Sashe 56
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*63* *K*allonshi tayi tagan shi yayi fresh fuskarshi tayi fayau sai dai idanuwan shi da suke mata wani irin kallo wanda baya rasa nasaba da kallaman da yaji tana fad'a,jikin shi ya janyota nan da nan kirjin layla ya fara bugawa dan ita yanzu sam bata son taji ya rab'eta duk sai taji ta tsangwami kanta cikin sanyin murya taji yana magana, Layla idan rai ya b'aci hankali ake sawa ya nemo shi,yanzu wad'annan kalaman da kike fad'a koni ban cancancesu ba bare uwa mahaifiyarki wanda tayi d'awainiyarki,tana sonki hakan yasa tayi miki wannan abun wanda take ganin kamar shine dai-dai kedai yanzu tunda kin gane gaskiya kici gaba da istigfari itama ki dinga yi mata ko Allah zai sa ta gane gaskiya kin gane ko?! Layla da tayi lamo ajikin shi ta d'aga kai alamar taji sai dai har lokacin zuciyar ta batayi sanyi ba kasan cewar tasan oud d'in nata baya sonta yanzu arniya tafita k'ima a wajan shi,tasan ita kawai cikon gida ce a gurin shi.Modu ya janye ta daga jikin shi yana duba agogon dake kafe a katafaran parlon sannan ya kalleta yana kokarin tashi tsaye yace, Zan fita zuwa wajan Aliyu hydar idan kina da sako wajan kawarki queen Basmah ki kawo sai na kai mata. Layla ta saci kallonshi nan da nan suka had'a idanuwa dashi tayi saurin sauk'e nata,kai ta girgiza kafin ta bud'e baki da kyar a hankali tace mai, Ka gaida ita kawai... Modu ya juya yana murmushi tare da cewa, Ok zata ji.. Bin shi tayi da kallo har ya b'ace mata sannan ta sauke ajiyar zuciya bedroom ta koma ta kwanta zuciyarta cike da tunanin yadda rayuwarta zata yi a gidan yadda taga oud na wani shareta yana d'auke kai tasan zata sha wulakanci da wannan tu nanin bacci ya d'auke ta mai cike da mafarkai kala daban daban... _*Shehuri_* Misalin k'arfe 10:30pm aunty yaruwaiya ta kamo hannun Meenah,ta k'ofar kitchen suka bi ta yadda babu wanda zai gansu sai dai Ammi dama tana fakwansu yanzu ma sai da ta biyo bayan su ba tare da ta yadda sun ganta ba nan aunty yaruwaiya ta bare iborn ta sawa Meemah a baki tace, Yauwa tawan idan kinje kina d'ora lips d'inki akan nashi ki zura mishi ita kin gane ai,kina d'an yi mai fari da idanuwa sai kin tabbatar da sakwanki ya isa gareshi sannan zaki cire bakin ki hope m clear?! Meenah ta sosa hab'arta kafin ta kalli aunty yaruwaiya tace, Kince dai shima kinyi mai magana ko aunty?! Eh mana nayi mai ba kina gani d'azu na fito daga fada ba ai zancen naje nayi mai. Jin haka yasa Meenah jin dad'i sannan ta juya ta tafi hanyar da tasan zata samu sarki Aliyu hydar ba tare da ta samu 'yan tsurku ba,Meenah na zuwa ta hange shi zaune yana duba wata jarida kafar shi d'aya kan d'aya gefen shi coffee machine ne da cupcakes ta juya bayanta taga babu kowa sannan ta k'arasa cikin bedroom d'in, yana jin motsi amma be ko kalli gurin ba dan yasan babu me zuwa sai Basmah kuma ita yanzu suka yi waya tace tana wajan hajja yakolo yasan sai ta dad'e sannan zata shigo amma yanzu ya d'auka dawowa tayi d'aukar wani abun. Shirun da yaji ba'a k'araso ciki sosai ba yasan yashi kallon k'ofa karaf suka had'a idanuwa da Meenah ta sakar mai murmushin ta mai matukar kyau,da tsananin mamaki yake kallonta shi yanzu ma besan yadda zai yi da ita ba ya kuma kallonta tundaga sama har k'asa. Sanye take cikin wata had'ad'iyar laffaya mai matukar kyau sai dai sam bata yi mata kyauba kasan cewar Meenah ba k'iba sai tayi kamar zanata akayi sannu a hankali yaga tana warwareta ya zaro idanuwa bayan ya had'e rai bata damuba dan dama aunty yaruwaiya tace zai yi hakan,sai da ta cire nad'in lafayan tas ta tsaya daga ita sai wani arnan mini skirt dark blue da wata arniyar vest white ta k'arasa kusa dashi tana wata tafiya yayin da bakinta ke motsi alamar tana shan alawan. Aliyu hydar kuwa tsabar tsananin mamaki kasa rufe baki yayi sai binta da kallo yake,cikin shagala ya ajiye jaridar yana kallon Meenah ta zauna a gefen shi tare da kashe mai ido d'aya tana lumshe wa,a wahale zuciyar shi na bugawa yace, Meenah...! Yes honey. Tayi maganar tamkar wata karuwa tana sake matsawa jikinshi,tabbas yarinyar nan ta waye da yawa wai nan ma ko secondary school bata kammala ba Ina ga ta tafi higher level sai abin da yafi haka kenan,haka sarki Aliyu hydar yayi ta ayyanawa kafin yaji yatsunta a cikin kunnansa tana juya su a ciki shi kuma sai faman lumshe idanuwa yake can ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya da karfi. A dabaran ce Meenah ta sanya mouth d'inta cikin nashi tare da tura mai sweet d'in bakin shi gabaki d'aya ya rud'e ya fara yamutsa ta yama manta da cewar ba Basmah bace Meenah ce,ita kuwa duk da tana cikin tashin hankali sai tayi shiru ta kasa yin magana bare ta hanashi sai dai kana iya hango bugun zuciyarta saboda tsananin tsoro. Tafiya tayi tafiya sam sarki Aliyu hydar ya fita hayyacin shi domin wannan karan Meenah na bashi gudun mawa yana gaf ta shiga babbar fadar da ba'irin wanda ya saba shiga kullum bace kawai suka ji muryar Basmah bayan ta gansu tayi saurin juya musu baya, da gudu kuma tayi waje bedroom d'inta tayi tana kuka wani zazzafan kishi na addabar mata zuciya. Shikam gogan da kyar ya iya zame jikin shi a gun Meenah amma abin mamaki sai ta sake narke mai ta hanashi tashi kwata-kwata tana mai wani d'an kuka k'asa-k'asa, rasa yadda zai yi sarki Aliyu hydar yayi ga tunanin Basmah ga Meenah itama ta narke mai uwa uba ya kasa yin magana.Da kyar ya samu ya saita zuciyar shi yana kokarin tashi Meenah ta kuma makale mai ita kanta ji take bazata iya barin shi ya fita ba,ganin haka yasa shi rungumeta ba dad'ewa tayi bacci sai da yaga baccin yayi nisa wajan karfe 1:30am sannan ya zame jikin shi ya nufi room d'in Basmah. K'ok'arin shiga yake sai yajiyo muryarta tana kuka tana nagana daga ji waya take dan haka ya tsaya yana jin abinda take cewa, Wallahi umma duk ina yin abinda kuka ce amma wallahi tunda yarinyar nan tazo gidan nan sai ya dinga kiranta d'akin shi bansan meyasa ba wallahi amma duk magungunan da kuka bani ina samai kuma ina turare gidan.. Daga can cikin wayar hajja yakolo ce ke cewa, Rabu dashi kedai ba kina yin yadda muka ce ba?Toh kisha kurumin ki itama zamuyi maganinta ai ke kin fara ganin alfanun maganin ko?! Basmah ta share hawayan dake bin kuncinta tace, Eh Mama har fa na k'arkashin gadon da na samai wallahi yana nan amma kullum cewa kuke zai kara so na amma sai dai inganshi da wannan figaggiyar yarinyar da babu abinda zata nuna min. Sha kurumin gimbiya abinda ma gobe zasu bar gidan ki dena damuwa zamu san abin yi kinji ko?! Kafin tayi magana ta ganshi a tsaye akanta fuskarshi babu yabo ba fallasa baza ka tab'a gane yaji maganganun ko bejiba yadda yayi sai dai tsarguwa da kuma rashin gaskiya tasa asirinka ya tonu,Basmah jiki ya fara rawa tayi saurin katse kiran tana kallonshi harya k'arasa inda take shima ya zauna. Basma keda waye haka cikin dare?! Kasa cewa komai tayi banda kirjinta dake dukan tara-tara jikinta na rawa hawaye na bin kuncinta jiyayi kanshi na sarawa ya fara kifta idanuwa yana dafewa kafin wani lokaci idanuwan shi sunyi jawur, da sauri ya mik'e directly ya wuce d'akinshi Meenah na kwance na bacci yayi saurin lekawa nan yaga wasu jikejike da wasu layu rakwacam a karkashi tamkar wani d'akin d'an bori.Kanshi ya dafe saboda tsananin sara mai da yake yi ya fara furta kallamar da ya dad'e bejita a bakinshi ba. Lahaulawalakuwata illabillahil aliyulazim, innalillahi wa'inna'ilaihir rajiun how comes?! Da sauri ya kalli saman gadon yaga Meenah na bacci hankali kwance yayi saurin mik'ewa tare da d'aukarta a hannu yayi waje shaf ya manta da matsayin shi na sarki yayi hanyar apartment d'in da yake tsammanin su Ammi na can. Wani d'aki ya nufa yana bud'ewa yaga aunty yaruwaiya ta rafka wani uban tagumi kai da ka gani kasan tana cikin tashin hankali,tunanin shine ya bashi ko da Ita Basmah tai waya sai kuma ya had'e rai cikin b'acin rai yace, Aunty wa kike jira ko waya kika yi?! Ai tana jin muryar shi ta mik'e tana hamdallah musamman da taga ya taho da Meenah,cikin murna aunty yaruwaiya tace, Yo ga tanan yarinya tayi tafiyar ta daga cemin kana kiranta. K'arasawa yayi kan gado ya kwantar da ita sannan ya kalli aunty yaruwaiya yace, Ni k'arya take min ina Ammi take?! Zaro ido aunty yaruwaiya tayi tana kallon sarki Aliyu hydar jin yana neman Ammi da sauri kuma ta kamo hannunshi suka fita, wani d'aki ta kaishi lokacin karfe 2:00 na dare suka hangi Ammi zaune akan sallaya tana jan carbi bayan ta farka uban tagumi,cikin sanyin murya taji murya kamar ta Aliyu hydar sai dai tayi tunanin gizaune kamar yadda ta sabaji kullum amma sai taji ya kuma kiranta kamar a zahiri tayi saurin juyowa ganin shi yasa tayi saurin mik'ewa tsaye. Kasa hak uri yai da sauri ya nupeta ya rungumeta yana hawaye wani tarin soyayyar mahaifiyar tashice takara shiga zuciyarshi gefe d aya Ammin kuwa wani tausayin d an natane yasake mamayeta ahankali tasa hannu tana goge masa hawayen, Ammi yafurta ahankali yana sake rungume Ammin kamar wanda xa a kwace masa ita, am Aliyu.. tabashi amsa tana k arin maida hawayen dayake neman zubo mata, Ammi dan Allah dan annabi kiyafemun kinji Ammina I deserved to be punish rayuwata is miserable Ammi kimun duk abinda kikaga yadace saboda ni... Sssh ...Ammi ta katseshi tana girgiza kai cikeda nutsuwa tace, Mekaimun Aliyu?!bakamun komai ba Aliyu karma kasake fad in haka kaje kasamu bacci Aliyu kaji?! a kai kawai yai yanasake kankame Ammin sun jima ahaka seda Ammi tace yatafi haka sannan yakoma apartment d insa jikinsa duk ba dad i cikin zuciyarsa kuwa sake sake yake na hukuncin daxe d