← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 107

Sashe 92

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kamar wadda xa a kwace masa ita cikin muryarsa daddad a yace, Ammi.... Rufe idanuwa Ammi tai ta bud e baki hangame ta dube shi tana murmushi kafin tace, Alhamdulillahi..Allah kaine abun godia Tana k arasa fada ta fuskanci gabas tai sujudish shukru wato sujjadar godia ga Allah.. Ngari.. cewar Aunty yaruwaiya cikeda dadi tasake cewa, You can talk again...Alhamdulillah what a blessing! tafad a tana hawaye Murmushi kawai yayi mata kafin ya sake rungumo Ammi kowannensu yana hawaye ahankali Ngari yasa Ke cewa, But Ammi nayi mafarki mara kyau.. Akan menene Ngari?! cewar Ammi fuskarta cike da damuwa... Girgiza kai yayi kafin yace, It was about my past..Ance ba kyau mutum ya fad i mafarkin dayai mara kyau..Kede kawai kicigaba da mun addu Insha Allah Ngari Allah xe cigaba da kareka mugun nufin su yakoma kansu Hannun Ammi ya d auka ya d ora akan bakinsa yana hawaye,cikin rawar murya yace, Ammi ki tashe ni daga mafarkin dana keyi Ammi..Dagaske ni ne nake magana bayan kusan shekaru talatin bana yi?! Girgiza kai Ammi tai hawayen dadi se kwaranyo wa yake a fuskarta, Ngari ba mafarki kake yi ba kai d inne kake magana Allah yakawo k arshen komi kasan dama duk runtsi to fa akwai dadi a gaba a kai yayi yana murmushi kafin ya dubi aunty yaruwaiya dake hawaye dan murmushi yai cikin sanyayyar muryarsa yace, Aunty yaruwaiya kela yasken(kitson gaba)ki yayi kyau Dan dukan wasa takai masa tana goge hawayen dake kwance akan fuskarta,hannuwanta tasa tana taba gashin kanta, Dankari yo aini banma san ba dankwali akai na ba oh ni rukayyah da wannan uban daren.. Daria suka saki dukkan ninsu sannan daga bisani tai musu sallama tafice da sauri don tsarkake kanta Ammi ta jima awajen Ngari har asubah tatemaka mashi yai alwala ya tsarkake jikinsa da ruwan adduoin ganyen magaryar da ake mashi bayan yayi azkhar na subhi, Seda Ngari yace taje ta huta dakyar tafice ta ta koma sashenta sosai yanxun takeji kamar and au ke mata wani gundumeman dutse azuciyarta don dadi..ya jima yana addu oin kariya kafin daga bisani yakoma ya kwanta don sam beyi wani baccin kirki ba.. Wajan misalin k'arfe 6:30am Aliyu hydar ya d'auki wayan shi,layin Ammi ya shiga nema ta dad'e tana ringing dan har sai da ta kusa tsinkewa sannan yaji ta d'aga tare da yin sallama kai daga jin muryarta kasan tana cikin farin ciki. cike da ladabi kamar yana gabanta ya gaishe da ita sannan yace. Ammi yanzu zan shigo nasan anjima bazan samu ganinki ba. Ammi tayi murmushi muryarta a sake fiye da yadda ya saba jinta yaji tace mai, Toh rankashi dad'e ai ni na koma gida tun jiya yanzu haka inada babban albishir da zanyi maka amma sai ka fara bani tukwaici tukunna. Murmushi sarki Aliyu hydar yayi tare da k'ara manna jikinshi dana Meenah yace. Ammi ai duk duniya banga abinda zan d'aga nace zan baki shi ba a matsayin tukwaici sai dai nace Allah ya kara kauna tsakaninki da babana. Ammi tayi dariya mai sauti sannan tace, Amma hydar wai tukunna ma ina 'yata take. Ido suka had'a da Meenah wadda ke faman kad'a mai kai alamar karya ce suna tare yayi murmushi tare da shafa gashin kanta yace, "Ammi gata nan in bata ku gaisa..?! Ya tambaya yana kashewa Meenah ido d'aya tayi kicin-kicin da fuska dan baza ta iya yin magana ba gani zata yi kamar Ammi zata gano abinda suka yi,cikin sa'a kuwa taji Ammi tace. A'a kabarta har sai lokacin da zata d'auki waya ta kirani kamar yadda kayi. Tayi maganar tana dariya shima yayi murmushi sannan yace, Toh Ammi albishir d'in da za'a gaya min fa?! Ammi ta kuma murmusawa tare da cewa, Baah ya warke yanzu da bakinshi ras zan baka shi ku gaisa amma sai anjima dan sai ya fara yiwa babanku tukunna. What? Ammi Alhamdulillahi bari na taho ni yanzu, ash sorry Ammi babah yana cikin damuwa ina jin ma yanzu haka k'ila a had'a meeting na gaggawa anan cikin shehuri. Sarki Aliyu hydar ya fad'a cikin tashin hankali Ammi tace, What's wrong hydar?! Kasa fad'a yayi domin maganar babbace baxai iya gaya mata ba dan haka yace, Sorry Ammi but...but bazan iya fad'a ba da bakina. Ok tohm Allah ya kyauta bari na kirashi naji. Bata ko bari sunyi sallama ba tana kashe wayar tana kokarin kiran mijin nata sai ga yayya gumsu ta shigo d'akin ta kalli Ammi tare da cewa. Baba ya aiko da mota wai duk muje baki d'aya,har baah Ngari a tafi dashi. Kirjin Ammi ya buga hankalinta ya tashi ta fara tunanin abinda ke faruwa, mik'ewa tayi gaba d'ayan su suka shiga mota suka tafi ga murnar baah Ngari ya samu sauki ga kuma fargabar kiran da aka yi musu na sassafe wanda basu san kona menene ba har suka shiga cikin shehuri babu wanda ya gano kiran da ake yi musu.. *KATSINA STATE* *KURFI LG* Tun ranar da baba maigadi da haj salamatu suka tafi kurfi take xaune agidan yayar sa akauyen na Kurfi kasancewar shi Baba mai gadi bashida aure matar sa ta rasu shekarun baya kuma Allah be bashi arzikin yaya ba harta rasu.. A can wata unguwa yayar Baba mai gadi take xaune da mijin ta amma yakanyi tashi xuwa gari gari yayanta kuwa duk manya ne kowannensu yayi aure Toh anan haj salamatu ta sauka kan Allah yasa ta gano gidan tsohon mijin nata da yayanta domin ta rokesu gafara ko Allah xesa su yafe mata.. Zaune suke itada inna hab i yayar Baba maigadi akan wata jemammiyar taburma suna tsince shinkafa y ar gwamnati kallo d aya xakaiwa haj salamatu kagane yanxun duniya bata damawa da ita gaba d aya ta fice a hayyacinta ko kadan baxaka iya kawowa itan bace.. Bushe shinkafar inna habi tai tana kakkabe xaninta da alama ta gama, Tsiyata da hinkafar hausa akwai aikin gyara dubi heda nakusan b ata awa biyu fa ina gyarenta.. Dan murmushi haj salamatu dake gyaren wake agefe tai kafin tace, Haka take kam in baka gyara taba kuwa da kyau kaita tauna b untu.. Sallamar Baba maigadi ce ta tsaidasu daga maganar da suke,shigowa yai hannunsa d auke da fatanya dayan hannun kuwa leda ce baka d auke da salak dasu tumatir agefe ya ajiye yana goge gumin dake gangarowa a fuskar sa, Sannu Danjuma..Neman halal da wuya bari akawo maka ruwa cewar inna hab Jinjina kai yayi kafin yaja kujerar dake gefe ya xauna yana duban haj salamatu, Hajia Alhmdlh an gano gidan iyalin na ki.. Dafe kirji haj salamatu tai kafin ta mike tsaye dadi duk ya isheta ta jima a haka kafin ta nemi waje ta xauna kusada inna habi data ajiyewa Baba maigadi ruwan randa a kofi,dauka yai yasha sosai seda yai hamdalah sannan yasake dubansu, Wallahi yaya ashe gidan Malam Bashiru na unguwar kuka take nufi.. Kayya bade surikin hurera ba.. cewar inna habi Shi de wallahi dattijon Malamin nan mahaifin su muhammadu harith mai jan sallah ba Toh Alhamdulillahi komai yaxo cikin sauk Wallahi kuwa se sanda kika kimtsa se a rakaki ko hajia?! cewar danjuma dake kallon haj salamatu Mayafinta haj salamatu ta janyo cikeda zumudi tace, Yanzu ma se muje baba don abinda yakawoni kenan Baki inna habi ta rik e kafin tace, Kayya salamatu yanxun titin unguwar kuka baxata shigu ba kibari de xuwa gobe idan Allah yakymu se mu rakaki don ance hanyar su Fulani ke tare matafiya suna kwace masu kayayyakin su.. Badon taso ba haj salamatu tace, To shikenan inna da yau da gobe duk dayane Allah yakymu goben lapia Amiin cewar inna habi da Danjuma Sun jima suna tattauna yadda xasu bullowa tafiyar goben har aka kira sallar la asar sukayi abinci yadahu sukaci cikin kwanciyar hankali..... *WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB IN IYAYE```
Chapter 92 · 0% Book details