a halaka mr arrogant. Shima juyawa yayi yafita be sake bi ta kanshi ba, washegari 'yan yola suka zo harda aunty Maijidda da aunty yafendo dasu yakaka su gidado dasu