Sashe 35
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nanahafsat.wordpress.com This chappy is all urs dota *billy s fari*I love you beyond your wildest expectations love and endless amounts of blessing momma hearts you muchos.......! *51* *D*aga nan taro ya fara watsewa kamar yadda yareemah Aliyu hydar da Basma suka je a mota d'aya yanzu ma haka aka yi Modu indimi ne ke jansu yayin da layla ke gefen shi mamaki layla keyi ganin yadda Oud d'inta keta faman kakkauda kanshi tamkar baya son ya dinga ganinta,ji tayi kamar ta fasa ihu dan takaici sai dai ba yadda za tayi amma cikin ranta fal yake da d'inbin tambayoyi game dashi. A baya kuwa Basma ce ta lafe jikin yareemah Aliyu hydar shi kuma sai faman murza yatsunta yake jikin shi duk yayi sanyi domin ya hango lokacin da hajja gajiram ta dafe kai tana cizon lips har ta fita daga cikin taron shi kuma yasan farin ciki ne bata yi na jin cewar za'a bashi sarauta gobe sai kace duniya aka ce za'a bashi,d'an k'aramin tsaki yaja wanda bema san yafito fili ba sai da yaji Basmah ta d'an d'ago tare da kafeshi da idanuwa alamar sonjin k arin bayani. Murmushi ya sakar mata tare da kuma maida kanta saitin chest d'in shi, har suka k'arasa cikin shehuri babu wanda yayi magana suna fitowa Modu yayi saurin shiga cikin abokan su yayin da layla jikinta yayi sanyi ta rab'a jikin Basma inda aka shigar dasu sashan Ammi, Suna zuwa aja janye Basma cikin bathroom aka shiga da ita wani ruwa ne a cikin jacuzzi da wasu fulawowi a ciki nan aka ce ta shiga tayi wanka, kamshin ruwan da dumin shi ya sanya Basma yin Bacci a ciki dama duk ta gaji ta sha wahalar zama, muryar wata mata taji hakan ya sanyata saurin tashi tayi wanka ta fito, cikin wani guri aka kuma sanya ta shima sai tada kamshi yake aka gama turareta kafin a fito da ita mai makeup aka sanya tayi mata sannan ta sanya bridal gown d'inta tayi masifar yin kyau jikinta sai kamshi yake tashi irin na turarukan Kanuri, farfesu Ammi ta bata wanda da kyar Basma ta iya sha sabida na magani ne ta shanye ruman daga nan aka wuce da ita wajan Maimartaba inda ya sanya mata albarka tare da yi mata nasiha sosai daga nan aka tafi apartment d'in hajja yakolo. Da kyar hajja yakolo ta samu ta seta nutsuwar zuciyarta kafin ta yiwa Basma 'yar nasihar da bataje zuciba daga na tana gamawa suka wuce na hajja gajiram,tararwa suka yi bata nan zama suka yi amma shiru shiru bata dawo ba suka tashi aka nufi katafaren apartment d'in sarkin gobe wato yareemah Aliyu hydar, abin sai dai ace Masha Allah domin tsayawa bada labari kauyanci ne kawai dai reader's kowacce ta kissima a cikin ranta, part biyu ne duk iri d'aya sai dai guda d'ayan ba'ayi mai paint ba na Meenah kenan kasan cewar ita ba alokacin zata tare ba an barshi ne sai gabannin zata tare itama. A can k awayen amarya suka kwana kasan cewar al'adar sukenan, Meenah kuwa ciwon kanta be barta yin komai ba har washe gari, *Safiya ta gari* Misalin k'arfe 9:30pm aka yiwa yareemah Aliyu hydar nad'in sarautar sarkin BORNU,taron daya tara manyan masu muk'amin ciki da wajan Nigeria ciki kuwa harda shugaban k'asa me ci a lokacin (president), A gurin aka yiwa yareemah Aliyu hydar nad'in kamar yadda aka sabayi seda aka warware nakan mai martaba sannnan aka nad awa Aliyu Hydar shi sannan governor ya sargafa mai sandar girma kawai sai ya saki kuka wanda ba zai iya cewa ga dalilin yin shi ba. A hankali ya juya yana kallon Mahaifinshi dake zaune sai faman murmushi yake mai yana jinjina kai alamar tabbatarwa,alama yayi mai da hannu cewar ya share hawayan ya dake karya bashi kunya yareemah Aliyu hydar ya goge sannan yayi k'asa da kanshi be sake d'agowa ba har aka kammala komai aka fara watsewa sannan shi kuma aka jashi zuwa wani extra room.... <><><><> A fusace hajja gajiram ta shiga cikin bedroom d'in yareemah babagana, zaune ta ganshi ya kifa kanshi a gefen bed d'inshi sai ajiyar zuciya yake saurin matsawa tayi wajan shi cike da tausayi ta d'auka shima rashin samun sarautar ne yasa shi kuka kanshi ta fara shafawa a hankali cikin sigar lallashi ita da tazo da masifa tace mai, Duk laifinka ne babagana me yasa tun sanda nake binka akan kazo mu had'u ayi duk yadda za'ayi ka samu ka d'are kan kujerar mulki amma kak'i?sai yanzu da komai ya riga yazo k'arshe sannan zaka zauna kana yiwa mutane kuka Shiru yareemah babagana yayi zuciyar shi tamkar zata fito yafi minti ashirin yanayi kafin ya d'ago ya kalli hajja gajiram; Mami yazanyi?mami bata sona,bata son ganina kojin muryata na zame mata tamkar dodo me neman rayuwarta, idan ta ganni Mami guduwa take yi wallahi ina sonta idan ban aureta ba Mami mutuwa zanyi zaki rasani Kuma fashewa yayi da kuka yayin da hankalin hajja gajiram yayi mugun tashi, kallon shi tayi cike da mamaki jin maganar dake fitowa daga bakin d'an nata da takeji dashi take kuma son farin cikin shi,hankalinta a mugun tashi tace mai, Yareemah ban fahimci inda maganar ka ta nufa ba,kana nufin ba bak'in cikin rashin samun sarauta kake yi ba?! Yareemah babagana ya kad'a kai alamar ehh sannan yaci gabada kuka, a hassale hajja gajiram ta ce, Sakarai kawai dama mace ka zauna kana yiwa kuka? Wallahi ka bani kunya da mamaki kamarka kana yiwa mace kuka sai kace yaron da aka doka beson laifinshi ba,toh 'yar gidan waye me takeji dashi da har zata kalleka tace bata sonka harma yasa ka shigo d'aki kana kuka....?! Kusa da ita ya koma ya zauna,hannunta ya kama ya damk'e cikin nashi kamar mutumin kirki yayi k'asa da kanshi, Mami bilkisu,wallahi idan ban aureta ba toh kema rasani zaki yi,itace farin cikina,jin dad'i na walwala ta da duk wani motsina in fact Umma I can t do with out Bilkisu Mtwww hajja gajiram taja wani k'atan tsaki tamkar bakinta zai ciro cikin takaici ta mik'e tsaye tare da cewa, Kaima baka santa tunda na tambaye ka 'yar gidan waye a garin nan ko ince cikin fad'in Nigeria amma kayi shiru sai wani cewa kake min Bilkisu,idan ka tashi sanar dani waye uban.... Bata k'arasa ba taji yace, Mami wannan yarinyar cefa wadda kika...kika ganmu kwanaki anan d'akin. A razane ta juyo tana mai wani mugun kallo,shima had'e rai yayi ganin zata kawo mai matsala,yadda taga yayi ne yasa ta sassauta fuskarta dan tasan zai iya sauke mata nashi rashin kunyar tace mai; Kai yanzu babagana akan wannan watsatsiyar yarinyar zaka zauna kana kuka?! No Mami ba watsitsiya bace nine nan watsatse domin nina b'ata mata rayuwa, wallahi Mami idan baki sa an nemomin auranta ba zan bar muku gidan ba zaku sake ga..... Da sauri hajja gajiram ta rufe mai bakinshi tana faman share hawaye,ita kam tashiga uku daga wannan sai wannan yanzu komai babu nasara indai tayi sai ya lalace ko wani abun daban ya sameta ko wani nata, Kace bata sonka bata son ganinka toh ya kake son ayi maka yareemah?! Tashi yayi tsaye tare da yace, Kizo muje gidan kiyi musu bayani nasan zasu yadda su aura min ita koda bata sona idan yaso in munyi aure zata soni daga baya. Toh naji zanje amma ka bari sai komai ya nutsu sannan sai muyi maganar. Hajja gajiram ta fad'a tare da ficewa daga d'akin dan karma ya kuma yi mata magana. Komawa yayi ya zauna zuciyar shi na kara cusa mai kaunar Billy yana jin tamkar zai mutu saboda rashinta a kusa da shi,shi kam ya d'and'ano wa kanshi bala'i dan tun ranar da yayi raping d'inta be kuma samun nutsuwa ba. <><><><><> Yareemah Aliyu hydar kuwa bayan ya d'an huta aka wuce da shi cikin gida tsakanin shi da Modu sai dai kallo daga nesa kasan cewar manyan mutane ne ke rik'e dashi,a harabar gidan aka tsaya nan fa yaran gida da jikoki harma da tattab'a kunne duk suka fito anata taya yareemah Aliyu hydar murna, Ammi kam kasa fitowa tayi sai tayi alwala ta fara nafila tana yiwa d'annata addu'a da fatan alkairi ya kareshi duk sharrin mutum da aljan gabas da yamma kudu da Arewa, Kutsawa kawai take har saida ta samu ta ganta a tsakiyar su,hannushi ta rik'e tana girgiza shi alamun ya kalleta a hankali yakai idanunshi kanta yayi saurin zare idanuwa yana kallonta.Murmushi tayi mai sai d'age kafa take tana son yin magana a kunnanshi, Wallahi kayi kyau ban ganeka ba sai da gid'ad'o ya nuna minkai... Kalle kalle yareemah Aliyu hydar ya fara yi a hankali dan mulkin ya k'ara karfi sarautar ta fara aiki kokarin zame hannunshi yayi daga nata amma ta damke sai dashare mai hakora take,yakaka ce ta fara ganinta taje ta shunowa aunty yafendo gabaki d'aya mamaki ya rufesu yayan ta Ahmad suka hango aka gaya mai alama yashiga ya fito da ita aunty yafendo tayi apartment d'in Ammi da ita, Sakarai kawai kefa yanzu ba yarinya bace kin zama matar shi amma kike wannan sakarcin daga samun lafiyarki." Yakaka ta fad'a cikin k uluwa bayan sun shiga cikin bedroom,kallonta kawai aunty yafendo tayi ganin sai k uni take tasa aka nemo mata su Affy da Aysa ta had'a su tare sannan tace karsu fito sai an gama komai, Wajan k'arfe 10:00pm aka yiwa yareemah Aliyu hydar rakiya zuwa apartment d'in su,daga bakin k'ofa abokan shi suka tsaya Modu ya rab'a dai-dai setin kunnan shi yace, Mr arrogant!Yau girma biyu ya hau wuyanka,idan ka shiga ciki ka ajiye duk wani abu ka rungumi matarka idan ka fito sai ka maida rigar sarautar ka dan mata ba'a yi musu mulki a cikin gida,ka more kafin zuwan Meenah Modu na fad'a ya juya da sauri yana mai dariya har da 'yar kwallah ya share saboda gani yake kamar sun rabu,shi kuwa yareemah Aliyu hydar lumshe idanuwa yayi sannan ya doshi cikin parlon wanda keta tashin k'amshi tamkar anyi b'arin turaruka, a center corridor ya tsaya dan besan inda zai nufa ba kasancewar besan yadda tsarin gidan yake ba,upstairs ya nufa kai tsaye ya shiga wani d'aki yana b'ud'ewa ya hangi Basma