Sashe 86
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kwalliya xata... Ranka yadad cewar gajiram cikin sigar jan hankali Kallonta shehu Bulama yai yana sake runtse idanuwansa na kode mafarki yake ne, Ba mafarki kake ba ranka yadad e..Nice dai gajiram dinka mahaifiyar babagana ar daria shehu Bulama yai yana dubanta Matsawa tai kusa dashi ta karbi serving spoon din hannunshi tashiga serving mashi abincin a plate.. Haa bud e bakin ta fad i hakan tana kai masa lomar bakinsa Bis... Be k arasa gajiram tai hanxarin cusa masa abincin Ganin xe sake wata basmalar bayan ya hadiye abincin yasanya gajiram sake danna masa wata lomar hade dasa hannunta tana shafa y ar furfurar dake sajensa,tuni ta sha afar dashi daga neman tsari hartaci galaba akansa ta faki ido ta tsiyaya garin maganin acikin black tea dinsa ta kai masa bakinsa nanma bata bari yayi bismillah ba harya shanye Seda ta tabbatar ta gama komi ta b angaren sa sannan tatashi tafita bayan sun dan taba hira sashen ta takoma tana shirya yadda xata binne layar anjima batare da an gano taba.. Tana xaune a parlor tana kar kad a kafafuwa falmata y arta tashigo idanuwanta kwance shab e shab e da hawaye tashi tsaye gajiram tai hannuwanta dafe akan kirjinta, Falmata.. Mami cewar falmata dake goge hawayen dake tsiyaya a face d inta Zo nan falmata kigayamun meke faruwa fada kukai da wata?tun jia bakya gidan nan falmata ina ki kaje?!sanar dani damuwar ki Fadawa falmata tai jikin gajiram tana kuka sedatai me isarta sannan tai shiru tana sauke zuciya,shafa kanta gajiram tashiga yi, Ko xan san meke faruwa falmata?? Mami... sekuma tai shiru, am falmata Mami promise me baxaki fadawa baaba komi nadaga abinda xance dake ba Nayi alk awari falmata Cikin kuka falmata tace, Mami ci...Ciki ne dani Neman jintaa da ganinta gajiram tai ta rasa na yan wasu dakikai kafin ta kwaso ashar ta dire akan falmata,cikin huci ta hankadeta gefe tana karkade jikinta kamar taga abun kyama cikin xaro idanuwa hade da tashin hankali bayan ta waske ta da mari har biyu tace, amun ba se anjima ba uban waye nace dan gidan uban waye ya miki ciki??da har xaki bud e baki ki cemun ciki ne da ke wallahi anyi haihuwar asara nayi dana sanin haihuwar ki bankad addiya y ar iska kawai Shiru falmata tai tana share hawayen fuskarta cikeda takaici gajiram ta sake sharara mata mari, Xaki gayamun dan gidan uban waye ya maki cikin ko sena hallaka ki yanxun?! Mami...Mami Amadi ne fa Sam Mami ta ma mance da wani me suna Amadi a duniya don kidimewa cikin kifkiftta idanuwa tace, Wanene Amadi sanar dani shin d an gidan uban wanene a yerwa?! Cikin ja baya da karkarwar jiki falmata tace, Mami Amadi de..Amadi..Amadi dogaren baa babs(babagana) Me yakwan gajiram tai salati ashar ta lalaiyo ta sake durawa falmata cikin takaici da masifa tace, Anmake barikin naki be kaiki ko ina ba se mutuncin ki daya ragu don uban ki ki samo cikin dan masu farcen susa mana wanda dole ne xa ace ya aure ki asirin ki a rufe shine xaki je don tsinantaka da shegiyar jaraba irin taki ki kwaso cikin Amadi,Amadi fa Amadi kaxamun dogarin babagana da ba kullum yake wanka ba bare wanki yaron da kullum cikin samamun wari yake aamma don tsabar kwashewar albarka shine xaki kwaso cikin sa banxa gantalalliya Amadin da ba asan asalinsa ba Ta k arashe xancen hade da sakin tsakin takaici Mami.. cewar falmata dake riko kafafun gajiram tana kuka Mami ki temakeni kikai ni asibiti Mami mutuwa Xanyi Tsaki Mami ta saki,kafin ta janye kafafunta daga hannuwan falmata dake rik e dasu, Koma menene ke kika janyo wa kanki dan uban ki lokacin da mahaifiinku yace kowa yaxabi makaranta yakaishi bacakikai bakya so ba ke anan xaki da kika fara anan din kika dena,kika saka yawo agaba dayake kunnen kashi ne dake ai ga irin tanan abinda ya biyo baya, Kuma a hakan kike so na kwashe ki na kaiki asibiti xancen cikin yafito kowa yasani?!tukun nama ina shi Amadin?! Cikin kuka falmataa tace, Mami yace shi ba cikin sa bane wai sharri nai masa Wayar Mami ce tafara kara lokacin anfara kiraye kirayen sallar magrib ganin yakolo ce yasa tai hanxarin dauka ta kara a kunne, Hello..Yakolo,na am!kai haba har yanzu?!kassh to se yaushe kenan?!okay can anjima kenan?to shikenan tawan sekin dawo,nima nagama dayan saura na anjima,to sekin dawo wani mummunan alkaba in yasake faruwa kede bari abinda babagana yai shi akaiwa falmata ita harda rabon shege aciki wallahi..Kede bari sekin dawo kawai abun ba a cewa komai Katse wayar tai ta mike bayan ta makawa falmata harara sannan ta wuce sama fuu kamar xata tashi sake fashewa da kuka gimbiya falmata tai tanayi tana surutai ita kad ai kamar xaucacciya... <><><> Da k yar jakadiya Mangu ta mike tana d an d ingisa k afa don yau kam taci alwashin ko gunduwa gunduwa su gajiram xasuyi da namanta hakan baxe hanata fayyacewa hajjagana kullun kutingwilar da sukai mata abaya ba kai haryanxun ma da bata tare da su tareda neman yafiyarta na abubuwan da aka had a baki aka k ulla da ita.. Sandarta ta dago tafara dogarawa da ita sannu a hankali harta k arasa sashen na hajjagana dake cikin shehurin tana xuwa tayi neman iso aka bata izini tana shiga ta tarar da hajjagana da kuma aunty yaruwaiya a parlor se murmushi suke da alama tad in da suke ya masu dad i... Mangu na karasawa ta xube a kasan carpet din dake baje a harabar parlorn cikin hawaye face face a fuskarta hajjagana da yaruwaiya suka dubi juna kana suka maida dubansu kanta cikeda isa yaruwaiya tace, Salon makircin ku da asirinku be bar muba shine kika biyo ta har sashenta shin da wanne kikaxo!! Narantse miki da Allah idan da bokayen maiduguri kikaxo dasu akanki nan wajen yau sekin sauke su yanzu Xata k ara magana Ammi tadaga mata hannu alamar tai shiru cikeda dattako da kima irinta mutanen kirki Ammi tace, Shin da me kikazo Mangu?! Share hawayen fuskarta Mangu tai don sosai yanxun tayi nadama nadaga abubuwan data aikata don kusan kullum cikin mafarkai take marassa dadi wanda idan ka auna suna nuni ne da abubuwan da ta aikata a baya marassa kyau cikin kuka tace, Na cancanci ko wane irin mummunan hukunci da xa a yankemun hakika ni Mangu bada wani abun naxo ba fyace tarin dimbin laipuka dana aikata wanda naxo na fayyace su na kuma roki gafara idan da halin afuwa.. Tsaki aunty yaruwaiya tai ji take kamar ta tashi ta rufe jemammiyar shegiyar da duka gashi Ammi ta hanata magana wannan shine adakeka ahana ka kuka... Cikin k asa da kai hawaye na kwarara Mangu ta soma magana.... *Kankiya LG* yar mahaifiyar layla ta mike bayan ta idar da sallah tana bubbuga kwankwasonta saboda azabar ciwon dayake mata,Shafa addu ar tai sannan ta nannade dankwalinta ta daura shi akanta ta rame ta xuge ta lalace ainun kamar ba ita ba y ar dattijuwa mai farcen susa,kallo d aya xakai mata kasan tayi nadama kwarai matuka don sam yanxun sallah bata wuce ta hakama karatun qur ani kullum cikin yinsa take ga yawan Kai kukanta ga mai sama daya yafe mata dimbin laipikan data aikata saboda shi din mabuwayine gagara misali.. Farfajiyar gidan ta fita tsit ba kowa yau tun asubah bataji duriyar kartin banxan ba jinjina kai tayi har xata koma cikin gidan sekuma tai saurin xura takalmanta ta fita tana d an had awa da gudu megadin dake tsare gidan ne ya tsaida ta yana kallonta, Ina xuwa hajiya?! Baba mai gadi kaimun rai ka ji kaina katemakeni ka kyaleni na tafi dan Allah yadda katemakeni na kubuta kaima Allah ya temakeka kaji?!dan Allah ka tausayamun baba Shiru yai yana de kallonta amma bece komai ba ganin beyi magana ba yasata sake kwararo masa roko duk dan ya kyaleta ta kubuta, Dan Allah baba kaji?! Hajia idan na kyaleki kika kubuta mexance da iyayen gidan nawa?? Shiru haj. Salamatu tai sanin batada tacewa don gaskia ya fad a har ta hak ura xata koma ciki yakirata, Zo hajia Be rufe baki ba ta dawo jikinta se bari yake, A wane gari kike?! Baba ni yar kano ce amma inada iyali a katsina a kauyen kurfi Kurfi?! ya maimata sunan.. E kurfi baba.. Allah mai iko nima dan kurfin ne..Kuma Ina tunanin yanxun na biki kawai mu kubuta tare saboda idan kika barni anan suka dawo suka ga na kyaleki kin kubuta tofa ba makawa sunan baba me gadi murugayi domin kashe ni xasuyi To baba muje mana ko?! cewar haj salamatu dake kallon kudu da arewa kar wani yataho.. a kai kawai baba mai gadi yai hade da nade kasan wandonsa ya kwasa aguje a baya haj salamatu ta bishi hade da tattare kasan jemammen xaninta itama tana tafiya a tattale kamar y ar kaciya don ta wahala ahannun barayin ba kadan ba don kowannensu ya kwaso sha awarsa akanta yake gyagije ta harse yasamu nutsuwa.... Basu suka dena sharara gudu ba har seda sukaje babban titi suka samu mota suka haye da kwandasta (conductor)keta kwala kiran, Kurfi kurfi na kurfi su haye mu cale... _*Nima xoxo nace to ina katsinawan dikko?!d akin kara kunya gareku bade tsoro ba...Na gaisheku katsinawa ina kuke?!To Nana Hafsatu na mik o gaisuwarta musanman yan kankiya local government_ _Ina kuke yan kurfi?!to ga munan muda su haj.Salamatu da baba mai gadi..._ #Assalamu Alaykum Beautiful people acigaba da hak uri da Miss xo abubuwa ne sukai yawa wanda dole typing din yaxamto ba kullum nakeyi ba se an d an d auki lokaci,Ayi hak uri de munkusa k arasa shi Insha Allah #Nagode kwarai Allah yabar zumunci... _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB IN IYAYE```