Sashe 54
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tana kuka cike da gabunta, wata dariya ce ta kwacewa aunty yaruwaiya dan haka ta dinga yi tana dukan cinyar Meenah,da kyar ta samu dariyar ta tsaya sannan ta kalli Meenah tace, Meenahtu tawa ni d'aya, wallahi kina burgeni over kawai dai dan ina son ki k'ara wayewa ne amma da zanso ki tsaya a haka nasan sai kin bawa hydar wahala, any ways kema mace ce., Kin gane ko Meenah wannan duk ba wani abu bane Mu da zamu samu ma yayi miki cikin da munji dad'i kuma Insha Allahu da izinin Allah komai zai warware but yanzun ma bata b'aci ba sai dai Ina son ki dinga yawan yi mishi text message zafafa masu shiga rai na soyayya Meenah zaki sha mamaki nan gaba yadda hydar zai mutu akan sonki,duk da yanzu ya rainaki yana ganin kin mai yarinta baki iya komai ba baki san komai ba Ina son ki nuna mai cewar ba'anan take ba kin gane tawan?! Aunty cewa fa kika yi wai yayi min cikin na bani wallahi bana son ciki shine fa ya sanya Maman Afrah kawata ta mutu wayyo ni nashiga uku ni bazan ma sake zuwa gurin shi ba. Haba tawan me yasa kike haka ne kinga gobe zamu tafi gashi babu wani kwakwaran abu daya shiga tsakanin Ku,kuma ai mutuwa riga ce tana wuyan kowa idan banda abinki ko a d'akin ku waye auta amma ai Amman ki bata mutuba so ki dena ambatar mutuwa sai kin haifarwa sarki Aliyu hydar yara masu yawa wad'anda zai yi alfahari dasu. Ni dai gaskiya wallahi... Wallahi me?! Aunty yaruwaiya ta tambayeta ganin sai faman cuno baki Meenah take ganin ta had'e rai tace, Amma aunty ai shima sai ayi mai magana amma kullum ni sai ayi tamin yana bani wahala. Toh Zan gaya mai sannan kuma zuwa dare zaki koma duk abinda nace kiyi toh kiyi shi kawai,haka ma duk abinda kikaga yayi miki toh ni nasa shi kuma za'a baku lada mai d'in bin yawa. Kad'a kai Meenah tayi jin ance shima za'a mai magana daga nan ta mik'e aunty yaruwaiya ta fara gyara ta cikin kayan kamshi masu sanyaya zuciya,tun abin na bawa Meenah haushi har ta fara biyewa aunty yaruwaiya idan ba'ayi wani abu ba zata ce ayi mata ko tayi da kanta.. _*DAMBOA ROAD_* Zaune layla take da innah da alama nasiha take sake mata sun dad e suna magana sannan inna ta k are da, Kibi mijin ki sau da k afa laylatu don kisani aljannarki tana k afarsa i nayi bari na bari duk abinda be sa dake ba babu ruwanki ciki kinji de nagaya maki Insha Allahu inna layla tafad a bakinta na rawa tasake cewa Toh inna niyanxu awane yanayi nake shin laifuffukan dana aikata abaya anya inna allah xe yafemun kuwa?! Kayya laylatu kidena dawo da hannun agogo baya hak a Allah me gafara ne tabbas zina tana daga cikin manyan laifuffuka wanda dukkan shariun da Allah la ya saukar sun hadu akan haramcin zina, Al kur ani mai girma da Sunnar Annabi saw,da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina Kofofin zina guda biyar ne _kallo zuwaga Abinda Allah ya haramta,Shigar batsa,Kalaman batsa,kebancewa da matar da ba muharrama ba,Shaawa Mai karfi babu aure Allah taala yace: kada ku kusanci xina Manzon Allah saw yace :Mai zina ba zaiyi zina ba,yayin da yake xina har sai an cire masa imani. Abdulllah Dan Mas ud Ra yace :Duk Al ummar da take zina,ta jawo wa kanta fushin Allah,da sun halaka.Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa biyar,sune : Addini,Dukiya,Rayuka, Hankali,Mutunci, Nasaba,amma zina ita kadai tana rusha adannan duka,Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa,mara aure bulala dari da daurin shekara. Ana tabbatar da zina ta hanya uku,shedu guda hudu,Mutun yayi ikirari da kansa,samun mace da ciki babu aure,ko shubha.Bisa sharudda da aka sanyawa kowanne Tabbas laylatu abinda kika aikata abaya babban laifine domin Zina wata babbar musifa ce da bala i da dukkan sharri,da take ruguza al umma,take wargaza iyali,take tarwatsa gari,take rushe mutunci,take jawo karayar tattalin arziki,da fatara,da tsiya,da annoba,a cikin rayuwar dai dai ku,da gidaje,da unguwanni, da gururuwa,da kasashe,da duniya baki daya, Zina itace cikakkiyar fitsara,acikin zina ake samun dukkan sharri kamar : Raunin Addini,Raunin Akida,Karancin Imani,Rashin kunya,Rashin kishi,Rashin mutunci rashin kwarjini,Rashin hasken fuska,Duhun zuciya,Rashin kima,Rashin Nagarta,Rashin Nutsuwa,Rashin Amana,Fushin Allah,cikawa babu imani,da Azabar Allah, Wannan shine kad an daga cikin illolin zina laylatu amma Alhamdulillah ked in yanxu bakya cikin masu aikatawa Allah ya tsare mu da zuriyar mu,da dukkan al ummar musulmi daga afkawa zina,wadanda suke yi Allah ya shirye su mukuma Allah ya k ara tsaremu da kariyarsa Innah na kaiwa nan tai shiru tana sauraron kukan layla ahankali layla tad ago tadubi innah da idanuwanta da suka koma jawur kamar gaushin wuta cikin murya kuka tace, Yanxu inna se Allah ya kamani da laifukan baya ko?! Kidena fad in haka laylatu karki k ara fada kisani shifa Allah me saukine kuma yana saukakawa bayinsa adukkan lamura Innah nagama fad in haka ta mik e had e da kiran furera dake k arasa gyara gidan laylan sallama sukaiwa layla domin aranar xasu juya katsina kauyen kurfi sosai layla tayi kuka takawo alherin da Modu yace tabasu tabasu tarakasu har gate sannnan tadawo parlornta taxauna tasaka disk d in wa axin malam ja afar tana sauraro dayake magana akan: YANA DAGA CIKIN ILLOLIN DA ZINA TAKE HAIFARWA TUN ANAN DUNIYA.... 1-RUSHEWAR TATTALIN ARZIKI: annabi (saw) ya bayyana acikin hadisi cewa dukkan society da suka ta allaQa da aikata al-fasha Allah madaukaki yana dankwafar dasu ta fiskan tattalin arziki dss, 2-GUSHEWAR KUNYA: annabi (saw) yace da imani da kunya dan-juma ne da dan-jummai, muddin 1 ya tafe to 1n ma baya zama, 3-YA DUWAR ANNOBA / CUTUTTKA: annabi (saw) yace zina bazata bayyana ba (kowa yana aikatawa ba shuwagabanni da mabiya ) face sai Allah me girma da daukaka ya sauQar wada mutane annoba / cututtuka, Dan-uwa ka dubi yanda HIV/ AIDS yake kashe mutanenmu, Allah ya kyauta, 4-MUDDIN KAYI SAI WANI YAYIWA NAKA: annabi (saw) yace ita zina BASHI ce, inkayi sai an maka, Duk wanda yayi zina da yar-wani ko uwar- wani ko yayar-wani, to shakka babu sai anyi da nashi akwan atashi Allah sarki hakan ya faru a yankin mu Wani mutum ya kasance me tsanani wa yarsa (mace) kasancewar ta girma ya hanata fita koda makaranta ne, kullun haka--- Rannan saiga da ciki, Karshe yasa mata wuQa awuya kota fa wanda yayi mata ko ya yanka ta, Qarshe tace - ina wannan Qawarta me zuwa yau-da kullum akace tace ba mace bace namiji ne, Kaga illan zina kenan 5-GUSHEWAR MUTUNCI/KIMA ACIKIN JAMA ka kula duk wanda yake zina to Allah saiya cire masa kima da kwarjini acikin jama zakaga bashi da kima acikin mutane. 6-MUTUWA BA IMANI: annabi yace duk me aikata zina al-fahsha to Allah ze zare imani daga gareshi Qarshe ya mutu ba imani Annabi yace duk wanda yayi zina da matan aure- to Allah ze kwashe dukkan aiyukansa na al-khairi yabawa mijinta Aranar tashin al-Qiyama kuma Allah ze masa azabar rabin wannan al-ummah ita matar ma haka. Innalillahi wa inna ilaihir-raju un !! Annabi yace babu laifi da Allah yafi kyama sama da mutum ya saka AL-AURANSHI A CKIN FARJIN HARAM !! Dan-uwa na ka sani aduniya dayan shirka wa Allah da kisan kai babu laifi dayafi Qirma sama da zina !! Allah ka mana katangar Qarfe da aikata zina Layla na k arasa jin k arshen wa azin tafashe da kuka ahankali taketa maimata, Nashiga uku ummah ta lalatamun rayuwata Allah kaiwa ummah abinda.... Ssssh Modu yakatseta da alama yajima awurin yana sauraronta da sauri tad ago kai tadubeshi sekuma ta mayar da kanta k asa tanaci gaba da kukanta... #Alhamdulillah dole nai godia da babbar murya agareku masoya nana hafsatu hakika banda bakin godia agareku kusani alkalami yayi kadan wurin zayyano sunayenku Nagode k warai wurin nuna damuwarmu akaina hakika adduoinku sun karbu idanuwana sun warke rak as k as ubangiji Allah yabar zumunci da k auna,kusani akullum kuna cikin zuciyar matar yusleem har abadan da iman...! WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB IN IYAYE```