← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 107

Sashe 84

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*73* *A* cikin kitchen suka jiyo motsin ta dan haka can kiara ta nufa da saurinta tana kiranta da, Sister where are you?! Da sauri layla ta ajiye knife d'in hannunta tare da juyawa tafita,kusan cin karo sukayi da juna gaba d'aya suka sakarwa juna murmushi kiara ta bud'e hannuwanta suka rungume juna suna dariya, a hankali kiaran ta kai hannunta saman cikin layla cikin gwarancin hausarta da ta fara iyawa yanzu tace, Sister yaya babyn mu hope yana mosi?! Da sauri Modu ya girgizawa laylan kai alamar tace a'a aikuwa layla tayi kalar tausayi da fuskarta kafin tace, A'a sister 4 day's kenan banjin komai am scared. Gaba d'aya hankalin kiara ya tashi ta rud'e tare da jan hannun layla ta fito da ita daga cikin kitchen d'in ta kamo na Modu ma tace, s go to the hospital please ina son wannan baby muje aI check up . Dariya taji sunyi gaba d'aya hakan yasa tabisu da kallon mamaki kafin ta had'e rai,Modu ya zame hannunshi daga cikin nata sannan ya kamo kumatunta yana kallon cikin idanuwan ta yace, Sorry my dear lafiyan baby fine and good it was just a joke,we are kidding you m sorry Ya fad'a yana kuma yin dariyar,dukan wasa takai mai gaba d'aya suka dara sannan layla ta koma kitchen ta samo musu abin motsa baki ta dawo parlorn ta zauna suka ci gaba da hirar su tamkar ba kishiyoyi ba anan ne kuma kiara ta sanarwa da laylan cewar tana son musulinta layla tayi murna sosai harda hawaye dan dama abunda yake damun ranta kenan kin musulintar ta amma yanxun sai taji wani farin ciki tamkar yau ta haihu. Toh sai muje a sanar da baba ko honey?! Yap abinda nace kenan nasan zasuyi murna sosai idan suka ji wannan zancen. Sister ina son idan na yi musulma asa sunana Nanarh Aisha ina sonta sosai. Alhamdulillah sister insha Allahu as you wished Allah yasa ki amfanar da addinin musulinci Allah kuma ya karb'i tubanki. Amin. Cewar Modu daya karkatar da hulan kanshi kowaccen su kokarin faranta mishi takeyi shi kuma sai k'ara narkewa yake kamar wani k'aramin yaro. *SHEHURI* Kuka Meenah ta dingayi tamkar bazata bari ba,da kyar ta iya motsa hannunta tana laliban wayanta so take ta kirawo aunty yaruwaiya amma wayam babu ita a inda ta ajiyeta,hawaye na zubar mata ta mik'e da kyar tana ci gaba da neman wayan amma bataganta ba wayar kuwa kamar sarki Aliyu hydar ya sani ya d'auketa ya tafi ta ita bedroom d'inshi nan ta ci gaba dayin kukanta har wajan asuba sai a sannan ta mik'e da kyar ta wuce bathroom babu abinda yafi d'aga mata hankali irin jinin da ta gani ya fito mata sai ta kuma sakin kuka lokacin sarki Aliyu hydar ya shigo d'akin yana sanye cikin wata jallabiya mai masifar kyau. K'arasawa yayi bak'in k'ofar bathroom d'in jin kukan da takeyi cikin muryarshi mai sanyi yace mata, Meenah bud'e min na shigo karki bari na kuma yin magana indai kin yadda cewar ni mijinki ne. Haushi da takaici suka cika zuciyar Meenah a hankali ta zare sakatar sannan ta b uya bayan kofar,shiga yayi sannan ya kalli bathtub d'in da ta kunna famfo na zafi dana sanyi ya kuma maida kallonshi bayan k'ofar data b uya daga ita sai towel ta cure hannuwanta a fuskarta ya kalleta yace, Oh wai har yanzu haushina kikeji?hakkinki ne na aure fa na baki ko sokike yi na fara sab'awa Allah daga zuwanki?! Meenah tayi mai shiru ta kuma ki bari su had'a idanuwa ganin haka yasa shi matsawa wajanta tare da sanya tausasan hannuwanshi ya janyota jikinshi ta kuma kankame jikinta saboda wani irin tsoranshi takeji ganin haka yasa shi d'aukarta daga ita har towel d'in ya tsilmiya cikin kwamin kwankan aikuwa ta saki wata razananniyar k'ara tare da kankame hannayanshi dama tuni towel d'in ya cire sarki Aliyu hydar yaki fito da ita daga ruwan har saida taji ta farajin dad'in ruwan sannan ta sakeshi da sauri tare da janyo towel d'in ta kara shi a jikinta. Zama yayi a gefen bathtub d'in sannan ya sanya hannunshi cikin ruwan yafara d'iba yana zubawa a jikinta gaba d'aya jinta take a takure ga haushinshi gashi yazo ya hanata sakat muryarta a sark'e ta turo baki wanda ya zame mata jiki tace, Dan Allah ni kafita. Yiyayi tamkar bejita ba ta kuma kankamewa shidai ruwan yaci gaba da d'iba yana wanke mata bayanta dashi ganin sunab'atawa juna lokaci yasa shi mik'ewa tare da d'aukan bucket ya tari ruwa a cikinshi na zafi dana sanyi sannan yaje ya fitar da ruwan da take ciki a hankali yace mata, Kiyi sauri ki wankan tsarki zamuyi sallah. Duk da cewar tasan sallan asuba yake nufi amma duk da haka sai da kirjinta ya buga gani takeyi tamkar irin na jiya za'ayi da ta idar da sallah ya kuma yi mata abinda yayi,shi kuwa yana gama fad'a yafita ya koma kan sofa ya kwanta yana zaman jiranta,sai da ta dad'e a cikin bayin sannan ta fito ko kallanshi batayi ba tasa kayan da tagani akan gado wanda da alama shine ya d'akko mata Arabian gown ce golden color sai kyalli take da kamshi ta zura yana kallonta har ta kammala sannan ya koma bathroom din yayi alwala yazo yajasu jam'i. Suna idarwa ta koma ta makure yanzu kam Meenah duk wannan bakin tsiwar sarki Aliyu hydar ya d'inketa babu ita sam, a hankali ya waigo yana kallonta kafin ya saki murmushi ya mik'a hannu zai janyota tayi saurin jan baya juyawa ya kuma yi yana murmushi tare da d'aga hannu yayi addu'a ya dade yana yi daga bisani ya shafa ya kuma waigowa sai ya tarar tana gyangyad'i ya mik'e tare da d'aukarta cak saboda ba tada wani kiba kamar ka doketa da bayan hannu ta fad'i k'asa wanwars,ai tanajin ya kaita gado tayi saurin mik'ewa tana zaro idanuwa tana bashi hakuri cikin kuka. Baah...Yaya...yallab'ai...rankaya dad'e dan..dan Allah karka kuma yimin komai wallahi kaji na rantse maka na dena yi maka duk abinda zai b'ata maka rai,wallahi hatta yawo babu d'ankwali baxaka sake ganin nayiba kayi hakuri kaji yayana sarki me adalci me tausayin Meenatu kanwarshi...! Sosai yaji ta bashi tausayi jin sumbatun da take tayi dan haka ya janyota yasa kanta a k'irjinshi yana d'an bubuga bayanta alamun rarrashi ita kuwa tayi lamo a jikinshi sun jima zaune shiru kafin a hankali ya kwantar da ita shima yabi bayanta ya kwanta a jikinta murya k'asa-k'asa yace, M sorry Meenah bazan miki alkawarin cewa na denaba domin wannan abun shine tushen auren sannan yanzu ke kad'ai gareni duk da cewar a daran jiya kafin na shigo nan na dawo da Basmah amma bansan ranar da zata dawo ba,infact ma dai ko ta dawo banajin zuciyata zata iya yarda da ita domin akwai abinda nakejin tsoro,please Meenah karki dinga guduna wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa ban bari wai sai kinyi wasu kwanaki a gidannan ba saboda nasan koba dad'e kobijima ked'in tawace koma dole sai nayi so kiyi hakuri kinji. Jikinta ne ya cigaba da yin rawa hakan yasa Sarki Aliyu hydar cewa, Kiyi kwanciyarki ni babu abinda zanyi miki yanzu. Sam kasa yadda tayi dashi ta kasa yin baccin duk kuwa da cewar tanaji amma tsoro da fargaba sun hanatayi,har kusan k'arfe 8:00am Meenah ta kasa koda kwakwaran motsi sai da taji ya tashi a hankali ya sumbaci goshinta sannan yafita daga d'akin ya koma nashi sannan ne Meenah ta sakko ta ruga da gudu tasawa kofar key ta koma kan gado tayi kwanciyarta.Tunani ta fad'a tana ta mamakin shi dan sam batayi tunanin zai iya yin wannan abunba koda kuwa a mafarkine lallai maza basu da kunya ta dinga ayyanawa da haka bacci b'arawo yayi awan gaba da ita.wajan misalin karfe 10:15am aka aiko musu da breakfast d'insu anan dining table ya gani lokacin shima fitowarshi kenan ya nufi bedroom d'in Meenah yana murd'awa yajishi a kulle ya san saboda shi ta kulle hakan yasa shi yin murmushi sannan ya koma parlor ya zauna yana duba wata jarida. Sai misalin k'arfe 11:30am sannan Meenah ta farka kodata tashi ma kukan ta cigaba dayi ta dad'e tanayi kafin ta wuce bathroom tayi brush tana fitowa sama-sama ta dinga jiyo hayaniya a parlorn farko hakan yasa tayi saurin k'arasawa wajan mirrow ta shafa powder da lipstick ta kuma fesa turaruka a jikinta sannan ta bud'e k'ofar a hankali tayi hanyar da dake jiyo manar su yaya gumsu dasu aunty yaruwaiya su Aysa tana zuwa dai-dai matakala suka had'a idanuwa da gid'ad'o yana yi mata wani kollon rainin hankali ta juya suka had'a idanuwa da yayah gumsu taga tana kallon kafarta gaba d'aya sai ta tsargu cak kuma ta tsaya ta dena sakkowar da ta farayi,ji take kamar ta juya ko ta tsalar ihu amma sai taji zuciyarta tak'i yi mata ko guda d'aya shi kuwa gogwan ya wani maze fuskarshi baza ka tab'a gane cikin yanayin da take ba aunty yaruwaiya tace, A'a Meenahta a sakko mana ko bazaki iyaba na k'araso?! Tayi shiru still tana tsaye sai wasa take da ring d'in yatsanta, juyawa yayi a hankali yadda babu wanda zai gane ya kallota akayi sa'a itama lokacin tana kallon gurin sai ya lumshe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana turo baki,Aysa ce ta mik'e tana cewa. Ah aunty Meenah ko har kambunci sarauniya sun fara aiki ne?bari nazo na take miki baya. Aysa ta fad'a tana taka matakalar dad'an gudu tana zuwa ta riko hannunta suka sakko Meenahn sai faman had'e rai take yi. Ikon Allah Meenah wai ko mutashi mu fitane sai wani faman had'e fuska kikeyi?! Yayah gumsu ta fad'a tana harararta cikin rawar baki Meenah tace, A'a wallahi yayah kiyi hakuri nifa fad'owa nayi daga kan gado. Aka kwashe da dariya shi kuma sai ya kalleta da sauri a tunaninshi gaskene amma taki had'a idanu dashi gid'ad'o yace, Ikon Allah anji gado ba irin na house ba harda su fad'uwa. Eh d'in banza kawai. Nanfa suka fara harsai da aunty yaruwaiya tayi magana sannan suka yi shiru,shi kam sarki Aliyu hydar tashi yayi ya basu gurin saboda sun isheshi da hayaniya.. Bayan Aliyu yabar parlorn aunty yaruwaiya ta dumamawa
Chapter 84 · 0% Book details