Sashe 43
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi ta shafo kwantaccen quarter million d'in dake jiki tace, Sai za'ayi biki zanje na gayama family na sannan sai ayi biki irin namu. Da sauri Modu ya kalleta girgiza kai yayi tare da Kara matse yatsunta cikin nashi yana cewa, No baby irin namu za'ayi kema zakiji dad'in shi. Duk maganar suna yinta me cikin harshen turanci batare da damuwa ba Kiara ta yadda domin ita dama ba wani damuwa tayi da sai anyi wani shagali ba, nan suka ci gaba da zancen yadda zasu gabatarwa da iyayan su tare da yin alkawarin babu wanda zai bar wani duk wuya duk tsanani musamman Kiara tafi nanatawa Modu dan tasan a gurinshi ne za'a samu matsala. Kasan cewar weekend ne hakan yasa Maimartaba sarki Aliyu hydar ya shirya dan zuwa gida gurin Ammi,shiryawa yayi cikin shigar sarakai tagani ta fad'a,rawaninshi aka shigo mai nad'i yayi mai sannan ya fito, da kallo Basma ta bishi dan kullum kara kyau yake yi sai faman murmushi take mai ya karasa a hanhali kusa da ita tare da kafeta da idanunshi dasuke a waje, cikin silent voice d'inshi yace mata; Wai meye sirrin ne kike ta wannan hawan kamar ana sanya miki yeast eh?! Baki ta turo mai tana bin ilahirin jikinta da kallo,ita kanta tasan tayi kiba sosai har tana neman takura mata tayi saurin kamo hanmuwan shi tare da cewar, My sugar boo ni kaina haka na ganni kuma ni bana son k iba gashi sugar boo ko b'atan wata bantab'a yi ba bare ace ciki ne... Maimartaba Aliyu hydar ya zame hannunshi a hankali daga cikin nata sannan ya shafi fuskarta, tana bashi tausayi sosai gashi tana son ta haihu kullum sai ta fad'a mai kamar shine wanda yake badawa amma sai dai yace mata tayi hakuri sannan taci gaba da yin addu'a Allah maji rok'on bayinsa ne,bayi take sosai ba dan datayi sallar zata shafa hannu a fuska ta mik'e tabi lafiyar gado kota wuce apartment d'in su hajja yakoko. Janye hannun yayi tare da cewa, Zanje gida gurin Ammi idan na dawo zan zauna a cikin fada so sai zuwa night insha Allah,kiyi min addu'a kinji?! Kai ta d'aga mai sannan suka jera har wajan kofar parlor Basma ta rakashi sai da fadawanshi suka rufamai baya sannan itama ta juya tare da komawa cikin bedroom. Motoci hud'u aka yi ta maimartaba Aliyu hydar itace a tsakiya sannan mafi kyau da tsada a cikin su, damboa road suka nufa suna zuwa aka wangale musu get shiga suka yi aka yi parking tare da shimfid'a wani dogwan carpet jah tun daga wajan murfin kofar Aliyu hydar har zuwa wajan kofar shiga cikin parlon Ammi na k'asa a tsakiyar an rubuta emir hydar da farin rubutu. Wani bafadene ya bud'e mai kofar motar yayin da sauran suka k'arasa sukayiwa kofar rumfa kafar shi ya fara zirowa guda d'aya wadda ke sanye cikin cover shoe ash color sannan ya fito da d'aya kafin ya fito da jikinshi baki d'aya, sandar shi aka bashi ya rik'e lokacin ne kuma fadawan suka bud'a mai hanya wannan abun duk anayi ne akan idanun Meenah wadda ke hangensu ta windown daga cikin d'akin su na upstairs, Baki bud'e take binsu da kallo har suka shige, Aysah ce ta k'arasa inda take tare da sa hannu ta rufe mata bakin wanda hakan yasa hankalin Meenah dawowa jikinta, cikin murgud'a baki take kallon Aysah tace; Kinga ki bari ko,ba Ammi ta shiga tsakanin muba ina ruwanki da bakina kawai zaki zo ki rufemin?! Aysah tace tana kokarin bud'e wardrop, Gani nayi kinga miji harda sakin baki shi yasa nazo na rufe miki dan gudun kar sauro ya shiga. Ahh abinda yafi miji na gani ba mijin ba,Allah kina shigar min hanci da kudundine karki bari na fatoki dan ni girmanki baya bani tsoro kawai dan dai kar Ammi ta sake min fad'ane amma da kinga abinda zan miki. Meenah ta fad'a tana harar Aysah, wajan mirror ta k'arasa dan dama powder take shafawa shine tajiyo dirar motoci taje ta leka, Oh dai ni kinga tafiya ta sai kiyi da aljanu bani ba. Aysah ta fad'a tare da turo mata bayan ta,jinjina kai Meenah tayi wallahi dama ta dad'e tana tara Aysah dan haka sai tayi fad'a da ita zataji dad'i, A parlor ya tarar da yareema Ngari sai faman murmushi yake mai da ka ganshi kasan yana cikin nishad'in ganin d'an uwan nashi, junan su suka rungume cikin tsantsar kauna a haka Ammi ta fito ganin su tayi manne da juna kafin tayi wani abun su Affy da Aysah sun rungume su baki d'ayan su hud'un ta saki lallausan murmushi wanda ya baiyanar da fararan hakoranta. K'arasawa tayi wajan tare da cewa; Toh asamu guri a zauna mana wannan murna haka kamar an dad'e ba'a had'u ba. Zama suka yi su duka suna dariya, kasan cewar idan yazo gidan nishad'i yake ji shi yasa ma har mantawa yake da cewar shid'in sarki ne,jiki yake warewa ayita hira dashi.Suna ta hira amma ko gilmawar Meenah babu,Ammi ce ta kula da hakan lokacin k'arfe 1:30pm anata kawo lunch ana ajiyewa ta kalli Affy tare da tambayar ta; Affy ina Bitti..?! Sai da kirjin Maimartaba Aliyu hydar ya buga jin sunan da Ammi ta fad'a, ya manta da sunan kwata-kwata nan da nan ya bi bakin Affy da kallo danjin abinda zata fad'a, wayar yareemah Ngari ce a hannunta tana kallon wani game tace. Ammi tana d'aki d'azu da na duba bacci takeyi. Oya toh maza jeki kice nace tazo ina nemanta. Da gudu Affy tayi upstairs tana kiran Meenah harta shiga cikin bedroom d'in, tashinta tayi tana yatsina ta bud'e idanuwa ganin Affy marainiyar wayon ta yasa tace, Dalla kekuma meye na tashina ina bacci,yasin zan mareki. Affy tayi saurin jan baya tare da cewa, Toh ba Ammi ce ke kiranki ba. Sakkowa tayi tabiyo ta da gudu suka fito parlon Affy ta cewa, "Ammi! Ammi!! Wayyo kinga wai saita dokini ko."tafad a cikin hausarta da bata fita, Ganin wanda ke cikin parlon yasa Meenah saurin dakatawa tana hura hanci, Ammi ce tayi mata magana da cewa, Zonan Aminatu. A kusa da ita ta zauna tana turo baki tare da hararar inda Affy ke zaune Ammi tace, Bitti baki ji zuwan yayanku bane shine kikak'i zuwa ki gaida shi?! Ina bacci nefa Ammi shine waccan marar kunyar taje tana duka na. Kai kai kai ni d'in ce na dukeki aunty Meenah? Ammi wallahi ban doketa ba cewa kawai nayi tazo injiki. Affy ta fad'a jin Meenah zata yi mata sharri,Ammi ce ta harareta tare da cewa, Ai gashi yanzu kin karyata ta,maza ki bata hakuri ai yanzu auntyn kuce gabaki d'ayan ku. Kamar Affy zatayi kuka ganin ga mari ga tsinka jaka,a hankali tace. Sorry aunty Meenah. Shafa hancinta tayi sannan Meenah aka kad'a kai alamar an hakura,mik'ewa Maimartaba Aliyu hydar yayi zuwa bathroom dan yin alwala,yana fitowa ya tafi sallah, Ammi ce ta kalli Meena tare da fad'in, Bitti eki sallah idan kinyi saikizo ki kaiwa yayanki abinci can dining room d'in baba. Tsuke fuska tayi alamar ita fa gaskiya bata son zuwa inda yake, ganin hakan ne yasa Ammi yin murmushi tare da dagewa akan cewar ita zata kai dan so take yau su kulla juna saboda shariyar tayi yawa babu me neman wani a cikin su. Ko bakiji niba bane Bitti?! Ammi ta tambayeta cikin d'an d'aga murya,a razane Meenah tace, Naji Ammi amma nida su Aysah ko zamuje kinga fa kayan da yawa?! Eh sai kuje da Affy. Tashi tayi ta wuce room d'insu,bayan tayi sallar ma k in tashi tayi sai da Ammi ta shigo tayi mata magana sannan ta fita,yana zaune kishingid'e hannunshi rik'e da phone yana ta faman kiran Modu amma yaki picking,sai da suka gama ajiye komai dama ya tambayi Affy tace sauran abu biyu su gama d'akkowa dan haka suna yin shigowa ta k'arshe yace, Ke zonan. Ba tare da ya kallesu ba Meenah tayi kokarin fita Affy tace, Ni?! Ya girgiza kai tace, Aunty Meenah dake yake fa. Zabgawa Affy harara tayi karaf suka had'a idanuwa yace mata, I said come here...! Ai tuni sai tsintar Meenah yayi a gaban shi sai faman tura mai baki take tana kunkuni,hannu ya d'agawa Affy alamar tayi tafiyar ta sannan ya maida kallon shi gurin Meenah wanda ke ta faman cizon kasan lips d'inta. A hankali ya mik'e tare da komawa kan kujera ya zauna, itama Meenah mik'ewa tayi tana binshi da kallo cike da takaicin shi. Kishingid awa yai akan kujera mecin mutum uku yaxaro wayarsa yashiga dannawa ganin kamar yama manta da ita a tsaye yasanyata furta kalmar, Latsi ahankali tana wani yatsina fuska Me kikace?!common Matso nan dak iya kawai Yafurta yana nuna kusa dashi,girgiza kai tayi tasoma hawaye saboda tasan abinda yake shirin yi inmade yaci xalin gashinta kokuma ya shiga kissing d inta wanda tad au hakan ta ajiye amatsayin iskanci ashe d an iskane tananan tana shirya ranar zata fito ta fad awa Ammi cewar yaya Aliyu Hydar d an iskane... Baxaki matso ba sena taso na kwasheki da mari Matsowa tashiga yi tana hawaye hannuwanta d aure akan tulun gashinta dayasha shuku,se ynxu ya lura ashema ba d ankwali akanta bayan uban warning din daya buga mata kwanaki akan lalle taxauna kullum kanta d aure da d ankwali ko hula,jikinta rawa yafarayi ganin irin kallon dayake watsa mata, Ganin tana b ata masa lokaci yasanyashi tashi xe fincikota tai saurin dakatar dashi, Dan Allah kayi hak uri karka tab ani wallahi bakyau Sakin baki yayi wai yaushe yarinyar nan zatai hankaline?!gashi har zata shiga ss2 amma batasan menene aure ba siririn tsaki yasaki had e da murtuke fuska taku d aya biyu yai ya cafkota yaxaunar da ita a kusa dashi, Sleepy eyes d insa yaxuba mata yana mata wani shegen kallo na ido cikin ido kasa kallonsa tai ta sadda kanta k asa tana wasa da pattern d in rigarta ajiyar zuciya yasauke kome yatuna oho ahankali cikin daddad ar muryarsa yace, Zubamun Abincin and feed me Yana k arasa fad a ya lumshe idanuwansa kallonsa tai tana cuno baki k atoto dashi zata bashi abinci abaki, Latsi Cewar Meenah had e da tab e baki