← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 107

Sashe 45

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ```HASKE WRITERS ASSOCIATION``` _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` *```57```* *```shehuri```* *S*ai wajan k'arfe 10:00pm sannan maimartaba Aliyu hydar ya samu damar komawa apartment d'in shi,wanka ya fara yi sannan ya sanya kaya marasa nauyi,parlor ya koma yana jiran zuwan Modu dan yanzu suka gama waya yace mai gashi nan zuwa. Zaman jiran Modu yayi tayi bunu-bunu Basmah ta leko ta gani ko sunyi sun gama amma sai taga Aliyu hydar kad'ai a zaune yana duba wani d'an k'aramin littafi na addu'o'i *Fortress of the Muslim*, tana k'ok'arin fitowa taje wajan shi sai kuma taji muryar Modu a cikin parlorn ya shigo yana cewa, Kan bala in can, aure me gyara mutane, kai dama haka ka zama?Toh wallahi an gama dakai guy domin rawanin nan da ake sargafa ma b'oye maka komai yake yi kai zuki Masha Allah... Modu ya fad'a yana k'arewa Aliyu hydar kallo domin gani yayi kyawunshi ya karu ga wata irin kamala data k'ara baibaye shi.Sarki Aliyu hydar ya shafa hab'arshi yana sakin wani kayataccen murmushi,zama ya gyara yana kallon Modu yace, Kaga guy nifa ba surutu nace kayi min ba so nake ka gaya min ina ka tafi kayi min yaji...?! Guy naje neman aure ne kuma na samu. For real?! Eh mana dama ai na gaya maka bazan kuma ne manka ba sai na samo auran Kiara, toh baba ya yadda kuma insha Allahu soon zaku sha biki. A mamakin ce sarki Aliyu hydar ya kalli Modu jin abinda ya fad'a, kallon shi yayi cikin sonjin k'arin baya ni Modu yayi dariya yana cewa, Kayi mamaki ko? Toh ai ba abin mamaki bane domin Basmah da Kiara ba d'aya bane,ita Kiara dama a haka aka haifeta cikin addininsu,sab'anin Basmah da koyi takeyi da d'abi'unsu shi yasa kasamu matsala wajan neman auranta a wajan baba,ni kuma bayan soyayyar Kiara akwai jahadi tare da d'inbin lada mai yawa agurin Allah idan har ta musulinta sanadiyar auran mu. Jin-jina kai kawai sarki Aliyu hydar yayi dan ba k'aramin mamaki yayi ba ta yadda maimartaba maimurabus ya amince da batun Kiara,sun dad'e suna hira har wajan 1:00am sannan Mudo yayi mai sallama ya tafi sai dai har suka gama hirar be gayawa Aliyu hydar cewa shima za'a had'ashi da wata ba dan ya tabbatar idan ya fad'a sai yayi mai dariya. Kwana biyu tsakanin maganar babagana da mahaifinsu yana jiran ya karajin an kirashi amma shiru,ganin baza'a kara nemanshi bane yasa shi yau ya shirya cikin wani tsadaddan yadi mai matukar kyau ya sanya direct ya wuce gidan su billy,cikin sa'a kuwa yana zuwa ya tarar da mahaifinta zai fita. Da sauri babagana cikin ladabin da baima san yana dashi ba ya fito daga mota ya k'arasa wajan shi tare da yi mai sallama, gaisawa suka yi cikin mutunci sannan babagana yace, Baba dama magana nake so muyi. Toh toh shikenan mu k'arasa daga zaure ina tunanin hakan yayi aiko?! Eh baba yayi. K'arasawa suka yi cikun zauran gidan sannan babagana ya kuma gaida mahaifin bilkisu har k'asa kafin ya fara magana; Baba dama nine wanda yake son auran bilkisu, dan Allah baba ka amince min inasonta nayi alkawarin rik'e maka ita da gaskiya da rikon amana, zan iya auranta a yadda take baba sannan zan nema mata magani aduk inda yake baba amincewarka nake so, domin mahaifina yace sai kun yadda tukunna Kafin Abban billy yayi magana sai ga su billy da kanwarta zasu fita, tsayawa billy tayi kurum tana kallan yareemah babagana ko kiftawa bata yi, gaban shine ya fad'i a tunanin shi ko tona mai asiri zata yi dan shi besan hajja gajirim tasa an gusar da hankalinta akan shi ba. Saurin sunkuyar da kai yayi k'asa yayin da kirjinshi ke bugawa tsoran shi d'aya karta fallasa abunda yayi mata gashi yanxu an kara zazzaga mishi wutar kaunarta,lallai billy the magnificent domin har wani sauk'in ta yak'e ji cikin magudanar jinin shi. Abba ne ya kalleta tare da yin murmushi yana shafa kanta yace, Bilkisu ko kin sanshi kike ta faman kallonshi keda ko had'a idanu da namiji bakya yi?! Bata yi magana ba tana ta kallon yareemah babagana,ganin haka yasa abba cewa, Zainab ina zakuje?! Ya tambayi k aramar wadda suke tare da bilkisun,ledar hannunta ta nuna mai tana cewa, Abba Umma ce tace muje mu kaiwa yakaka kubewa ce. Kai kurum ya jin-jina sannan yace, Toh bilkisu zo ku tafi aikenku kuyi sauri Ku dawo duk wanda ya kiraku karkuje Ku tafi. Fita suka yi amma duk da haka billy bata dena waigen yareemah babagana ba,ganin sun kule yasa shi sauke wata katuwar ajiyar zuciya sannan suka ci gaba da magana. Abban billy yace, Toh yareemah naji bayaninka amma ka bari zanje can fadar dan muyi magana nida mahaifinnaka insha Allah komai zaizo da sauk'i Jin haka yasa babagana zura hannu cikin aljijun wandon shi ya zaro kud'i wanda bemason adadinsu ba ya mikawa abban billy sai godiya yake abinda be tab'a yi ba kyauta da godiya,nan abban billy yace a'a bazai karbi ko kwandala ba amma yareemah babagana ya ajiye mishi ya fita da Sauri yana jin farin ciki.Ba yadda mahaifin billy yayi hakan nan ya d'auki kudin yaje yana bawa matar shi labarin yadda aka yi,itama addu'a tayi tare da cewa idan da alkairi Allah ya had'a idan babu Allah ya had'a kowa da rabansa. Sati d'aya wani lokaci Basmah ta shirya cikin shiga ta alfarma,lokacin sarki Aliyu hydar na fada ita kuma ta aika aiyi mata iso wajan maimartaba mai murabus cewar zata zo tana san magana dashi, bayan an sanar mai yace toh yana sauraran zuwan nata,cikin ladabi ta shiga sitting room d'in nashi yana kishin gid'e jikin wani tum-tum babu kowa sai shi ta samu waje ta zauna kanta a k'asa jin sunan da yakirata dashi tace, Sannu baba barka da rana anyini lafiya?! Lafiya lau Maryamu ince dai lafiya lau kuke ko babu wata matsala ko?! Lafiya lau baba dama akan Muhammad ne wato Modu,baba akwai wata friend d'ina da suka dad'e tare dan tunkafin musan shida maimartaba 'yan uwane suke tare, toh kuma baba ta riga ta fad'a a gida tana da wanda take so wato shi sai yanzu kuma katsam ya fara nuna mata cewar shi yanzu kamar dai so yake su rabu kuma sunfi 3years suna tare shine nace to bari zan gaya maka inyaso sai aji inda matsalar take. Mamaki ya kama maimartaba maimurabus zama yayi sosai yana kallon Basmah yace, Ya sunan yarinyar?! Basmah cikin zakuwa tace, Sunanta layla baba. Ashsha ashsha kenan dai idan na fahimta ya yaudareta kenan ko? Dan ni yazo ya sanar min da cewa yana son auran wata yarinya sunanta Kiara amma ba muslma bace, yanzu haka ma na tura mutum biyu sun had'u da can kawunsu na yola Mai Alooma Ghaji dan suyi bincike daga nan sai a fara shirya-shiryan aure Ashe yana can ya yaudari yarinyar mutane,Shikenan Maryamu tashi kije zan yi magana dashi Mudon dan naji daga inda matsalar take. A hankali Basmah ta tashi tana yiwa maimartaba maimurabus godiya sannan tayi mai sallama ta fita,tana fita ta kira layla akan cewar tayi addu'a ta kwantar da hankalinta.Shi kuwa maimartaba maimurabus waya ya d'auka ya kira Mudo, ba b'ata lokaci sai gashi fuskar nan wasai cike da farin ciki ya kalleshi bayan ya zauna baban yace, Mommodu wacece kuma layla....?! Daram zuciyar Modu ta harba da k'arfi cikin razani ya kalli baban yana kwalalo idanuwa,baba na ganin haka ya gazgata maganar Basmah dan haka ya gyara zama danjin ta bakin Modu wanda keta faman soshe-soshe. Ina jinka kayi shiru. Cikin rashin gaskiya Modu yace, Baba ex girlfriend d'inta ce ita. Murmushi ne ya kwacewa maimartaba cikin murmushin ya maimata Kalmar a fili, Ex girlfriend Mommodu?Saboda ka samu Kiara shine zaka barta ko kuma dai wani abun tayi maka?! Wallahi baba d'abi'unta ne basu yi min ba,akan idona na ganta da wani arne suna rawa agaban mutane kuma. Shine dalilin da yasa ka dena sonta?! Eh baba." Murmushi Maimartaba yayi sannan yace, Toh idan banda abinka ai da sai kayi k arin tsamota daga inda take k arin fad'awa, tunda dai da kana sonta toh yanzu ma ka daure ka cika ladanka itama ka aureta dan kar a barta ta shiga wani halin, kaga barinta da zakayi bamusan kuma abinda zata fad'a ba kayi jahadi ka dad'a da ita kaga kanada d'inbin lada a gurin Allah,kaga dai itama Basmah tunda aka aureta dawa ka tab'a ganinta? Babu sai dai mijinta toh kaima kayi jahadi zanyi bincike akanta idan har an dace toh inason ta zama wadda itace *ZAB'IN MU* da muka yi maka tunda kaima an baka *SON RANKA* ko ba haka ba Mommodu?! Tunda maimartaba ya fara magana komai na d'aukar magana dake jikin Modu sai da ya tsaya dan haka beji karshen maganar ba sai jikin shi dake faman rawa tamkar wanda shocking ya Kama. Tashi ka tafi Allah yayi muku albarka,insha Allah bikin bazai wuce one month ba za'a had'aku da kai da babagana dan shima munyi magana da mahaifin yarinyar. Tashi yayi yabar gurin ko ganin gaban shi bayayi har ya bigi falmata be kulaba sai jin tsakinta yaji, apartment d'in su na Aliyu hydar ada nan ne yake a matsayin inda Modu ke zaune dan haka can ya nufa zuciyar shi na zafi yana tunanin yadda aka yi har baban yasan tsakanin shi da layla. Bayan 'yan binciken London sun dawo ne aka kuma tafi gidan su layla, itakam an samu matsala dan iyayanta basu yadda ba sunce bazasu had'a yarsu kishi da wadda ba musulma ba, ganin yadda laylan ke kuka harda su suma yasa suka amince ba yadda zasu yi a gurin itama aka biya kud'in nagani inaso aka tsaida biki one month dukan su. Hajja gajirim kuwa hauka takusa yi jin cewar an samowa yareemah babagana auran bilksu, tsine tsine ta dinga yi harda wad'anda sukaje nemo auran babu wanda besha zagi ba, shi kuwa yareemah babagana yana wajan parking lot taje ta shak'i wuyan shi wai wallahi sai yace ya fasa ya rasa wadda zai aura sai 'yar matsiyata wadda ta gama gararanba a titi, ya kalleta yana kecewa da wata shegiyar
Chapter 45 · 0% Book details