← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 107

Sashe 25

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

idanuwa dan bata manta damk ar da yayi musu ba,kallonta Modu yayi yana mak ale dariyar shi yasan ba k aramar damk a yareemah Aliyu hydar yayiwa gashin ba,suna tafiya suna hira sai ga gid'ad'o da gudun shi ya k'araso gurin Meenah yana nishi tare da kama hannunta yana ja yana cewa; Meenah kije inji Baffa yana sitting room yana jiranki. Ya fad'a yana nishi dan ba k'aramin gudu ya sha ba,ta kalli Modu tare da sakar mai murmushi tace; Na tafi Baffa na kirana,idan na dawo zaka kira min su Affy a waya mu gaisa. Modu ya d'aga mata kai,suka kwasa da gudu itada gid o yabi su da kallo yana girgiza kai tare da hango yareemah Aliyu hydar da ita a matsayin matarsa(sungul amama d'an shilan gwangwani). Tana shiga ta haye kan kujera tana nishi Mai Alooma ya bita da kallo yana girgiza kai.sai da ta huta sannan ta kalli Mai Alooma tana murmushi tace; Baffa gani,Allah yasa sak on aka siyo min?! Kallonta yayi tare da cewa; Dawo nan magana zamu yi,kai gid'ad'o jeka cikin gida kafin mu gama tazo ta sameku acan. Juyawa yayi yana turo baki ganin an ce banda shi.yana fita Mai Alooma ya kalli Meenah tare da shafar kanta zuwa fuskarta yace; Ameenatu itace mahaifiyar manzon Allah (s.a.w)wato fiyayyen halitta kinji de a tarihi shine d'anta to da ace tayi nisan kwana tare dashi to da baxe k'ijin maganar ta ba komai tasa shi xeyi mata,koda wuta ta had'a tace ya shiga bazai ji tsoro ba zai shiga saboda yana da biyayya dabin nagaba dashi tsira da aminci sutabbata agareshi,ina fatan kema zaki yi min biyayya a duk abinda zan ce mike kiyi dan nima nayi alfahari da sunan da na samiki ranar lahira kuma insha Allahu ke d'in 'yar aljanna ce?! Murmushi tayi tana k'ara shigewa jikinshi,kallon shi tayi tare da cewa; Baffa ka gayamin ko menene zanyi nima kodan na shiga aljanna naga larabawa da hurul inn wallahi Baffa bana son wuta bare ma idan ya sayyadi yana yi mana tarihi har cewa yayi ta lahira tafi ta gawayin mangal. Ta fad'a cikin gazgatawa tana jimamin tunowa da tarihin da tayi.wani farin ciki ya rufe Mai Alooma ya matseta a kirjinshi yana jin kaunarta na ratsashi cikin lallami da karya murya yace mata; Ameenatu ina son kiyi min biyayya kar kuma kice baza kiyi minba domin kinga ni mahaifinki ne, ina son had'aki aure da yayan ki shi yasa muka dawo tare dasu dan ku k'ara fahimtar juna. Zaro idanuwa tayi tana kallon Mai Alooma dake faman shafar bayanta cikin ranshi yana addu'ar Allah yasa karta k'i yadda sai yaga tayi murmushi tare da rufe fuskarta cikin dariyar ta mai kyau tace; "Hahaha Baffa ai yana da kirki wallahi yafi d'ayan shi bamu tab'a yin magana da shi ba baya dariya.!" Wani farin ciki ne ya kama Mai Alooma yayi saurin d'ago da fuskarta yana murmushi yace mata; "Ashe ma kuna magana to Alhamdulillahi komai yazo da dad'i Allah yayi muku albarka." Ya fad'a ita kuma ta kad'a kai tare da cewa; "Yanzu mafa muna tare dashi muna hira gid'ad'o yaje yace kana kira na, wallahi Baffa Yaya Modu yafi Yaya Aliyu hydar d'in nan kirki." Shiru Mai Alooma yayi yana nazarin ta,can! Ya gyara zama tare da kallon fuskar ta yana cewa; "Toh ai Ameenatu ni yareemah Aliyu hydar d'in nake nufi ba wai Modu ba,da Aliyu hydar d'in za'a had'aku aure kwanan na ma." Bakinta ta turo cikin shagwab'a ta fara murzar idanuwa alamar zata yi kuka be ankara ba kuwa sai ganin ambaliyar hawaye yayi suna bin kuncinta, sai ya shiga damuwa ya janyo ta jikin shi cikin lallashi yake cewa; "Ya isah Aminatu ba zan yi miki dole ba kinji?!" Hawayen ta share cikin sanyin murya tace mai; "Toh Baffa na yadda zan aure shi nima inason nayi koyi da annabi (s.a.w) amma dama ba shi bane,dama Yaya Modu ne." Tayi maganar cikin shagwab'a,jin ta amince yasa shi farin ciki tare da sanya mata albarka mik'ewa tayi ta fita yayi murmushi tare da janyo phone d'inshi yana neman layin yareemah Aliyu hydar... Team#MEENAH AUR BASMA [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!*
Chapter 25 · 0% Book details